AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ranar juma’a kamar yadda aka sa aka daura auren Aysha suheer samaila, tare da Abdurasheed Ahmad Matawalle akan sadaki dubu dari, Rasheed yasha wani ubansun getzner fara kal sai walkiya da rawa take yi, babbar riga da yar ciki da wando kallo daya zaka musu kasan ba karamin kudi suka ciba, komai na jikinshi fari ne, sai hulan shi dake hannunshi domin yakasa sawa, tsabar yawan gashin kansa,sha’aninka da ba sabonba, yafi karfi wuri sa p.cap, sai fara’a yaake yana ta gaisawa da mutane, koda dai bai wani gayyaci jama’a ba amma yayi mamakin yadda aka taru harda yan jarida ga kuma abokan aikinshi dana kasuwanci shi.

lokacin da labarin ya iso gidansu suheer da shike ba wani mutane aka tara ba kasancewar yadda abun yazo iya kawayen ammi ne dana anty hafsa suma basu fi mutum shida baa bangaren amarya kuwa ba kawayensu ko daya, dama fareeda ne uwar zagwadi to ita kuma ga halin da take ciki na zaman shiru. Kamar daga sama sukaji yara suna shigowa gidan kasancewar masallacin da aka daura auren ba nisa da gidan don haka yara suka shigo suna cewa andaura auren Abdurrasheed da Aysha Suheer, wasu hawaye ne masu zafi suka gangarowa fareeda a idonta wacce tun ranar da taji labarin sai yau hawaye ya sauka a idonta take zuciyar ta ya fara gudu kamar tana wasan polo, suheer kuwa wani irin bugawa zuciyarta yayi a daidai lokacinne kuma wayarta yayi kara alamar shigowar sako, budewa tayi tana duba content din “tabbas nayi rashi wadda bazan taba maida makamancinsa ba a rayuwar duniya, zan rayu dake a cikin zuciya ta har abadan, dukda cewa gangar jikinki ya barni bari mai nisan kilomitoci, ina miki fatan alheri a cikin sabuwar raguwar da zaki shiga, daga habeebi,…” sai kuma emoji na kuka guda biyu, wani kuka ne ya zowa suheer mai karfin gaske hakan yasa ta toshe bakinta da hannu, wani sako ne ya kuma shigowa jikinta yana karkarwa ta bude ba nomban dazu bane wani ne daban karantawa ta farayi,

“Ina miki barka da shigowa duniyar auren fansa.”…….

Da babu dai gwara ba dadi,…… Nasan cikin minti daya zaku karance shi…
????AUREN~FANSA????

PAGE 57 / 58

             INDIA.

Awanni masu yawa kwararrun likitocin suka kwashe suna aiki akan lamido, tsawon wnn lokaci kuwa hafsa bata zauna ba ta nan tsaye akan kafafunta sai addua take akan Allah yaba dan uwanta daya tilo da ya rage mata a duniya lafiya, bude kofar theater room din akayi likitocin suka fara fita daya bayan daya suna share zufar dake tsattsafo musu a goshi, duk wanda hafsa ta tare da tambayarshi jikin lamido sai yai mata banza ya wuce, ba karamin tsorata tayi ba ganin yanayinsu, ……wani likitan ne ya kara fitowa yana kokarin cire handgloves dake hannunshi hadi da daurawa akan wani dan tiren silba da wata nurse ke rike da tana biye dashi a baya.

Da sauri hafsa ta matso kusa da su tace “dr ya jikin dan uwana? anyi nasara?, idanuwanta a waje take jero mishi tambayoyin, dan dakatawa yayi kana ya sauke facemask dake fuskarshi, wani kallon da ya mata yasa hafsa jin kafafunta suna kokarin gaza daukarta,….Yace “cikin harshen turanci ba laifin mu bane, meyasa kuka yi jinkirin kawo shi asibiti, ina tabbatar miki da patient dinnan ya kara wasu awanni baku kawoshi ba da ba lallai yayi surviving ba, komai na iya faruwa, cikin firgici anty hafsa tace “me kake nufi dr, kar kace min dan uwana ya rasu,” yana kallonta yace ” you don’t worry ma’am the operation was successful.

Wani irin tsalle hafsa tayi ta rungume nurse din dake tsaye bayan likitan tana ta furta Alhmdllh, likitan ya kalli nurse din yace “a maida patient din zuwa ICU, tace “yes sir” yana kallon hafsa yace zaki iya biyoni office for more information, da to amsa farincikinta ya gaza boyuwa, sai juyawa take tana kallon kofar theater room din…

Habeeb yana kwance tun bayan da ya turawa suheer sako a waya, idanunshi lumshe ji yake kamar yana tsakanin rayuwa da mutuwa ne, tsabar irin radadin da yake ji a zuciyar shi, da farko rikicewa yayi da ya samu labarin auren ta da rasheed har ya fara tunanin kodai maganar mamarshi gaskiya ne, saida da wanda ya kawo mishi labarin ya tabbatar mishi cewa auren sadaukarwa suheer tayi kafun ya dan samu salama, yana tuna irin soyayyar dake tsakanin suheer da mahaifinta, tabbas ta cika ya ta gari mai sadaukar da farin cikinta domin mahaifinta, kallon kwalaben maganin tarin da ke gabanshi yayi yanason yasha kozai rage mishi tunanin da yake yi amma kuma yayiwa mama alkawarin bazai kara sha ba, shima a nashi bangaren yayi mamakin yadda matasa keshan wannan abu wai da sunan maganin rage damuwa, ehh lokacin da yasha wancan karon ya manta komai da kowa inda ya ringa bacci kamar sakarai saidai labarin ya sauya daga lokacin da ya farka domin tunanin dawo mishi yayi sabo fil har ma fiye da na farko, (wnn yana daga cikin sharrin kayan maye zai ringa baka feeling kamar yana kawar maka damuwa ne, amma deep down yana yaudararka ne har saika zama addicted to it, yadda dole sai kasha zaka sami nutsuwa,) Allah ya shirya mana zuriya baki daya ameen, kawar da kai yayi daga kallon kwalaben, a hankali ya furta Allah kai ka samin sonta so mai tsanani a zuciyata karon farko da na ganta, Allah kai ka raba mu kuma ka fi mu sanin ma’anar hakan Allah kasa hakan shine mafi alheri a garemu nida ita baki daya, sannan kabani hakuri da juriya Ya Rabbi, ya fada hadi da daura hannunshi gefen zuciyar shi dake bugawa da sauri kamar zai balle ya fado kana ya kara rumtse idanunshi yana fatan samun salama.

Kamar wadda aka tsikare shi kuma ya tashi ya hau hada kayanshi a travelling bag nashi, saida ya hada duk abunda yake bukata kana ya zuge zip na jakar ya jingine a gefe ya koma ya kwanta yana jiran right time, domin ya riga da yayi making mind nashi. Niko nace hmmm habeebi ai hijira halal ne, kuma idan ka fita hijira dama mutum zai tadda dayan abu biyu ne ko ka tararda arzikinka a can, ko kuma ajalinka,????.

Ammi na zaune palo da sauran frnds nata biyu da basu wuce ba hajiya saratu, sai kuma maman saudat wacce nan makwabtansu take ita, dan hira suke yi sama sama amma ammi tafi karkata hankalinta duniyar tunani, tana cikin farin ciki yau tunda hafsa ta kirata ta sanar da ita anyi nasaran aikin da akawa lamido, saidai kuma daya bangaren na zuciyar ta ya karkata ne ga tunanin rayuwar yayanta, auren suheer mara kan gado wanda gaba daya basu fahimce shiba, domin kamar dai yadda akasan aure a kasar hausa kuma aurenma na budurwa wnn yasha bambam don basuga wata daga bangaren ango yazo ba, sai suka alakanta hakan da yanayin da auren yazo bagatatan, amma duk da haka ai ko mutum biyu zasu zo wani zuciyar ya bata amsa, ……Ga kuma bangaren fareeda wacce tana tunanin dole nema gobe ta kaita asibiti din lamari nata is getting worst, sai karewa take yi a tsaye gashi saita kwana ta wuni bata ce ko uffan ba, haka kuma bata cin abinci na kirki zata tashi ta wuce daki kana bata fita sai ya kama dole.

Kamar dai yadda aka saba auren hausa fulani mata ke zuwa daukan amarya, to auren suheer dai yazo da sauye sauye masu dama, misalin karfe tara na dare rasheed ya iso kofar gidan bisa rakiyar buba wanda baisan ina suka nufa ba, saida ya gansu kifar gidansu matar boss ya fara mamaki a ranshi ki me zasuyi anan kuma? banda abun boss minti nawa ya rage akai masa amaryar da zaizo wani zance kuma, shi buba ya dauka tadi rasheed yazo, tunaninshi ya katse ne lokacinda yaji rasheed yace “fita ka mana sallama da yarinyar kuma ku dawo da wuri, because i have many things to do, don haka bani da lokacin batawa anan.” with seriousness yayi maganan hakan ne ya bawa buba mamaki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button