AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Lallashi sosai anty hafsa tayiwa fareeda kafun ta dan fara dawowa nutsuwar ta, wanko fuskar ta tayi tazo ta dan gyagyara sannan ta koma, wnn karonma dai kasawa tayi daga an daura camera a kan fuskar ta sai kuka,, har abun ya fara bawa masu daukan mamaki, daga karshe dai korata akayi da cewa akwai masu jira akan layi tana ta bata musu lokaci, ta fito tana rusar kuka ta fada jikin anty hafsa tana mata bayani, aiko nan hafsa ta fara bala’i ta inda ta shiga bata nan take fita ba har saida takai ga duk masu ruwa da tsaki a daukan shirin sun fito ciki kuwa harda buban rasheed, kallon hafsa yayi da tambayar ta dalilin hayaniyar da ta ke musu aka, hafsa tana masifa tana magana har ta kai karshe.

Kallon sama da kasa yabi fareeda da shi sannan ya maida kallon shi zuwa ga hafsa yace”akan wannan mara class din kike daga mana murya haka? ko lokacin da kuka shigo baku samu wadanda suka fita sau goma ba to maza ku fita ku bar mana wuri sakarkaru kawai,” hafsa tace mu kake kira sakarkaru? to lallai zaka ga aiki irin sakarai ganin idonka,” ta ja hannun fareeda dake ta kuka (wanda inda ace hawaye suna kare wa da tuni hawayen ta sun kafe) suka fita suka nufi gida.

Da yamma inspecta garba ya isa gidan rasheed kamar yadda buba ya sanar mishi sun koma gida, a wani daki mai cike da kayan motsa jiki kala kala inspecta ya same su, Rasheed na ta faman gudu akan gym sanye yake da three quater fari kal da riga mai yankakken hannu dark blue, sai silipas dake kafarshi suma farare, yayinda buba ke zaune gefe daya yana aikin gadinshi, yakai minti goma da shigowa kafun rasheed ya sauko ya zari towel yana aikin share zufar da ta mishi wanka, kana ya karbi glass cup mai dauke da orange juice mai sanyi wanda buba ke mika mishi, zama yayi akan resting chair yana sipping juice din, hannunshi ya daga sama kana ya karkada yan yatsunshi guda biyu idanunshi a lumshe, buba ne da ya gane language din yace wa inspecta zaka iya magana,dan matsowa inspecta yayi yace” yallabai naje na samu danginshi wadanda suka kasance talakawa ne sosai nayi musu tayin kudi 5 million 10million 12 million but they refused to accept nayi matukar mamaki da suka ki amincewa, amma duk laifin wannan yarinyar ne wacce taga lokacin da abun ya faru sai iyayen sunyi kokarin amincewa sai ta karkatar da tunaninsu, tace lallai saidai kaje ka bada hakuri da kanka, tunda inspecta ya fara magana sai a sannan rasheed ya dago kanshi yace” inbada hakuri? woww i like it, inspecta yace kuma tace insanar da kai cewa ITA SUHEER LAMIDO baza ta taba janye wannan karar ba har sai ka fuskanci hukunci ko kuma kabada hakuri.”wannan karon mikewa rasheed yayi yace ” SUHEEEEER, good i like it, ya koma bakin jym nashi ya tsaya zuciyar shi na tafarfasa, ya yafito inspecta yace “hau” inspecta yace me zan hau”? gym din ya nuna mishi ba musu ya hau ya tsaya, take rasheed ya kunna makunnin, aiko inspecta bai ankare ba yaji shi yana ta gudu kara karfin gudun yayi sosai sannan yace ka maimaita abunda ka fada”,

Nan inspecta ya fara maimaitawa yana jin duniyar tana juya mishi gudu abun yake bana wasa ba tun inspecta na gane abunda yake fada har ya dena sai zufa ke karyo masa a duk hudar gashin dake jikin shi, ganin ya galabaita sosai ne yasa rasheed danna makunnin kiiit ya mutu take inspecta yayi wani irin katantanwa ya tiku da kasan tiles sai ga hakoranshi biyu na gaba a kasa, wani dan siririn sarka ne yayi tsalle daga aljihun inspecta lokacin da ya fado,bai tsaya ko ina ba sai jikin kafan rasheed, hannu yasa ya dauki sarkar yana kare mishi kallo kafun ya dawor da kallonshi kan inspecta dake kwance azabar fitar hakori na dibanshi takowa yayi gabanshi hadi da nuna mishi sarkar ” da gyar ya dago kai yace ita ta bayar a kawo maka tace ince maka kasa a wuyanka ka ka zauna a gida kayi girki domin mata aka sani da tsoro, wani irin karkata kai rasheed yayi yana kara kallon sarkar kamar mai son ganin fuskar mai shi a ciki, wani munafikin murmushi yayi sannan ya kalli buba yace ” saina sa SUHEEEER LAMIDO ta saka wannan sarkar sau dubu amma ni nawa na azaba ne bana zama gida da girki ba”, gyada kai buba yayi yace “duk yanda kaso haka zakayi boss.”

Nuna inspecta dake kwance wahala ya isheshi rasheed yayi yace “a fitar min dashi,” angama ranka ya dade cewar buba, zuwa yayi ya kama shi da kyar tsabar aukinsa, buba aranshi yana cewa dole hakora su fita ae irin wannan cin kasa haka da wannan uban nauyi, haka ya lallaba ya kawo shi waje ya zubar kamar kayan wanki, tashi inspecta yayi yace “lallai zakasan kayi da dan halak”. bani musa garba ka taba ba,? zaka sani ne ba’a yi bama ina nema ballantana kuma anyi.

Wayar shi ya ciro a aljihu wandonshi wasu lambobi ya tattaba kana ya kara a kunnenshi, yace hello khamees ina bukatan yan jarida masu zaman kansu…..,

Fareeda na zaune a gida tun bayan dawowarsu tayi kuka har ta gode wa Allah, tun amminta na rarrashinta har ta gaji ta barta, dama anty hafsa kam suna dawowa dakinta ta shige ta kulle kanta tana ta zaune a palo taji ana knocking kofar ammi dake jera wasu kayan da aka dawor mata daga sari ne ta dago kanta tace ” jeki ki bude kiga waye, tace ” ammi jikina ba karfi ki kira sweetheart mana, ammi tace suheer ta fita sayan biredi tashi ki duba ko ni intashi,?

A hankali ta tashi tana jin kamar iska zai kada ta ta nufi kofar ta murda makulli ta bude kafun ta ankara taji karan saukar camerori ta ko ina daukan ta ake yi daga masu hoto sai masu video rikicewa tayi yan jarida ne sun kai su goma kowannensu dauke da abun magana, tambayoyi suka fara jefo mata a tare a tare tun wani ya gama wani ya jefo nashi tambayar

Madam kozaki iya gaya mana abunda kika gani a lokacin da abun ya faru.?

Did you personally meet Rasheed matawalle.?

Is there any pressure on you from his side?.

Shin ko akwai wani magana da kukayi dashi baki da baki?.

Ya fada mana yana son yayi solving wannan matsalar ta hanyar tattaunawa, ko kinga alamun hakan?.

Plsss madam ki bamu amsa. Plssss maam answer our question..
Wannan sune irin jerin tambayoyin da taron yan jaridar suke yiwa fareeda wacce gaba daya ta rude gashi sai faman daukanta hoto sukeyi duk sun kashe mata idanu, daddagewa tayi ta k…………,
????????????AUREN FANSA????????????

BOOK ONE

NA

Ummu Fadeela

Typing????

Page 25

…….Ihu ta kwala da iya karfinta tana toshe kunnuwanta, a tare ammi da anty hafsa suka fito har suna karo da juna. Hada baki suka yi wurin tambayar meke faruwa a wurin? fareeda dai ta toshe kunne hadi da rumtse ido yayinda yan jaridar ke cigaba da jero mata tambayoyi,.

Wani daga cikin su ne yakuma cewa ” hajiya ko zaki iya fadawa duniya yanda abun ya kasance tsakaninki da Rasheed matawalle,”?

Rasheed? anty hafsa ta fada a zuciyar ta, da sauri ta ja hannun fareeda suka shige cikin palon hade da banko kofar suka bar yan jaridar a waje, kallon fareeda tayi tace ” me wadannan suke fada ne? kamar sunan rasheed naji sun kira ?” sai a lokacin fareeda ta dawo cikin hankalinta tace ” inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un, wayyo anty hafsa na shiga uku! abunda kika fadawa p.a nshi dazu ya iso kunnenshi, hasbunallahu wani’imal wakeel, shikenan yanzu bazai barni in shiga masana’antar kallowood bama gaba dayanta balle in fito a fim tare da shi, wayyo anty hafsa kiyi wani abu akai, duk ta rude gaba daya ta fice a hayyacinta, ammi dai sai kallonsu take yi, da sauri hafsa taje ta bude kofar palon daman yan jaridar sunan tsaye cirko cirko a wurin, suna jin an bude kofar suka yo kanta, da tambayoyi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button