AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan kwana biyu ummie na zaune kan kujerar dake gaban gadon da rasheed ke kwance, bacci yake amma da ka ganshi kasan ko cikin baccin hankalinsa ba kwance yake ba, fuskarshi tayi fayau ya rame sosai kamar ya debi wattani a kwance, tunanin abunda likita ya fada mata take wai rasheed nata na gab da kamuwa da ciwon zuciya matukar ba’a sama mishi abunda yake so ba, ammi da kawu lamido ne suka shigo dakin dukkansu sun rikice ganin yadda rasheed yake jin jiki,….Nan suka zauna suka tattauna mafita inda daga karshe suka yanke shawaran da suke ganin shine daidai.

A haka aka gama bikin fareeda suka wuce london da angonta,suheer kuwa ta dan samu sauki saidai ba sosai ba, yanzu duk abunda taci dawowa yake,dan bread dinma yanzu bata iya cinsa,laulayi take yi mai zafin gaske, cikin haka su ammi suka maidata gidan rasheed bazata iya musa musu ba dan basuyi mata wannan tarbiyar ba, saidai ta sha alwashin da kanshi zai dawor da ita,…Duk wani irin alwashin da suheer tasha yabi iska duk tsiyar da ta tashi aikata mishi da ya manna ta da kirjinsa dai shikenan tayi shiru, wataran ma saidai yaji minsharinta tayi nisa a bacci, da wannan daman yake samu ya mori abarsa son ransa, saida cikin suheer ya shiga watanni shida kafun laulayin ya dan tsagaita mata, sai wani irin kumbura da cikin keyi, idan ka ganta saika zaci nanda awa daya zata haihu tsabar girman cikin,hakan yasa rasheed yake tausayamata sosai yanzu hatta wanka shi yake mata, ga wani uban ci da take kamar gara yanzu zata ci yanzu tace yunwa takeji…

Bayan wata tara, suheer na kwance duk tayi laushi da kyar take iya ko magana girman cikin kuwa zaka dauka yaya goma ne a ciki, idan ka ganta dole ta baka tausayi, rasheed ya shigo yazo ya tsugunna a gabanta yana shafa kumburarren fuskarta, tausayi take bashi bil hakki, ji yake kamar ya cire mata cikin ko zata huta itama,a hankali ta bude idanunta ta kamo hannunshi dake yawo a kan fuskarta, yace “sorry wife, insha Allah zaki sauka lafiya kinji, girgiza kai tayi tace Allah yasa, in kuwa abokin tafiya ne ina rokonka gafara,. Take idanunshi suka kada jawur yace “no wife bazaki tafi ki barni ba ke din rayuwa ta ce, matukar kika barni to banda sauran amfani, murmushi tayi tace “hmmm ban yarda ba, yace “serious Ayshhha na fara sonki ne daga ranar da na fara ganinki a bakin hanya randa na buge wani wawan da yake miki murmushi, na buge shi ne sakamakon kallon ki da nakeyi, believe me ina sonki da gaba daya zuciya ta,wani sanyi suheer taji yana ratsa zuciyarta, ta lumshe idanu tace thank you, amma ya ake ciki da batun case din da ka shigar, yana murmushi yace “yanzu haka ma daga station nake, gobe za’a fara zama a kotu insha Allah, tace Allah ya bamu sa’a.

Zama biyu akayi a kotu,bayan sauraren kara da hujojji daga bakin lauyers kotu ta yankewa alaji umaru hukuncin daurin rai da rai,ba karamin farin ciki ahalin suka shiga ba, alaji umaru yana ji yana gani aka mika shi gidan maza for death.

Cikin siririyar muryarta tace “habeebi are you there”? lumshe idanu habeeb yayi duk lokacinda sameera ta kira shi da wannan sunan sai kirjinsa ya buga, ya kanji kamar suheer ne ki kiransa da wannan dalili ne yasashi fara kulata, har yanajin zai iya amsar soyayyarta kamar yadda take rokonshi tun farkon zuwanshi gidansu, sameera diya ce daya tilo a wurin alhaji abubakar dan chanji babanta yana dan chanji ne yana da masifar arziki tun da habeeb ya bar kano motar Adamawa ya shiga koda ya sauka a jimeta cikin rashin sanin inda ya nufa, tsautsayi ya sa motar alhaji abubakar kade shi tunda ga lokacin yake gidan har yanzu, ganin irin amincin da yake dashi ne yasa alajin daura shi kan wasu harkokinsa,tun daya fahimci baida wurin zuwa, a haka Allah ya daurawa sameera kaunarshi, sai muce Allah yabada sa’a.

             BAYAN SHEKARA BIYAR..

Wasu yara na gani kyawawan gaske twins mace da namiji suna ta tsere a cikin wani kayataccen palo,suheer ta fito daga kitchen ta rike kugu tana kallonsu wani tsawa ta daka musu,duk suka nutsu, tace “cikinku waye ya shiga kitchen yamin barnar madara, cikin zakin baki macen tace “mommy ASHRAF ne, shima Ashraf yace mommy Allah ASHFAT ne, kowa yace dan uwanshine suna ta zare idanu, rasheed ne ya fito sanye da kayan bacci, yana kallonsu yace dearies me kukayiwa sweetheart take fushi, duk sukayi kanshi a guje wannan yace wannan ne dayan ma yace wannan ne, yace Ok to duk muje muba mommy hakuri, kneel down sukayi a gabanta har da rasheed din suka kama kunne suka hada baki wurin fadin sorry mommy, ta dungurewa yaran kai tace “Ashfat nasan ke ce da wannan barnar ai,rasheed yana kallonsu yace “oya a je ayi home work kar a kara yiwa mommy barnar madara, bayan sun wuce rasheed ya lakace mata hanci yace “ai ke ta dauko mommy” turo baki tayi, cakk ya dauke ta ya shige daki ya rada mata a kunne “yau fa zan baki wasu twins din, dariya tayi, kawai.Rayuwa yayiwa iyalan dadi gaba dayansu sunje morocco inda suka tadda wasu daga cikin dangi wasu kuma sun mutu a yanzu fareeda tana da yaya uku kuma suna zaune lafiya a london da mijinta da yan uwanshi,kuma tana aiki da wani NGO, su ammi ma suna zaune lafiya da juna, yayinda suheer tunda ga kan twins bata kara haihuwa ba a cewarta sai ta gama karatun likitancin da ta fara wanda yake gab da karewa yanzu.

 ALHAMDULILLAH...

Nan na kawo karshen littafin AUREN FANSA. Abunda na fada daidai Allah ya bani ladan shi, inda na kuskure Allah ya yafe min ya shafe shi cikin aiyukana.Dubun godiya ga masoya na wadanda suka daure,suka jure through thick and thin suka bibiyi labarin nan,Alherin Allah yakai gareku. Godiya ta musamman ga yan group na ummu fadeela novels da kuma ruqayya ibrahim matar makaho novels, comment da likes naku yana burgeni Allah ya bar kauna, mutane na na amana yan AUREN FANSA Whatsapp group jinjina a gareku kaunar ku na musamman ne a zuciyar ummu fadeela, ina jin dadin sharhinku Allah yabar zumunci idan nace zankiraku daya bayan daya sai mu kwana, amma ku sani ina sonku irin sosai dinnan.

Litaffin AUREN FANSA sadaukarwa ne ga Anty na abun alfahari na,Anty ADAMA, alherin Allah yakai gareki,Allah ya kara miji juriya da jajircewa.

Littafin auren fansa kyauta ne idan kin karanta kinji dadinsa kimin addu’a.duk wanda ya sayar min na barshi da Allah. And ku sani there’s power in toungue.
Watch out for my new book Insha Allah…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button