AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushin nasara inspecta da ya juma bakin kofar dakin asibitin yayi sannan ya tura kofar ya shiga, yana shafa tumbinsa.duk dago kai suka yi suka kalli kofar, karasowa yayi still smilling ya samu wuri ya zauna yana karkada kafa, su sun dauka dacta ne shiyasa sukayi shiru dukkansu suna kallon shi.

Dan muskutawa yayi bayan ya gama studying nasu yace” mala mamman ya mukaji da abunda ya faru cikin tsadan rayuwar nan kuma? mamman yace to mungode wa Allah kaddara ce bata wucewa lokacinta, ni yanzu fargaba ta ma yanda zan biyaku kudin asibitinku wllh, ba komai gareni ba dama shine karfin gidan namu gashi yanzu yana kwance Allah kadai yasan randa wannan kariya zata warke, har ya fita ya fara aikinsa. girgiza kai inspecta yayi pitifully yace” ashhaa kace shine ke rike da gidan kenan dama baida wani takamammen aikin yine? asabe ne ta karbe zancen da cewa” dan girman Allah dacta ka dubashi ka fita ka bamu wuri, ya muna cikin tashin hankali zaka xo ka karamana, juyowa yayi yace mama ba tashin hankali nazo kara muku ba, hasalima nazo in fitar daku a tashin hankaline, ido suka zuba miahi dukkansu hade da tambayar ta yaya?.

Yace yauwa yanzu kuka yi magana, sunana inspecta musa garba, ni dan sanda ne kuma a hannuna case din hatsarin danku yake, yanzu ina son insan ta yadda zaku iya biyan kudin asibitin habeeb har zuwa warke warshi kuma ta ya zaku yi rayuwa kafun ya warke har ya fara nema muku abunda zaku ci?

“Kamar yadda kowane talaka wanda ya dogara da Allah yake rayuwa”.

Suka ji an fada daga bakin kofa duk dagowa suka yi suka kalli suheer dake shigowa, tace me kake kokarin fadane inspecta hope dai ankama wnn mai motar, dariya yayi yace” yan mata kenan baki san waye kike fada dashi ba, don haka yanzu ba wurinki nazo ba ki bari in gama magana da masu yaro, ya juya ya kuma kallon asabe da mamman,yace,” nasan baku da amsar tambaya ta dan haka kamar yadda nace nazo in fitar daku daga damuwa ne, don haka zan biya muku kudin asibiti daga yanzu har danku ya warke, sannan zan baku naira na gugan naira har million biyar, kawai abun bukata shine ku janye case din da yarinyar nan ta shigar jikin asabe ne ya fara daukan rawa yayinda mamman ya sake baki kamar yaga abun mamaki domin shidai a tsawon rayuwar shi bai taba kallon million5 ba balle ya rike su, karfin halin saisaita kanta asabe tayi sannan baki na rawa ta kalli mamman ta nuna mishi inspecta tace ji…..jish.. jishi yana maganar million 5 kamar…….. Katse ta inspecta yayi yace na kara million biyar ya zama goma wannan shine karshen farashina, zare ido suheer da habeeb da kuma maryam sukayi yayinda asabe ta sharce gumin da ke tsatsafo mata a goshinta da bakin mayafinta, Jikinta yana rawa taceee……

Ina godiya da kulawar ku fans, bana jin dadi ne shiyasa jiya kuka jini shiru, amma Alhmdllh ina samun sauki, what’sapp people naga sakonnin gaisuwarku, da wadanda suka bini private da wadanda suka gaisheni public duk na gani kuma na gode Allah ya bar kauna, one luv guys,

Sai daku alkalamina yake zama alkalami, sharhinku shine karsashi na. ina yinku irin sosai dinnan.???? kuyi hakuri idan kunga typos banyi edit ba.

Where is Rasheed fanssss????????????.
????????????AUREN FANSA????????????

BOOK ONE

  NA 

ASMA’U MAI ANGUWA

  Ummu Fadeela

Typing????

Page 23 / 24

….Jikin asabe naci gaba da karkarwa ta nuna inspecta da yatsa tace” ji shi yana maganar million goma kamar wani abun azo a gani, rayuwar dana daya kwal a duniya kake hada wa da banzan million goma?… Daya kashe min shifa? ba don Allah ya takaita ba me kake tunanin zai faru? ka banke mutum da mota sannan kayi wucewar ka, wannan zalunci ne kuma bazamu yadda da hakan ba,” ta karisa tana ta hada uban zufa yayinda kirjinta yake ta bugawa da karfi da karfi.

Inspecta da baiyi zaton jin haka da ga gareta ba, da mugun mamaki yace, “karki biyewa wnn yarinyar kiyi gaggawan yanke hukuncin da zaku zo kuna nadama, wannan abune da zai taimake ku gaba dayanku, kuma da kikace da ya kashe shi, naga ai bai kashe shinba gashi nan a gabanki.a harzuke suheer ta taso zata yi magana, amma asabe ta dakatar da ita ta hanyar cewa ” barni da shi yannan nasan yadda zanyi dashi”, ta nuna inspecta da yatsa sannan ta nuna kofa tace “ga hanya bama bukatan kudinka anan, kallon su yayi yana murmushin mugunta yace “million 12 ku janye case,”

Zuwa lokacin jikin asabe ya tsananta rawa don har wani zufa ya mata wanka gajab,( a ranta tana nanata million12! wayyo Allah garin dadi na nesa),

Mamman ne yace tunda ance ba’a so kayi ta kanka kawai, kaje kayi aikin da gwamnati ta dauke ka domin shi,

Suheer ta kuma mikewa tace “a maimakon kudin da ya turo ka ka bayar kace mishi yazo ya bada hakuri kawai ya isa tunda ya na tsoron hukunci, yazo ya tsugunna yaba shi hakuri that’s all, inba haka ba kuma kace mishi, NI SUHEER LAMIDO, nace bazan taba janye wannan karar ba har sai an yanke mishi hukunci, inspecta ya girgiza kai yace lallai yarinya baki san waye kika tunkara ba, tace” bansan waye ba,kuma bana bukatar sanin waye, amma ina da karamin sako dana keso ka kai mishi,”…dan siririn sarkar da ke wuyanta ta cire ta kamo hannun shi ta saka a ciki, tace”ka kaimishi wannan kace yasa a wuyanshi ya zauna a gida yayi girki domin mata a ka sani da tsoro, … ………..(TOHFAA)……………..

Kallonta kawai inspecta yake yi, yana mamakin karfi halinta, kwafa kawai yayi sannan ya juya ya fita.

Mamman ya dubi asabe bayan fitar inspecta yace “amma asabe baki taba burgeni irin na yau ba, duk da bala’in son kudi irin naki amma kin nuna yau rayuwar habeebu yafi miki kudi amma gsky naji dadi sosai”, ta wutsiyar ido ta kalleshi tace” inganka a waje” yace me kikace?” tace inason ganinka a waje nace” au to toh muje, fita sukayi asabe taja kofar ta rufe ta matso kusa da mamman sosai da magana kasa kasa kamar munafuka tace “kasan me ya sa nayiwa polis dinnan haka?, girgiza kai mamman yayi, tace so nake mu samu million 20 a wurinsa, domin duk yadda akayi mutumin da ya buge habibu ba karamin mai kudi bane, kaga fa cikin minti talatin daga miliyan biyar har yaje miliyan goma sha biyu, to me tunaninka inmun ja abun yayi kwana daya,? da mugun shock yake kallonta yace”amma asabe ban taba tsammanin halinki ya kai har haka ba,.”

Fareeda ta gama shirya wa tsaf da ita tayi kyau iya kyau sai baza kamshi take yi,cikin taku dai dai ta fito palon tana kokarin daidaita jakarta a kafada, da kallo ammi da aunty hafsa suka bita, ganin irin kyan da tayi kamar amarya ranan budan kai, masha Allah, fatabarakallahu ahsanul qhaliqin, cewar ammi tana shafa kan fareeda da ta matso kusa da ita, Allah yabada sa’a kici gaba da kiyaye wa kinji dota na Allah ya miki albarka, da ameen ta amsa sannan suka mike ita da anty hafsa suka tafi don yau ne fareeda zata je audition na wani fim wanda Rasheed ne star a ciki, wannan shine babban burinta dama, lokacin da suka iso ba karamar tsorata fareeda tayi ba, ganin irin taron manyan yan mata masu ji da kansu wadanda suka fita komai zazzaune kuma dukansu irin role da take nema suma shi suke nema, a haka suka zauna duk tana tsorace, badon anty hafsa dake wurin tana encouraging nata ba da tuni ta gudu, a haka har layi ya iso kanta, tashi tayi ta shiga dakin da ake daukan, nuna mata abunda ake bukata tayi mai kula da bangaren yayi, lokacin da aka seta camera a kanta tuni ta firgice ta soma karkarwa jiki, da ta bude baki ta fara magana kamar yadda aka umurce ta sai muryarta ya fara stammering, ” Action” mai bada umarni ya fada, sai kawai ta kara rikicewa, yakuma fadin “Action” take hawaye ya balle mata ta ringa kuka kamar zata shide sauke camerar akayi directorn yace taje ta daidaita kanta anbata 30 minutes idan ta kasa to that’s final, saidai wani fim din kuma amma wannan kam ya wuceta, fita tayi jiki a mace tana ta aikin share hawaye, na gaba ne ta mike cike da yauki ta shiga.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button