AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sake matsowa kaɗan nayi yanzu bala ne ke magana yace” sama’ila kenan tunda kana tsoron bata ai sai ka bari ta haifar maka ɗiyar kawai ” sama’ila yace ta haifa min fa kace? ashe baka da tunani, ya muna maganar hankali kana sako mana shirme a ciki.

Ɗan dariya bala yayi yace” to me zance inba hakan ba? sai kawai ka bari ta haifu kaga daga nan sai komai ya faru ko?.
cikin mutuwar jiki alaji samaila yace”bazan yadda inrasa komai ba, bazan rasa dukiyata da sarauta ta ba, kai kanka bala kana ganin yadda arziki na yake ta kara hauhawa sannan ina ɗaya daga cikin masu faɗa aji a wannan yanki gaba ɗayanta, kuma wannan shine abunda nake nema dama kuma na samu, kai kasan haihuwar hauwa daidai yake da rasa komai nawa,haka mutuminnan yace kuma a gabanka ya faɗa. (wa’iyazu billah) shiya ɗauka bokan ke mishi yana tsoron saɓa masa amma baya tsoron sabawa ubangijinshi , yana iƙirarin kar boka ya kwace dukiya da mulkin da ya bashi, ya manta shima bokan Allah ne yayi shi kuma bai isa ya motsa koda ɗan yatsanshi ba face da izinin Allah.
(Allah ka shiryemu kaba mu ikon gujewa saɓama ka, ka bamu abokai na gari.)

Samaila yace “saidai kamar wannan dukiya bata min amfani bala, ina amfanin dukiya ba ƴaƴa, kodai komawa zamuyi wurin shine ko zai sassauta min wnn sharaɗi” lallai baka da hankali inji bala ” yanzu kai har ka manta irin abunda aka mana lokacin da muka koma kan neman sassaucin sharaɗin nan? ido alaji ya zaro tuna irin azabar da boka yasa aljanu suka gana musu da bulali.

Yanzu me mafita ya kuma tambaya shi.
Bala yace mafita kawai a bata wancan maganin itama tasha amma kayi taka tsan tsan karka zuba mata dewa,ina ga itama balki kayi zari ne wajen zuba mata shiyasa a ka samu matsala. kai ya jinjina alamun gamsuwa, zuwa wannan lokaci zufa yagama jiƙani sharkaf, yayinda jikina keta mazari kamar ana ƙiɗa min ganga, ƙwaƙwalwata kuwa ta kasa aiki yadda ya kamata sai nanata min kalmominsu take , kamar. balki, ciki, mace, boka ,magani,sharaɗin boka, suka ɗai take ta aikin nana ta min duk na fice a haiyacina, na rasa abunda zan kama na kasa daidaita maganar su a kan mizani, a hankali naji kamar ana zare min lakar jikina, guiwa ta kamar ansa gatari an sare ta,jinake kamar ina tafiya ƙasa kamar kuma ina yawo a kan iska, sai kuma naji kamar ƙasar wurin tana daɗa yin ƙasa dani, banyi aune ba najini gwajab a ƙasa, still ina jin kamar kasar tana tafiya dani can ciki.

Ƙarar faɗuwar ta ne ya janyo hankalin alaji samaila da bala dake cigaba da tattauna damuwar su, izuwa bakin ƙofar.juna suka kalla sai kuma cikin hanzari suka miƙe haɗi da nufar inda suka jiyo ƙarar. cikin karfin hali na yi yunƙurin tashi jin takunsu suna kokarin cimmani k…………..

Follow this link to join my facebook group????????????

https://www.facebook.com/groups/299890475435292/?ref=share
????????????AUREN FANSA????????????

BOOK ONE

NA

Ummu Fadeela

Typing????

Page 10 / 11

Nayi kokarin neman maɓoya kafun su cimmani amma hakan ya gagara sakamakon jiri dake ɗauka ta duk kuwa da cewa a zaune nake,. koda suka iso wurin zaune suka tadda ni dafe da kai, kallon juna suka yi, sai kuma alaji ya miƙa hannu da nufin ɗago ni, duk da ina cikin wani hali hakan bai hanani watsa masa wani mugun kallo ba, ina faɗin” kada ka kuskura ka taba ni, mugu kawai, azzalumi, tir da kai tir da hali irin naka.

Insha Allah sai ka ga karshenka, domin Allah baya zalunci kuma ya haramta yinta a tsakanin bayinsa, sai Allah ya saka mana tun a duniya zaka gani kuma.” na yunkura na mike da kyar ina dafa bango har na shiga cikin gidan.

Koda hauwa ta wuce da ruɗani alaji ya kalli bala wanda da alama shima cikin ruɗanin yake, yace.”bala taji komai wallahi taji komai shikenan tawa ta ƙare nasan saita tona min asiri, me abunyi bala? na shiga uku na lalace wayyo dukiya ta da sarauta na “abunda yake ta faɗa kenan yana zagaya wurin kamar mahaukaci. bala dake tsaye wuri ɗaya kyam kamar statue yayi karfin halin kamoshi suka koma inda suka taso suka zauna, shiru sukayi naɗan lokaci kowa da abinda yake saƙawa a ranshi.

Can bala ya nisa yace” tabbas taji abunda muke faɗa kuma dole ta tona mana asiri amma mezai hana mu…..ya taso ya raɗa masa wani abu a kunne yana munafiƙin murmushi, kaga babu mai zarginka.

Tsoro ne ya bayyana karara a fuskar sama’ila yace” anya kuwa bala wnn mafita ce? ba ƙara ɓata al’amarinnan zamuyi ba kuwa? don kuɗi ba damuwa ta bace amma ina tsoron abunda kaje ya dawo, Gaskiya abunnan ya fara fitar min daga rai bala, ga kuɗi ga mulki amma bani da kwanciyar hankali da na ruhi, babu wani abunda zan kalla cikin gidannan inyi farin ciki, kafi kowa sanin yadda nake kaunan ƴaƴa amma sai zubar dasu nake yi duba kaga gidannan kamar kango wanda gobara ya lamushe ,ya fara isata haka nan bala ina son ganin gudan jini na nima.

A fusace bala ya miƙe yace” yaushe ma aka ci larabar bare jumma’a tazo samaila? to ai shikenan idan komai ya dagule maka karka kuskura ka nuna ka sanni, sannan ina maka tuni da cewa idan ka tsallake dokar mutuminnan hatta rigar da zaka sa saita gagare ka . dan haka na barka lafiya kayi duk yadda kaga dama.

Ya juya da niyyan tafiya saidai kafun ya isa kofa alaji ya iso shi, cikin kwantar da murya yace haba aminina ya za kamin haka, ni nasan inda kaine a matsayina iya matakin da zaka ɗauka ken…. dakata” bala ya katse shi yace” inda nine kai babu abunda zai dameni ga tarin dukiya ga ɗaukaka duk inda nabi jama’a na dago min hannu me zai dameni, inci mai kyau insha mai kyau in kwanata mai kyau. don kawai rasgin ƴaƴa, mene sabon abu a ƴaƴan daza ka bi duk ka ɗaga hankalin ka.

Samaila yace” to yanzu yaza’ayi ” wani ajiyan zuciyan samun relief bala ya sauƙe ,( bala yana ƙara tunzura samaila ne domin abunda yake samu a jikinshi kusan 50/50 suke yi da dukiyar). ya kalleshi da fara’a yace ” kawai shawaran da na baka da farko shi zamu bi, don haka kuɗi kawai zaka fitar”. anan wurin alaji yabashi adadin kudin da ya ambata suka rabu.

Koda hauwa ta koma cikin gida da kyar ta iso ɗakinta ta faɗa kan gado, wani kuka mai cin rai ne ya zoma ta nan ta ringa risgar kuka har magriba ya risketa tana cigaba da kuka har isha yayi, zuwa wannan lokaci ta rasa duk wani karfi da kuzari na jikinta,idanunta sunyi luhu luhu ga wani irin sarawa da kanta keyi tamkar zai ɓalle, da kyar ta iya miƙewa ta kunna torchlight ta haska agogo wanda ya nuna mata sha biyu na dare ” ya salam ” ta furta tana dafe kanta sannan ta nufi waje ta ɗauro alwala ta shigo ta shimfiɗa sallaya ta kabbarta sallah tayi sallolin da suka kubce mata, sannan ta haɗa da shafa’i da wutri a sujjadanta na karshe ta daɗe tana kai kukanta ga Rabbus samawati sannan ta dago ta sallame tayi sauran adduo’inta.

Anan kan darduman tayi kwanciyarta tana ta karanta zikiri har bacci ya ɗebeta mai cike da nutsuwa ba tare da ta kulle kofa ba.

Cikin bacci taji alamun mutane a tsakar gidan, can kuma taji ana magana ƙasa kasa, sai kuma taku zuwa bakin kofarta
Thats how hauwa passed away.

Washe gari aka tashi da jimamin mutawar hauwa sakamakon barayi da suka shiga gidan sarkin noma da niyyan sata suka kasheta, nanfa jama’a suka fara zargin tabawa da cewa ita ce ke kashe abokan zamanta domin kar su haihu su gaje dukiyar samaila tunda ita kowa yasan bata haihuwa, har wurin zaman karɓan gaisuwa yada mata magana akeyi, da haka shiga jama’a ya fara gagarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button