AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Suprisingly yace “amma boss a ina ka taba ganin anyi haka?, inace mata ke zuwa daukan amarya?,….. a fusace rasheed ya juyo yace “kai ina ka taba ganin aure irin na rasheed tunda kake a tarihi? so kamar yadda rasheed yake na daban hakama komai nashi yake na daban, ina fatan ka gane? so maza kamin sallama da ita ko kuma ni inshiga da kaina in daukota mu tafi.

Da dan sauri buba ya bude motar ya fita, ya kai minti biyar tsaye a kofar gidan yana tunanin yadda zai afka gidan mutane jibgege dashi wai yazo daukan amarya, “what naughty thing,”.

Dan tsaki rasheed dake zaune cikin motar yana hango buba tun dazu yayi kana ya balle murfin motar ya fito yana taku cike da izza wanda hakan yake hallitar sa ce har ya iso ya shige gidan ba tare da ya kula buba wanda ya zaro ido ba, da sauri ya bishi zuwa ciki.

Hajiya saratu ta kalli ammi tace “anya haj, adama yau zasu zo daukan amaryar kuwa? kodai….Bata kai aya ba duk suka juyo sakamakon bude kofar da akayi buba ya sungunar da kai kasa da kyar ya samu ya lallaba rasheed ya koma shikuma ya shigo yace “barkan ku da hutawa hajiya munzo daukan amarya ne, haj saratu tace “wacce amarya kuma kuda wa kuka zo daukan amaryar su baza su shigo ba sai kai gotai gotai dakai zaka shigo kan mata?…Kara sunne kai yayi yace “a’a hajiya ai mu al’adar mu maza ke zuwa daukan amarya, caraf tayi tace “wace iriyar al’ada kenan wacce mu bamu santa ba a garin kano? maman saudat tace “amma haj kinsan yanzu duniya ta ci gaba fa yawanci ma yanzu andena irin a debi kai jama’a gari guda da sunan wai an tafi kai amarya,” tace “amma dai duk da haka wannan sabon abu ne a wurinmu gaskiya bamusan haka ba, ya za ace aure dai aure na budurwa tsaleliya kamar suheer ba bazawara ba ace anzo daukan amarya haka, kai ai yau ko bazawara marar galihu baza a mata haka ba.Shidai buba kanshi a kasa yana ta Allah Allah kar boss yaji shiru ya shigo dan yasan bawai mi ake nufi da surukai boss dinshi ya saniba.

Cikin nutsuwa ammi dake kallon buba with shock tun dazu ta mike saida ta basu baya kafun ta share hawayen da suka silalo mata, a ranta tana ayyana Allah yasa ba sayar da yanci da mutuncin suheer suka yiba, dakinsu ta shiga ta samu fareeda kwance akan gado idonta a lumshe kamar tana bacci saidai ba baccin take ba hasalima duk abunda ake yi a palon suna ji, suheer kuwa tana zaune ta hada kai da guiwa tana ta aikin shehsshekan kuka…….Nasiha mai ratsa jiki ammi ta mata kana ta daga ta ta samata hijabinta har sun fara tafiya sai kuma ta juyo ta koma ta rungume fareeda ta saki kuka mai ban tausayi, dan shafa bayanta fareeda keyi idanunta a lumshe amma bata ce ko uffan ba, da kyar ammi ta rabasu ta fito da ita, ba karamin kai ruwa rana akayi ba kafun hajiya saratu ta bari a fita da suheer, a cewar ta wannan wani irin aure ne.

Yana jingine jikin motar shi, hannuwanshi biyu harde bisa faffadan kirjinshi kana kafafunshin ma suna harde cikin na juna, sanye yake da kananan kaya as usual kanshi dauke da p cap, ya dan janyo hular gaban goshi don haka ya rufe masa fuska, ta kasan ido ya hango fitowar su duk da darene amma ya fahimci hijabi ne jikinta har kasa, gefe kuma wata ce da bai tantance ba rike da ita tana ta aikin sheshshekan kuka, yayin sa buba ke rike da akwati babba da wani dan madaidaici, dauke idonshi yayi kana ya shiga motar ya budewa buba booth, bayan ya saka kayan ciki ya juyo da dan sauri ya bude bayan motar, hajiya saratu wacce tayi kicin kicin da fuska ta saka suheer ciki,..Kamshin da suheer taji yasa gabanta faduwa domin ta tabbata shine a gaban motar hakan yasa ta riko hannun haj saratu tace ita cikin raunin murya na wacce tasha kuka tace “kema barina zakiyi? din Allah karki tafi,” tace kar ki damu kinji dota ai gobe zamu zo gidan naki Insha Allah, ta juya tana kallon na gaban motar tace “DRIVER karka manta gobe kazo ka dauke mu zuwa can gidan amaryar,rasheed a ranshi yace “Damn it DRIVER! what nonsense ,kana ta kalli buba da ya zaro ido jin an ambaci boss da driver, tace “koda drivern zai manta kai ka tunawa uban gidannaku cewa a zi a dauke mu gobe,ita iya gaskiyarta ta fada dan bata san angonne gaban motar ba, musamman duba da yanayin shigar dake jikinshi, da sauri buba yace karki damu hajiya ya shige motar kafun boss ya aikata wani abun kuma,.

Da mugun gudu yaja motar don saida saratu tayi tsalle gefe in ba haka ba saura kadan ya buge ta……..Kuka kawai suheer keyi duk ta tuno irin nasihar da ammi ta mata da kuma halin da ta bar sweetheart sai taji wani sabon kuka ya balle mata, rasheed kuwa duk da tsananin tafarfasar da kirjinshi keyi na kiranshi driver da wancan matar tayi amma kukan suheer dadi yake mishi a zahiri domin aim nashi kenan, yana son ganinta cikin bakin ciki, amma a badini kuma ba abunda ya tsana irin kuka, kai shi ko kukan jarifi baison ji daga mishi hankali yake yi,…….

A haka suka iso gidan buba dai bai tanka ba domin yasan yanzu haka boss a cike yake taff, kar yayi magana ta pashe dashi. Wangale musu get din mai gadi yayi bayan uban horn din da rasheed ke dannawa, da gudu ya danna hancin motar zuwa cikin gidan, bai kai wurin parking ba ya tsaya ya bude motar ya fito a fusace ya bude bayan motar ya janyo ta, da shike ba shiri ya janyo ta din hakan yasa ta fada kirjinshi, a fusace yace “bullshitt” yana janye ta kana ya rike hannunta gam kamar zai balla ya fara janta zuwa cikin gidan.

Ummie dake zaune tunda safe take cikin zullumi dan ita bata da labarin auren rasheed har saida maigidanta ya dawo dazu yake sanar mata ai daurin auren rasheed sukaje, ji tayi abun ya mata wani bambarakwai, hakan yasa ta wuni cikin tashin hankali gashi tun safen take jiran ganin rasheed amma babu shi babu alamarsa, kamar daga sama ta ganshi ya fado palon yana janye da hannun wata kyakyawar budurwa saida suka iso tsakiyar palon ya watsar da ita kamar kayan wanki, a razane ummie ta nufi suheer da ta fadi kasa zuciyarta na kuna, a fusace tace “wnn wani irin shashanci ne haka, how can you treat a woman like dabba sai kace zamanin cinikin bayi?, ko uffan baice ba itama tasan bazai ce dinba dama, saima wani irin huci da yake yi ya nufi wani dan abu dake makale palon kamar switch dannawa yayi kusan sau hudu kana ya dawo tsakiyar palon yana zagaye ummie dai kallonshi take yi kawai with suprise don wannan ba dabiarshi bace, bayan kamar minti biyar saiga ma’aikatan gidan suna shigowa daya bayan daya suka jeru tsakiyar palon kansu a kasa.

Takowa yayi gabansu ummie yasa hannu ya finciko hannun suheer daya da karfi hakan yasa ummie ta sake ba shiri, janta yake har zuwa gaban ma’aikatan gidan ya turata gaban mai gadi wanda shine a farko yace “wnn shine get man, ya kuma tura ta gaba yace wannan shine driver, ya kuma fura ta gaba yace wnn shine cook a haka har saida yaje kan na karshe yace wnn shine mai ba fulawa ruwa……Sannan ya juyo da ita da dan karfi har saida kafafunta suka yi kara yace yana kallonta ” mutum nawa kika gani anan,”?

Kafeshi tayi da manyan idanunta tana kallonshi, bata ko kiftawa, wani irin tsawan da yasa gaba daya yan falon dimaucewa yayi yace “mutum nawa kika gani anan nace?” a hankali ta dga kai ta kalle su kana ta juyo tace ” mutum tara,” dan shafa goshi yayi yace “wife da alama kina yawan bacci a maths classes naki, wani irin juyawa yan hanjin ummie sukayi a ranta tace WIFE, knn wnn ce matar da ga aura? to meyasa yake mata haka? kafun ta samu amsa taji ya kuma cewa mutum nawa kika gani nace “kara juyawa tayi ta kallesu a tsanake ta kuma cewa tara”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button