AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kai adama ta jinjina,ta sunkuyar da kai kasa, yayinda a bangaren hafsa ba mai iya gane yanayin da ta shiga sabida expression na fuskar ta was so clouded, tun jiya da lamido ya mata batun zuwa gida, duk ta birkice tayi sanyi kamar ba ita ba.hakama yan matan biyu baka tantance yanayin da suke ciki, kallo daya lamido ya musu ya fice daga palon da sauri tun kafin su karya masa guiwa, wannan shine abunda ya dace yayi tunda jimawa a matsayinsa na babba.

Haka kuwa akayi bayan kwana biyu wadannan ahali suka dauki hanyar adamawa, yayinda a bangaren rasheed ya samu rahoton tafiyar su, domin wasu mutane musamman ya samu ya zuba musu makudan kudade suke kai mishi rahoton duk motsin da wani yayi a gidan, don haka kamar a tafin hannunshi su suheer suke rayuwa,.

Har la’asar suka iso Adamawa jimeta yola, yayinda zuciyar adama ke ta tsinkewa bin garin kawai take yi da kallo kamar ba abunda ya canza but komai ya canza, tuno rayuwar da tayi abaya ne yasa ta tsiyayar hawaye, wani karamin hotel sukayi lodging dakuna uku dan su samu su dan huta zuwa gobe sai susan abunyi, bayan wanka da sallah sukaci abinci, sunanan jugum jugum har dare,.

Washegari misalin karfe takwas suka dauki shatar motan dazai isar dasu kauyen su adama, kallonta lamido yayi bayan direba ya tambayeta garin da zasuje har sau uku bata jishi ba, tana can duniyar tunani, fareeda ne taba ta firgigit ta dago ta kalle su, fareeda tace ammi yana tambayarki fa sunan garin da zamuje, a hankali adama tace KAUYEN GORUBA, wani irin shock ne ya kama hafsa da lamido lokaci daya, a tare suka furta kauyen goruba, dariya direban yayi yace da alama kun juma bakuje goruba ba, ai yanzu goruba babban garine baza’a kirashi kauye ba, cikin sanyi suka duru a moyar suka dauki hanya, tafiyar mintuna ne ya kawosu goruba kasancewar hanya ce dodar shimfide da kwalta, lokacin da suka shigo nan adama ta kara yadda da cewa goruba ya tashi daga kauye, domin komai ya chanza, a ciki saidai wasu memory bazasu taba chanzawa ba.

Tamabaya suka shiga yi domin gaba daya kan adama ya kwance ta rasa ta ina zasu bi, garinda ta sani da duk gonakin masara a tsakanin gidaje amma banda yanzu, wani yaro suka tambaya ko yasan gidan sarkin noma? dariya yayi yace ba nisa nan gaba kadanne zakuga wani gida da farin penti to nanne yahi gaba abunsa, a hankali suke bin kwatancen yaron har suka iso gidan adama a ranta taji ba nan bane amma batayi magana ba, sauka sukayi suka shiga gidan aiko ba nan bane matar gidanne tace “kodai gidan samaila tsohon sarkin noma kuke nema ne,? da sauri adama ta gyada mata kai.

Yaro aka hada su da ya kaisu gidan, a bakin kofa ya tsaya yana kallonsu yace “iya kata nan zaku iya shiga, ya juya yayi tafiyar sa, a tare suka bi rubabben gidan da kallo yayinda zuciyar adama da hafsa ya bada wani sauti a tare, gidan yananan yadda yake amma komai ya sauya gaba daya ginin gidan ya rube wani bangaren ma ya fadi kana iya hango tsakar gidan ta cikin buhun da akayiwa kofar kariya dashi, suna cikin wannan yanayin aka daga labulen wani matashin yaro ne da bazai haura shekara sha takwas ba ya fito yana hura fito kallo daya zaka masa kasan ba karamin gawurtaccen dan iska bane, bisa dukkan alamu ma a cikin maye yake, ga wani sharbebiyar wuka a sai walkiya take yi a hannunsa yana kokarin cusa ta cikin wandonsa wanda shi da babu duk daya, kanshi yasha wani aski mai kama dna dujjal domin an kwashe gefe da gefe ne anbar tsakiya, yayinda hannunshi ke rike da wani kyalle mai dan karen wari yana cusawa a bakinshi yana fitarwa, kallonsu yayi da rinannun idanunshi yace cikin muryar maye, ku kuma su waye zaku tare min hanya?, baku san ba’a tarewa DAN BABA hanya bane,? yanzunnan sai in papparka m…….

????????????Auren Fansa????????????

Book two.

         Na 

Asma’u mai anguwa

Ummu Fadeela.

Typing????

Page 37 / 38.

…… Cikin muryar maye yace “sai in papparka cikin mutum kuma in kwana lafiya,!” har ya juya ya fara tafiya cikin tangadi, cakk ya tsaya ya kafe fareeda da jikinta keta makerketa kamar kyanwar da ruwa ya daka, da ido, tsawan second talatin kana yayi wani bahagon dariya, yana nuna fareeda kana ya nuna kanshi, yace “la la la la matar nan kina kama da DAN BABA kodai nine na rikide na zama ke,? yana shafa fuskar shi ya fadi hakan, kana ya miko hannu da niyyar cafko ta, wani wawan tsalle fareeda ta buga gami da kwalla kara, kana ta kankame ammi dake bayanta jikinta na cigaba da karkarwa.

Dogon tsaki dan baba yaja yace “ji wannan don kawai zan duba ko fuskata ne ta koma jikinki kawai saiki nemi cire min kunne, to na bar miki fuskar tawa, ni kuma zan rike taki, ya juya yaci gaba da fiton shi yana tafiya kamar zai fadi kasa.

Sassauta rikon da fareeda ta mata ammi tayi, zuciyar ta na mata nauyi, wani tunani ya bijiro mata, kardai ace Alaji samaila ya samu da namijin da yake buri?, kardai ace wannan ne magajin da alaji samaila yake kokarin kashe ta akai?, kardai ace akan neman wnn ne alaji samaila yai ta sabawa ubangiji, inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un.

Wasu hawaye masu zafi ne suka gangaro mata, bayan hannunta tasa ta share su, lamido ne ya juyo daga kallon da ya bi dan baba dashi , a hankali ya furta “Ya Allah ka shirya mana zuriya baki daya”, kana yace da ammi “Adama ke muke jira ki mana jagora, wucewa gaba ammi tayi rike da hannun fareeda wacce ke cike da firgici, yayinda lamido da suheer suke biye da su, har sun daga buhun da aka yiwa gidan kariya dashi, suheer ta juya hango anty hafsa tayi tsaye kikam bata da niyyar shiga.

Baya ta dawo ta kama hannunta tace “anty hafsa kina ta tsaye kuma duk zamu shiga mu barki,” firgigit hafsa da tayi nisa a tunani ta dago ta kalleta, kama hannunta tayi tace “muje ciki su ammi sun shiga,……..daga kafafunta da suka yi mata nauyi hafsa tayi kana ta fara jansu har suka shiga gidan suma,.

Tsatstsaye suka tarda su ammi dake karewa gidan kallo, dakuna uku ne suka rage a cikin gidan suma gab suke da rasa garkuwarsu, dan daya daga cikin dakunan ma da itatuwa aka rike sa, yayinda sauran gaba daya suka zube a kasa ciki kuwa harda dakin da adama tayi rayuwa a ciki da kuma dakin tabawa, madafa da store store na ajiyan amfanin gonan alaji samaila duk sun zube a kasa, hakama dakunan dake bangaren shi baka hango komai sai kasa jajawur a kwance. ga wasu tarin kwanuka a bakin kwararo kudaje suna ta yarindo a kai, gaba daya tsakar gidan was so dirty, baka jin komai sai wani irin nishi mai karfin gaske dake fitowa a cikin daya daga cikin dakunan.

Wa’alaikummusalamu, muryar wata dattijuwa da ta fito daga bayan wani katakai da’aka zagaye da alama bayi ne, ya amsa sallamar da suke ta kwadawa tun shigowar su, ta na ajiye butar dake hannunta, tace “sannunku bayin Allah baki mukayi ne? ina jin sallamar ku tun dazu na dan zaga ne, wa kuke nema ne?, ba dai dan baba ne ya muku barna ba dai ko.?

Binta da kallo ammi tayi, tana karewa yamushashshiyar fatar ta kallo, idan ka ganta zaka dauka takai shekaru sittin a duniya tsabar yadda ta rame,ta kode, ta jeme, gaba daya ta fice daga hayyacinta, amma a zahiri ko arba’in bata cikaba tsabar wahalar rayuwa ce kawai ya maidata haka. saidai duk yadda ta zama ammi baza ta kasa gane ta ba, domin sune mutane na farko da suka fara taimakonta iyayenta ne suka maida ta ya bayan mutuwar nata iyayen.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button