AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

A hankali ta tashi ta kuma shiga bayi ta ɗan juma a ciki kafun ta fito da sabon alwala, tayi rak’atal fajr zuwa zuwa wannan lokaci anfara sallar asubahi a wasu massalatai, a lokacinne kuma taji alamun buɗe ƙofar palon da sassarfa ta miƙe ta bude labulen taga ta leƙa babban mutum ta gani da waɗannan matasa biyu na jiya sun fita alamar masallaci zasu, a bakin get suka ci karo da mai gadi shima ya fito tare suka fita suka rankaya massalaci.

Ba tare da dogon nazari ba adama ta gyara zaman hijab ɗinta ta sunkuci fareeda dake baccinta peacefully ta buɗe kofar a hankali ta fito, fitowar ta yayi daidai da fitowar mum d………

LIKE COMMENT AND SHARE.

Follow this link to join my facebook group????????????

https://www.facebook.com/groups/299890475435292/?ref=share
Bismillahi Rahmanir-Raheem

????????????AUREN FANSA ????????????

BOOK ONE

          NA 

ASMA’U MAI ANGUWA

   ( Ummu Fadeela)

Typing????

Page 4&5

Sako kanta da niyyar fita yayi daidai da fitowar mum daga dakin daddynsu amaan tana ƙoƙarin shiga ɗakinta, ɗan dakatawa adama tayi sanda taji alamun shigar ta ɗaki da sound na rufe kofa sannan ta sauke wani wahalallen numfashi kana cikin sanɗa ta nufi jikin ginin palon kamar ɓarauniya haka take bin jikin ginin har ta kawo jikin kofar fita, a hankali ta kai hannunta jikin ƙofar glass ɗin ta tura tare da addu’ar Allah sa ya buɗe ba tare da yayi making sound ba.

Cikin ƙiftawar ido fittt ta fice daga palon bayan budewar kofar, da ɗan gudu gudu ta iso bakin wawakeken get ɗin gidan, da bismillah ta ja karamar ƙofar ta buɗe ta, nanma kamar walƙiya ta fice ta miƙe gabas ba tare da tasan inda ta nufa ba, tafiya mai nisan gaske tayi, saida ta tabbatar ta bar yankin anguwar kwata kwata kafun ta tsaya tana maida numfashi, wani ƙofar gida ta gani a kusa da ita mai ɗauke da ɗan karamin varenda nan ta kunce kallabinta ta shimfiɗa a wurin ta gabatar da sallar asubahi, tana cikin yin addu’a taji alamun ana magana a ta cikin gidan, can kuma taji alamar ana warming mashin mai ƙafa uku wato keke napep. ba jimawa aka fito da keken maishi yana ƙoƙarin tada wa kenan yaga kamar mutum zaune cikin varenda ,dallare adama yayi da fitilar keken sannan ya sauƙo ya taho inda take, cikin dakiya yace malama lafiya? daga ina.

Da rawar harshe adama tace ” lafiya nayi sallah ne” yace sallah kuma anan”?

Tace “kayi hakuri ina sauri ne yasa ni fitowa ba tare da nayi sallah ba.”

“Sauri zuwa ina”? ya kuma jefi mata tambayar .

Wannan karon sosai ta rikice ta fara kame kame “amm…..da ….da ….m dama tasha zanje tafiya zanyi. “

“Ina zaki je? Wanne tashar kika nufa?

Duk ya rikitata tace” gari mai nisa zanje shiyasa na fito da wuri dan insamu motar farko.”

Yace ” ohk tashar FARO zaki kenan tashi mutafi kinyi sa’a nima can na nufa kudinki ɗari biyar ne.

Cikin hanzari adama ta miƙe ta ɗaga fareeda dake baccinta bata san me duniya ke cikiba suka shige bayan sahun, take yaja su suka miƙi hanya, ta madubi yaron ke ganin adama dake ta sharar kwalla,can yace “Hajiya sai haƙuri fa haka rayuwar nan take kowa ka gani da tashi kaddara da kuma jarabawar, sau tari zaki ga wasu suna farin ciki, amma inda zasu buɗe miki cikinsu sai kin taya su kuka. So sai muna hakuri, da kuma godiyar Allah a duk halin da muka tsinci kanmu, hala rasuwa akai miki ? ya jefo mata tambayar.

Ganin taƙi cewa uffan shima yaja bakinshi ya tsuke. a haka suka shigo JIMETA sannan ya miƙe hanyar tashar Adamawa sunshine zuwa wannan lokaci gari yafara yin haske. bakin zaninta ta since ta ɗauko ɗari biyar ta miƙa mishi, ta kama hannun fareeda wacce ta farka suka shige cikin tashar .

Wasu dogayen Motoci ta gani jere reras gwanin sha’awa a cikin tashar ko wanne mota a samanta tana ɗauke da wani ɗan box mai ɗauke da sunan garin da motar ta nufa .

Ga mutane ta ko ina ana hada hada kai kace ba yanzu a gari ya waye ba.

Jikin wani mota ta tsaya wanda kusan ma cike yake da passengers, wani ɗan union ne ya tambayeta hajiya KANO ne? dama saura mutum ɗaya motar ta tashi.

A ranta ta maimaita “KANO”!

without thinking twice ta ɗaga fareda tana gyaɗa wa ɗan union ɗin kai ta afka cikin dogon motar wanda ke shaƙe da mutane. batare da taji tambayar da yake mata na “Ina kayanki hajiya” ba, saida ya leƙo bayan ta zauna yakuma tambayar ta a hankali tace masa “ba kaya” kai ya gyaɗa kana ya faɗa mata kuɗin kujerarta.

Dama kuɗin suna ɗamƙe a hannunta tunda ta ba ɗan sahu bata maida su ba nan ta ƙirga adadin abunda ya faɗa ta miƙa masa tana ƙarewa naira ɗari da hamsin da ya rage a hannunta kallo.

Jan murfin motar yayi ya rufe ta gam bayan mintunan da basu wuce biyu ba driver ya shiga yatada motar suka bar tashar.

Lokacin da suka hau kan babban kwalta iska ya fara kaɗa su sai adama ta kwantar da kanta bisa motar tana kallon bishiyoyin dake wuce wa da gudu, ta lumshe idanunta tana shafa dogon gashin fareeda dake bisa ƙafafunta,

Tana mai tambayar kanta .
Ko me rayuwa ya tanadar min?

Wacce irin ƙaddara ce ta ƙira ni zuwa kano jahar da ban taɓa zuwa ba koda a mafarki ?

Shin anya banyi kuskure ba kuwa na tafiya da yar mutane inda ni kaina banda tabbas ɗin ina na nufa.?
Ya Allah ka kawo min ɗauki.

( To ina yan kanawan dabo, gadai adama da yarta da kuma tirtsetsen cikinta, da naira dari da hamsin da ya rage mata kan hanyar zuwa gareku , da fatan kun tanadar mata GURASA, tunda ta guji FURA DA NONO. lols????)

Kafun muji ƙaddarar data lula da adama da ƴaƴanta kano bari mu koma baya kan tushen labarin domin samun sauƙin warware zare cikin abawa.

Flash back….

…. Malam idrisu da mai ɗakinsa zainaba asalin fulanin Adamawa ne cikin yola town, malam idrisu dai manomi ne dake zuwa tafiya ƙauyen goruba yin noma a duk sanda damuna ta tsaya, malam idrisu bai ta shi yaga dabbobi na kiwo a gidansu ba kamar yadda yake a akasarin gidajen fulani,(wannan yana nuna mana cewa ba kowanne ba fulatani bane makiyayi ,akwai fulani manoma, kamar yadda akwai wasu ƙabilu makiyaya).

Malam idrisu ya faɗa harkar noma ne ta dalilin amininshi malam yusha’u ɗan asalin ƙauyen goruba, inda ya fara da bashi aron gonanshi na gado yake nomawa wanda sannu a hankali ya har ya mallaki nashi gonar. wasa wasa noma ya karbeshi, inda daga bisani ya tattara matarshi zainaba da ɗansu guda ɗaya tal da Allah ya basu suka koma goruba da zama domin yaga amfanin noman damuna yanason ya fara noman rani,

Sama’ila yaro ɗaya tal da Allah yaba malam idrisu, ya taso yaro sangartacce kasancewar sa shikaɗai a wurin iyayensa, haka ya taso ba arabi, ba boko, baisan yi ba, bai san bari ba, iya yaren da sama’ila ke fahimta tun yana yaro shine kuɗi, shifa kuɗi su shigo kawai ko ta halin ƙaƙa ne.

Yauma kamar kullum yana zaune da babanshi dake gyaran bakin fartanyanshi, sai labari yake bawa uban na inyayi kuɗi kaza inna yi kuɗi zanyi kaza, ya gyara zamanshi yaci gaba da cewa ” wato ina faɗa maka baba idan nayi kuɗi aradu zaku huta, zan gina gidan da duk faɗin garinnan babu irinsa,san….. murmushi irin na dattawa malam idrisu yayi yace ” sama’ila kenan kai kenan baka da magana kullum sai na kuɗi dai, nace ka rungumi noma don itace tushen arziƙi nan kuma ƙaƙi,to ni me zance maka yanxu.

Dariya sama’ila yayi yace ” haba baba noma kuma kuma da kuka yi shekaru a harkar banga me kuka samu ba,”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button