AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Lokacinda ammi ta iso gida sosai hankalinta ya tashi gashi suna ta kiran layin fareeda dahafsa duka yaki shiga zuwa can ammi tace watakila basu da caji ne amma ai basu taba irin fitar nan ba, suheer da duk ta damu tace amma ammi dazu wayar sweetheart yana shiga fa dauka ne bata yi gashi yanzu kuma shigar ma bayayi, ammi tace karki damu duk inda suke yanzu nasan suna kan hanya, ammi tana gama rufe baki kenan suka shigo fuskar su kamar gonar auduga,.

Da gudu fareeda tazo ta rungume suheer, har ta manta cewa sun bata, tace albishir rabin jiki, dan ture ta suheer tayi tana hade rai tace “ina kuka shiga duk kun tayar mana hankali, ai ko a waya zaku kira ku fada mana,. fareeda tace kwantar da hankalin ki baga shi mun dawo ba, da gudu kuma ta wuce gun ammi cikin matukar farin ciki tace” albishir ammi,! ammi tace ” goro fari kal mamana amma daga ina kuke tukun? bana hana irin fitar nan ba? hafsa dai na gefe tana kallonsu, farin cikinta ya gaza boyuwa, fareeda tace ” kai ammi kitsaya kiji mana, daga gidan rasheed muke yanzu, a rikice suheer tace rasheed kuma?, ammi ma tace wane rasheed din?, me kuma ya kaiku can bayan duk abunda ya faru,? fareeda tace “shiya kirani dazu a waya kuma danaje yace ya zabe ni a matsayin wacce zata taka rawa a cikin fim nashi, da zuciya daya take maganan, yayinda murmushin saman fuskar ta ya kasa boyuwa, kara komawa wurin suheer dake tsaye baki agape tayi ta riko kafadunta tace”rabin jiki kita yani murna a karon farko zan fito a fim daya da rasheed, amma na masa alkawarin cewa zaki janye karar da kika shigar, ta hade hannayenta wuri daya alamar roko ta cigaba da cewa “plssss rabin jiki, for the sake of me, for my dream, for my life, kiyi hakuri ki janye case dinnan na roke ki,.

Kallonta kawai suheer da ammi sukeyi, kafun suheer ta samu karsashin cewa wani abu, ammi tace, ” innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, wato yana son yayi creating rift a tsakaninku ne shine ya biyo ta nan, dafe goshi fareeda tayi tace ” try to understand mana ammi ba wani rift da yakeson hadawa a tsakanin mu kawai fa taimakona yayi, ni kuma na masa alkawarin rabin jiki zata janye case din,. ammi tace ” meyasa ne ke kullum kwakwalwarki bata aiki mai kyau ne?, yanzu ba abunda kika fahimta anan.? fareeda tace hooo ammi, kana ta juya gun suheer tace ,” zaki janye case din ki yau ma ko a’a?, Suheer ta mata kallon cikin ido tace bazan janye ba domin bazan bari ina gani wani yayi fooling naki ba., fareeda tace ban taba tsammanin baki kaunata ba sai yau, suheer tace” ko kinki ko kinso rashin janye karar shine kaunar da zan nuna miki., amma sweetheart me wannan munafikin ya miki wanda ya janye ra’ayinki haka cikin mintina kadan? fareeda ta nuna ta da yatsa tace” karki kara cemasa munafiki domin a yanzu yafi min ke sau dubu.

Da gudu fareeda ta wuce daki tana zabga kuka, rabawa anty hafsa tayi ta gefen ammi itama ta wuce dakinta ba tare da tace musu ko uffan ba,.zaman yan bori suheer tayi a wurin, a ranta tana cewa wato tanan ka bullo kenan.?

Kasancewar LIVE yan jarida suka dauki hiran da suka yi da asabe a asibiti da kuma halin da habeeb yake ciki, a take wannan labari ya karade birnin kano duk gidan tvn da ka bude labarin zaka ci karo dashi, yayinda kafofin sada zumunta suka dauka suma duk wani babban shafi a intanet ya wallafa labarin, nan wasu daga cikin yan jaridar suka sake videon da suka dauka a gidan rasheed dazu lokacin da suheer tazo har ta kalubalance shi.

Cikin kasa da awa daya labarin ya kai duk inda ake bukatar yakai, gaba daya soshiyal midiya ya rikice, duk inda ka leka, sai #justiceforhabeeb# kake gani, mitin din gaggawa komishinan yan sanda ya hada da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, inda daga karshe suka tsaya akan a kami rasheed a hukuntashi dan kar hakan ya zamo barazana ga tsaron kasar, domin in matasa suka fusata na nemarwa habeeb justice, shima bangaren rasheed yana da fanss kuma dukkansu matasa ne dole suma su fito, hakan yasa suka tsaya akan ayi tackling na abun tunda wuri, yan sanda aka tura su kwamuso oga rasheed daga gidanshi domin ya fuskanci shari’a.

Sosai ummie ta firgita lokacin da yan sanda suka zo tafiya da rasheed, ba karamin tashin hankali ta shiga ba wanda rabon da ta shiga irinshi tun mutuwar mijinta kuma uban rasheed wanda har yau bawanda yasan musabbabin mutuwar sai rasheed kadai, alhaji umar dake zaune gefenta ba abunda yake yi sai murna a cikin ranshi, a zahiri kuma yace ” Kibar damun kanki minti nawa ne zaiyi ya dawo , ke kinsan tsarin kasar nan inkana dashi babu mai taba ka. rumtse idanu da karfi rasheed yayi hadi da cijar lips nashi na kasa tamkar zai hudashi, lokacin da wani kyamurmurin dan sanda yake saka masa ankwa a hannu, tasa shi gaba sukayi suna saukowa daga saman benen bangarenshi, da sauri ummie dake ta safa da marwa a palon ta juyo jin saukowar su, cikin sassarfa ta kariso wurin tana share kwallan da suke ta ambaliya a fuskarta, tace “son,me ka aikata da zasu tafi min dakai ?wana ke dashi a duniyar nan banda kai, meyasa kayi abunda za’a rabani dakai?, kallonka kawai ya isheni koda ace zamuyi shekara dari bakamun magana ba, idanun rasheed ne ya kada yayi jajir, yayin jijiyoyin kanshi suka tashi sukayi rado rado, alhaji umar ne ya taso cikin salon munafirci yace “haba hajiya kibar su mana su gadanar da aikinsu , karki manta a bakin aiki suke in anjuma sai mubisu can caji ofis din, wani kallo yama rasheed kana yace “yakamata ka sanar da mu inda takardun kamfanin sarrafa gwala gwalai din dan uwana suke, ko uffan rasheed bai ceba sai jan da fuskar shi yake kara yi alamar da free yake Allah kadai yasan me zai faru. lokacin da aka fito da rasheed ba karamin cika farfajiyar gidan yayi da masoyan shi ba, sai daga masa hannu sukeyi yayinda yan jarida keta aikin su,kokarin saisaita kanshi yayi duk da irin tafarfasar da zuciyar shi take yi,dan murmushin yake yayi kana ya daga masu hannunshi duka biyu dake dauke da ankwa,.

Wata bakar mota kirar G WAGON na miliyoyin naira buba yasa a ka kawo har bakin kofa da niyyan rasheex ya shiga amma polisawan sunki, dole mutar su ta shiga ba biya fita da Allah ya isa suka cusa shi. Police station aka wuce dashi, sosai buba ya bi kafan manya da basu makudan kudi da niyyan cin hanci amma abun ya faskara, kwana biyu rasheed yayi a cell kafun aka wuce dashi kotu, inda wannan kwana biyu yayi su cikin tarin bakin ciki da takaici da kuma burin daukan fansa,.

A kotu an tuhumeshi da laifin tukin ba bisa ka’ida ba, da kade mutum da gangan, da kuma gudu bayan ya buge mutum sannan da yada labaran karya ta hanyar gaiyyatar yan jarida, don haka alkali ya yanke masa zaman gidan yari na tsawon kwana 14 da kuma taran naira dubu dari biyar da daukan nauyin majinyacin har zuwa warkewarsa, numfashin rasheed ne ya kusa daukewa lokacin da aka sanar da hukuncin sa. Lauyoyinshi sunyi iya kokarinsu amma basu samu nasara ba, yanke jiki ummie tayi ta fadi a sume lokacinda aka wuce da rasheed da niyyan tafiya dashi gidan gyaran hali, da karfi ya rumtse ido ya kuma budewa ya hango ummie kwance wanwar a kasa ga mutane sun rufu a kanta,.

Sati biyu cur rasheed ya kwashe a gidan gyaran hali kafun aka sako shi, gaba daya ya rame yayi baki ya fita a haiyacinshi kamar ba wannan tauraro dan gayen da yan mata ke rubibi ba, wannan sati biyu yayi sune cikin rashin kwanciyar hankali da samawa kwakwalwa nutsuwa tsabar tunanin cikar buri na daukan fansa, yana shigowa gidan baibi takan ummie da kusan tare sukayi zaman gidan kason da ita ba domin tsabar yadda ta fita a hayyacinta itama,.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button