AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Suheer dai sai aikin kuka take yi, fareeda ta dube ta cikin matsanancin kuka tace “sai yanzu nema na fahimci tun asali dama kishi kike yi dani, kishin zamanto wata jaruma kike yi, inba haka ba meye cikin janye kara kawai, ta kuma pashewa da kukan daya fi na farko tace ashe kishiiii kikee yiii daniii niban saniba, to sai ki hada pati yanzu kuyi celebrating keda saurayinnaki kuyi murna nace, ta fada cikin tsawa, sai kuma ta sassauta murya tace kuyi murna kinsa ankama Rasheed, kuyi murna kinsa rasheed idan ya fito yar uwarki bazata taba shiga fim ba.

Sai kuma ta fada jikin lamido tana kuka, yana shafa bayanta yace ” me kike fada ne haka fareeda Rasheed fa jarumine kawai kamar kowa bai isa ya hanaki shiga fim ba ki kwantar da hankalinki.

Abun duniya ya hadewa suheer goma da ashirin, ga wanda ta dawo dashi ha kuma wanda ta tawar. Banda sheshshekar kuka ba abunda take yi jikinta na rawa.

Sake lamido fareeda tayi tana kallon suheer hakan kuma yayi daidai da shigowar ammi, tace i have already make my mind, don haka ku zaba ko ni ko ita, ta fada tana nuna suheer da yatsa, wani irin juyawa kan suheer yayi yayinda ta fara ganin mutanen dakin bibbiyu, abu na karshe da taji shine saukar mari mai tsananin karfi a fuskar fareeda, ko ba’a fada ba tasan lamido ne yayi marin saboda karfin marin. A take takai kasa ta fadi sumammiya.

Sati biyu cur ta kwashe a asibitin sai yau aka sallamosu, wanda yayi daidai da fitowar rasheed daga gidan yari. A cikin sati biyunnan ba irin kiran da habeeb bai wa suheer ba amma bata dauka shi a tunaninshi fushi take hakan yasa gaba daya ya fita a hayyacinsa, gashi karayarshi bai warke ba balle ya iya tashi.

     A BANGAREN RASHEED.

Koda yagama zana hoton suheer yayi alkawarin da yayi, zama yayi yana kare mata kallo yana murmushi da shikadai yasan ma’anarshi, buba ne ya shigo da abinci,ya tsugunna gefenshi yace boss kachi abinci plsss, sai kuma ya kalli abunda ya zana a hankali yace “boss suheer again? yakamata a fita harkar yarinyar nan haka, kamo bakinshi rasheed yayi da karfi yace ” na kade mutum anshigar da kara ka kasa yin komai akai, yarinyar ta kalubalance ni gaban dubban mutane, ka kasa yin komai akai, anje an kulle ni a cell tsawon kwana biyu ka kasa yin belina, ankaini kurkuku tsawon sati biyu ka kasa yin komai akai, duk nayi hakuri naci gaba da zama da kai, amma akan wannan komai zai iya faruwa, bana son inkara jin ka ambaci sunan yarinyar nan, nika dai nake da ikon daukan mataki yanzu, hope i am clear? buba ya gyada kai, don ba bakin magana sake shi rasheed yayi yace “je ka shirya yanzu zamu fita,”

Sauri sauri rasheed yaci abinci don tabbas yana bukatan energy, kana ya shiga yayi wanka na huce takaici, saida ya kusa karar da gorar shower gel nashi daga sama har kasa ya dirje, sanda yaji kamar fatarshi kamar zai fashe sannan ya dauraye jikinshi ya fito bayan ya goge jikinshi yayi yan shafe shafenshi ya shiga closet nashi, wasu kaya ya fitar kamar dai kullum kananan kaya ne bakin wando, da farar riga an mata wani layi guda uku ta gefen dama, da jan zare boxer da singlet farare kal ya saka kafun yasaka wandon hade da daureta da bakin belt kana ya sanya rigar, wanda ta fito mishi da murdadden kwanjinsa,take ya fito ainahin rasheed nashi yana ta walkiya, hular tashi ta gado ya dauko wato p-cap farine mai touches na ja a jiki da kuma tambarin star a gaban, kana ya fesa turarukanshi, masu dadin kamshi da sanyi, kasancewar yafi amfani da turaren samfurin oud, hakan yasa yake dasu birjik kawai duk wanda ya dauka kuma fesawa yake yi sai ya bada wani kamshi na musamman. Wasu jajayen takalma sau ciki yasa, kana ya daura agogo da zobe da kuma bracelet na gold irinna maza. Woww ko namiji yaga rasheed dole ne ya burgeshi tsabar irin kyawun dayayi, makullin mota ya zara ya fito yana taku as superstar he is, bai yadda yabi ta inda ummie zata ganshi ba.

Zaune ya tadda buba a parkin space yana jiranshi, ya goge wata arniyar farar mota kirar Royce Rossey, ba tare da dogon magana ba rasheed ya shige driver seat, buba cikin sauri yace boss da ka kawo nagi driving din ai,” bai kula shi ba hakan yasa ya shiga gefen mai zaman banza ya zauna, key yai wa motar yaja ta da mugun speed suka haura kan shimfidaddiyar kwaltar dake gidan, tun baiyi horn ba mai gadi ya tashi ya wangale kofar suka fice a guje.

Gudu kawai rasheed yakeyi, yayinda buba ke ta addua’ar Allah ya kaisu lafiya, ganin sun shigo titin sabon gari hakan ya girgiza buba yace Suheer kuma, shi ya dauka a ranshi yayi maganar, saida yaji karar burkin da rasheed yayi ne ya ankara, rasheed yace, fita ka duba mana taya,.

Ba musu ya sauka ya zaga kennan ya figi motar shi yayi gaba, buba yace ya salam boss kar kaje ka aikata wani abu fa, taxi ya tare yabi bayanshi duk kuwa da ya mishi nisa, a dab inda yataba buge habeeb ya tsaya ya tambayi wani yaro inane gidansu Suheer lamido, kasancewar gidan ba nisa da hannu yaron ya nuna mishi, dubu sabuwa dal ya mikawa yaron, kana ya wuce, bai damu da yadda mutane ke kallon motar shi ba dan yasan ba kowa ya mallaki irinta ba, sai wane da wane.

Kashe motar yayi ya fito yana yamutse fuska kamar yaga kashi ya nufi cikin gidan…..

Not edited….

????????????Auren Fansa????????????

Book Two

  By.

Ummu Fadeela.

Typing????

Page, 33 / 34

………..Suheer na kwance akan doguwar kujera a palo, idanunta a lumshe,kamar mai bacci amma ba baccin take ba, tunanin habeeb ne fal ranta, tambayar kanta take ko ina yake yanzu? ko jikinshi yayi sauki,? fuskar ta tayi fayau tamkar wacce ta shekara a gadon asibiti, sai wani hasken da ta kara, daka ganta zaka san ba karamin shan jiki tayi a rashin lafiyar da tayi ba,.

A daya gefen kuwa fareeda ne zaune a kan carpet,ta shimfida wani dan kyalle a gabanta hannunta rike da nail cutter tana gyara farcenta, itama gaba daya ta fice a hayyacinta tamkar tare suka yi jinyar, koda shike ita tata jinyar ba iya gangar jiki bane,harda zuciya.

Yayinda ammi ke zaune akan kujera mai zaman mutum daya tana yanka wasu fresh fruits a cikin bowl, tun safe suheer ta kasa cin komai hakan yasa take yanka mata fruits din maybe bakinta yayi dadi.

Mikewa ammi tayi bayan ta gama yankawa ta dauko fork guda biyu tazo ta ajiye bowl din a kusa da fareeda, kana ta dube ta tace, “kuyi kokari ku shanye wannan, dan kema ina lure dake tun safe ba wani abun kirki da kika ci,” kana ta juyo kan suheer tace “taso kema kafun in dawo ku tabbatar kun cinye wnn,” kwabe fuska tayi tace “ammi i don’t have appetite faa,” cikin fada ammi tace “wannan din shizai samar maki appetite din ai, sannan ki zauna har in fito in sameki a wurin”, ta juya ta tafi tana ta fadan ai ku ba yara bane daza ku hanamin nutsuwa.

A hankali suheer ta mike tana jin jiri yana kwasarta kamar zata fadi kasa, hannun kujerar ta kama tsawon minti daya kafun ta mike ta zari wayar ta ta matso inda fareeda take ta zauna,. Suheer kanyi mamaki idan ta tuna wai sweetheart bata mata magana, idan tayi dogon tunani saita rasa gane me laifinta a cikin wannan al’amarin. Tun kwanciyarta a asibiti sau daya ta tambayeta ya jikinta,.

Hannu ta sa ta dauki fork din ta dauko yankakken watermelon daya tasa a baki, a hankali take taunawa tana jin zakin ruwan kankanar yana sauka cikin makogoronta, kirrrr wayar ta dake kusa da ita yayi kara, bin wayar tayi da kallo ganin sunan habeebi na yawo bisa screen din wayar, dagawa tayi ta kara a kunnenta, cikin sanyin murya tace “Assalamu alaikum”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button