AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Komawa cikin gidan tayi ta shigo ta samesu tsaye yadda ta barsu, a hankali ta kariso kusa da suheer tana rike da file din tace” I know that I am wrong and you are right, suheer da zuciyar ta ya tsinke na tunanin me kuma zata fada mata, ta dago da sauri jin abunda ta fada, fareeda taci gaba da cewa ” nasan cewa na miki ba daidai ba ala kulli halin, amma ba abunda kika yi akai, i know i criticized you a lot. And also abused you, amma ba abunda kika yi akai, ni yayarki ce bazaki iya marina ba, kozaki iya?, ada nace kin kwace min mafarkina kinmin katanga da cikar burina, ashe ba haka bane hanya kika min na cikar burina, gashinan yanzu a hannuna,, ta fada tana nuna file din hannunta,. nasan ko ke rabin jiki ba abunda kike kallo yanzu a hannuna sai cikar burina na shekaru masu yawa.

Kuka ne ya kwace wa suheer yayinda ammi ke gefe tana kallon yayannta masu abun mamaki, fareeda taci gaba da cewa abu daya zakiyi yanzu ki rage fushin da kike yi dani, ba komai bane kuma face ki dena wannan hawayen da suke zuba a dalilina, sai kuma ta ware hannayenta ta mata alama da kai ceqa tazo, da gudu suheer tazo ta fada jikinta suka sake dariya mai hade da kuka a tare,… fareeda tana fadin ki yafemin rabin jiki..!

Gudu Rasheed yake yi akan titi kamar kullum, a zahiri yace “TUBA, YAFIYA what a crap,. I like it, in fact I like her, ina nufin Aysha Suheer i really like the GAME…….

NOT EDITED.

Muna samun tsaiko ne 2dyz dinnan domin ina da baki a gidan kuma suna da dan yawa, so muyi hakuri duk yadda muka samu abubuwa suna min yawa har bana iya samun lokacin typing da kuma editing, amma insun tafi zamu dawo normal post namu, ILVYSM GUYS.

????????????Auren Fansa????????????

Book Two

Na

Asma’u mai anguwa.

Ummu Fadeela.

Typing????

Page 35 / 36

….. Da daddare Suheer na kwance bisa gadonsu, har misalin sha biyu da rabi na dare ta kasa bacci, juyawa tayi ta kalli fareeda dake baccinta peacefully tana makale da script da rasheed ya bata tayi karatun script dinnan yafi sau dari, tana cikin karatunne ma bacci yayi awon gaba da ita, dan murmushi suheer tayi ganin yanda ta kankame takardar kamar mai tsoron kar wani ya kwace mata, a hankali ta janye takardar daga kirjinta kana ta mishi mazauni gefen gadonnasu.

Zuro kafafunta tayi kasa kana ta mike ta fita zuwa palo cikin sanda, har ga Allah ta kasa bacci kuma bata san me ya hanata baccin ba, saidai tafi alakanta hakan da zuwan da rasheed yayi gidan dazu, zama tayi palon tsawon minti biyar amma bataji ta ta dawo daidai ba, hakan yasa ta kuma mikewa ta nufi fridge nasu, gorar ruwa ta dauka a ciki ta bude ta kafa a baki ba tare da tabi takan cup dake jere saman fridge din ba. Sosai tasha ruwan kana ta maida sauran ta ajiye ta fara sauke ajiyan zuciya, dakin ammi ta nufa ta bude ta leka kanta kadan,.

Zaune ta hango ammi a tsakiyar gadonta tayi tagumi, karasa shiga dakin tayi ta zauna a bakin gadon tace “ammi, ammi, sai ana uku ammi da batasan ta shigo ba ta daga kanta ta ganta, cikin damuwa ammi tace “me ya kawo ki nan yanzu? bakiyi bacci ba? me ya hanaki bacci? a jere ammi ta mata tambayoyin fuskarta dauke da mamaki.

Suheer tace banyi bacci ba ammi, shiya sa nazo inganki,” ammi tace, me ya hanaki baccin?, da kyar ta tattara kalmomin cikin sanyi tace” abunda ya hanaki bacci ammina, nima shi ya hanani baccin, studying na yar tata ammai tayi tsawon minti biyu, kanta a kasa taci gaba da cewa nasan zuwan rasheed gidannan dazu ne ya hanaki bacci ammi, nima haka ne. Na kasa yadda cewa rasheed ne zai bada kai a takennan a dan sanin da na mishi nasan wannan ba rasheed din dana sani bane, nafi tunanin wani ne yasa fuskar sa, ko kuma in shidinne to wani wasan kawai yake son yayi playing, shiyasa yazo nan ya sauke mana kai, sannan yayi amfani da ambition na sweetheart domin ya cimma munafikin burinshi.

Matsowa ammi tayi ta kamo ta, ta kwantar da kanta akan cinyar ta yazama suna fuskantar juna, tana shafa dogon sumar ta mai laushin gaske tace “mamana,there is different kind of people in dis dunya, sau tari wasu mutane suna aikata kuskure ba tareda sunsan cewa kuskure suke aikatawa ba, har sai wata rana Allah ya kawo mai nuna musu gaskiyar abunda suke yi, kamar dai ke da rasheed, ba wanda yake iya tunkararshi ya fada masa laifinsa, kowa yabonshi yake, inma saboda dukiyar sa, ko kuma saboda daukakar da Allah yabashi, kwatsam kika fito rana daya kika nuna masa gaskiya kika nuna masa laifinsa, and now he realized his mistakes shiyasa yazo ya bada hakuri, don haka karki sa damuwa a ranki kinji dauta na.

Gyada kai suheer tayi tace ina fatan Allah yasa hakanne, amma ammi tunda kinsan haka why are you so upset?.

Kauda kai ammi tayi tace “ina damuwa ne sabo ke” wara dara daran idanunta akan ammi tayi,cikin mamaki tace “saboda ni kuma ammi? to me nayi nidin?” ammi tayi kokarin boye damuwar ta ganin suheer ta tsorata tace “dazu baban yaronnan habeebu yakira kawunku a waya akan yana son abasu dama suzo su nemi aurenki, shine ya tabbatar musu da zai ji daga bakinki idan kin amince sai ya fara bincike akan yaron dan shi bazai yiwa yayanshi auren dole ba, yanzu dai ya basu kwana goma.

Amma ba wannan ne ya dame ni ba, abunda yafi daga min hankali shine maganan da lamido ya fada min, i know nothing ya fada min but the truth, zallar gaskiya ya fada min amma bansan meyasa ba hankali na ya tashi sosai, suheer da bata ce komai ba tunda ammi ta fara magana kanta na kasa tace “kamar ya ammi ? me kawun ya fada miki, dan murmushin karfin hali ammi tayi, tace “cewa yayi ya zama dole inkaiku gida, wai lokaci yayi da zanje gida, ya kamata inkaiku kuga mahaifinku da danginku, domin babanku ke da ikon bada aurenku ba shiba, wai inkaiku gida kodan saboda halin rayuwa, bamusan me gobe zata haifar ba, suheer baisan dalilin da ya sa na bar gida ba all those years, muna rayuwar mu happily anan ba tare da yan uwa ba, meyasa yake son bata mana farin cikin mu? baisan waye mahaifinku bane, da yasani bazai taba yadda inkoma wancan gari daku ba, he’s wicked person, baisan komai ba sai zalunci da son kansa, ta fada tana mai fashewa da kuka,.

Kukan suheer ma ta kamayi sosai kamar an aiko mata sakon mutuwa, ganin haka yasa ammi share mata hawaye itama tana share nata duk da cewa sunki tsayawa, suheer tace “ammi kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki, shekara dai dai har ishirin ba kwana ishirin bane, i believe cewa duk abunda ya fitar dake a wancan lokacin a yanzu ya zama tarihi, tabbas ya zama tarihi, kiyi hakuri ki dena kuka Allah yana tare damu kinji ammi na?, fareeda dake tsaye bakin kofar ta shigo, tun fitar suheer bai juma ba cikin bacci ta laluba taji bata nan hakan yasa ta farka, ta dade a zaune a wurin kafun ta fito ganin suheer bata shigo ba muryoyinsu taji a dakin ammi a hankali hakan yasa ta nufi can, takowa tayi har tsakiyar dakin, ammi ta bude mata hannu zuwa tayi itama ta fada jikinta sukayi kukan su mai isarsu, anan suka karasa kwanansu na ranar.

Washe gari bayan sun kammala breakfast, lamido ya kalle su daya bayan daya, (a zahiri su din ba jininshi bane amma kuma sun zamo wani bangare na rayuwar shi, wanda a yanzu yake jin bazai iya rayuwa ba matsawar basa tare dashi, shidin bangon jingina ne a garesu, yayinda suko suka zamo masa ruwa maganin kishi wanda sune suka kore mishi kishirwar danginshi shida tilon kanwarshi.) ya kalle su yace ” ku zama cikin shiri anytime cikin kwana biyu masu zuwa zamuyi tafiya mai cike da tarihi”, ya kalli ammi yace ” adama hope dai zaki gane kauyenku idan mun iso?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button