AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mama macece mai dan banzan masifa da tsananin kishi ga jarababben son kudi na masifa wannan yasa tun addatu na karama ba wani lungu da sako na cikin kano da bata sani ba saboda talla,sadi kuwa da babansu yake aikin wanki da guga,umaru shine wanda ya fi kwafo halayyar uwarsu tsab na jarabar son kudin tsiya, saidai shi jikinshi bai tabuwa baison aikin wahala ko kadan yafi son abunda zaiyi kudi masu kauri su shigo hannunshi, haka nan suke kara zube ba arabi ba boko.

Yayinda larai umma ta kasance mace mai hakuri da kawaici da gudun duniya, ba laifi tana da ilimi na addini da na boko dan tayi primary har zuwa aji bakwai irin tsarin karatun farkon boko, addini ma ta sauke kur’ani ta kuma karanta takardu masu yawa,hakan yasa suke zaune lafiya dan ko mama ta takale ta bata kulata, danta Matawalle kuwa ta dage sosai wajen ganin ya samu ilimi both bangare biyun,duk wani kokari tana yi wajen ganin ta inganta rayuwar shi tare da taimakon danginta don ba laifi suna da hali kaddarar aure ne ya jefota gidan mala audu.

Haka mama zata zauna tayi ta yada habaici duk sanda matawalle ya fita da sunan tafiya makaranta, amma ko ci kanki umma bata ce mata,wannan yake kuma hasala ta,shikuwa babansu ba ruwanshi tunda ba sisinsa a ciki yakan ce kowa yayi abunda zai fishsheshi.
Kwanci tashi asarar mai rai.Yanzu su matawalle sun kare babban sakandire,zuwa lokacin abubuwa da dama sun faru, kamar mutuwar babansu, kana anyiwa addatu aure har ma ta hayayyafa,yayansu sadi kuwa ya rike wurin wankinsu inda ya fara zamanantar dashi kuma ba laifi yana samun customers da haka yayi aure bayan ya gina daki daya a cijin gidansu, autansu umaru kuwa ya samu uban gida a kantin kwari inda suke sana’ar yadi.

Tsayuwar daka mama mairo tayi akan sai an raba musu gado tun randa akayi arba’in din mala audu, haka kuwa akayi bayan rabon gado umma da danta matawalle suka tashi da wani karamin bangare na cikin gidan,inda mama ta hau hura hanci ita ce da gida yanzu tunda yayanta ne suka fi samun gado, kamar kullum umma bata tanka mata ba tun tana yi har ta gaji tayi shiru.

Wata rana matawalle ya dawo da farin ciki yake sanar da ummarshi gwamnatin tarayya ta dauki nauyin karatunshi zuwa kasar waje saboda kwazon da ya nuna, cikin duk wadanda suka gama a shekarar ba wanda ya kaishi samun maki mai yawa,wannan yasa gwamnati ta dau nauyin su shida wasu masu kokarin a sauran states.

Ba karamin murna umma da yan uwanta sukayi ba da wannan ci gaba da aka samu cikin zuriyar su.

Koda umma ta sanar da mama kyabe baki tayi tace. “A yi dai mu gani,inba lalace wa ba mai zai kai yaro wani uwa duniya can? salon yaje ya koyo mana salon yahudawan yamma, to ina sanar muku matukar ya zi mana da wani bidi’a gidannan tsab zaku kwashe naku ya naku ku bar mana gida ehe, wancan dan akurkin naku kuwa ko umaru na zai iya siyan shi ya baku kudinku”. Ta fada tana juya kai. But deep down she’s boiling. Zuciyar ta na tafasa dan kishiyarta zai tafi kasar masu jan kunne ga nata yaran suna gararanba ba abun kirki, addatu kuwa tana can tana kwasar bakin cikin namiji da danginsa a gidan aurenta, yanzu kenan Ahmadu jirgi zai hau ya lula wata duniyar da suke jin labari a rediyo, tuna hakan yasa ta wani irin zabura.

Shiri matawalle ya hau yi ba kama hannun yaro, yayinda umma ta kara kaimi wajen yi masa addu’a. Bayan wani lokaci suka daga zuwa birnin london inda canne suka samu scholarship din a oxford university, matawalle ya dage yayi karatu irin na ba marar da kunya inda ya karanci GEOLOGY wato ilimin albarkatun kasa, cikin nasara ya kare karatun wannan karon ma ya fito da sakamakon da ya kere wa saura hakan yasa ya kuma samun wani tallafi na yin masters degree nanma a bangaren dai na geology, cike da nasara ya kammala ya dawo gida.

Zuwa lokacin ya zama babban mutum mai cike da kamala,yanda gidan nasu yake haka ya dawo ya taddashi sai ma ci bayan da aka kima samu,matar sadi ta hayayyafa,gidan ya cika da yaya ko ina kazanta, yayinda umaru kuwa mai gidanshi ya koreshi sakamakon sata da ya mishi.

Saura kadan zuciyar mama mairo ya shige cikinta lokacin da tayi arba da matawalle sa’ilin da ya dawo.

Ganin irin sakamakon da ya dawo dashi da ba wanda ya taba samun irinshi yasa gwamnatin lokacin ta dauke shi aiki cikin lokaci kadan a ma’aikatar albarkatun kasa.

Wayyo ina wuta mama mairo ta jefa shi ciki.

Bayan wani lokaci a ka tura shi zuwa morocco karkashin ma’aikatarsu domin halartar taron karawa juna sani kan albarkatun dake cikin kasa, a can ya hadu da matar shi batool UMMIE Ya nuna yana sonta ita ma ta kyasa amma danginshi sunja a cewar su baza su ba bako dan wata kasa auren yar su ba.

Haka ya juyo zuwa nigeria rai ba dadi, zuwa lokacin kudi sun fara zama a aljihun matawalle wanda yanzu akafi kira da ainahin sunanshi wato Ahmad matawalle,hakan yasa ya fara canja wa ginin gidansu fasali zuwa ginin zamani. Ba tare da nuna san kai ba harda bangaren mama yasa a rushe inda aka fara tono domin maye gurbin ginin da sabon tsari.

Da bangarensu aka fara inda masu haka foundation suka tono wani abun mamaki, wata dutse suka sara mai dan karen kyau saidai duk kokarinsu sun kasa ciroshi, hakan yasa aka garzaya aka sanar da matawalle, kallo daya ya mishi ya gane cewa danyar gold ce,saboda wannan shine abunda ya karanta har degree na biyu.

Ba bata lokaci ya dakatar da aikin shikuwa ya hau bincike yadda za’a samu daman zakulo wannan abu mai dumbin arziki.

Bayan lokaci kadan aka zakulo danyar gwal a cikin kasar dake bangaren gadon Ahmad matawalle bisa taimakawar wata nau’ra wadda yayi tattaki har thailand ya nemo shi.Kima da darajar gwal din ya kai kimanin dalar amurka triliyan uku. wannan shine mafarin lamarin.

Lokacin da Mama mairo ta ji zunzurutun kudin da wannan dutsi zai bayar idan an saidashi nan ta rikice ta zama kamar zararriya, ta na ta sambatu,kana ta nuna saidai a raba da yayanta ai suma gidan su ne don haka suna da hakki a ciki.

A lokacin kam umma ta tanka ta.Inda ta nuna sam hakan ba mai yuwuwa bane, wannan hakkin danta ne, a cikin wurin shi na gado ya fitar dan haka ba mai tilasta mishi…..Duk wani hanya da mmma tasan zata bi tabishi amma babu nasara hakan yasa umaru wadda shike kara zugata daman ya kawo shawaran su sace gwal din kawai…..sau ba adadi suna attempting sace wa amma sun gagara har Allah yasa matawalle ya samu daman fitar da shi kasar waje domin sauran gwaje gwaje kasancewar mu anan bamu da isassun kayan gwaji.

Ba dau lokaci mai tsawo ba aka kammala ginin da aka fara a gaba daya gidan, nan umma ta matsa mishi kan batun aure domin zuwa lokacin ya girma sosai,matawalle ya sanar da umman shi yarinyar da ya ke so a morocco amma iyayenta sun hanashi aurenta, umma ta kwantar mishi da hankali da cewa idan rabonshi ce zai samu zata je ta sanar da wanta batun

Haka kuwa akayi yayyun umma biyu da wani abokin su daya suka tafi morocco bisa jagorancin matawalle,wannan karon iyayen batool basu hana suba…Basu dawo ba saida aka daura auren batool da matawalle kana ya juyo nigeria da dalleliyar balarabiyar matar shi.

Hannu mama ta sa akai ta rusa ihu lokacin da taga wannan tsaleliyar yarinya a matsayin matar matawalle,…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button