AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

         **************************.

Kokawa fareeda ta farayi da numfashinta tun bayan fitar su, ji take kamar ruhinta zai bar gangar jikinta, maman saudat ne ta shigo dakin da nufin daukar mayafinta tunda amarya ta wuce a rikice ta kwala kiran” Adama, Adama mun shiga uku, a dari da sittin ammi ta shigo dakin har rige rige shiga suke yi ita da saratu wacce ta dawo daga rakiyar suheer innalillahi wa’inna ilaihi raji’un suka ambata a tare, ido rufe ammi ta ciccibi fareeda wacce idonta suka kafe zuwa hanyar waje ko takalmi babu kafarta, rufa mata baya sukayi suma……cikin daren suka nufi asibiti a ka karbe su da gaggawa likitoci suka rufu a kanta suna kokarin janyo numfashinta…..Tsabar tashin hankali ammi kasa zama tayi sai sintiri take yi tana addu’ar Allah yabata ikon cin jarabawar da ta ke fuskanta a cikin yan kwana kin nan…..

Har karfe goma da rabi na dare ummie na zaune palon kasa tayi tunani har ta rasa irin tunanin da zata yi,…..Bude kofar palon a kayi wani dan saurayi da bazai haura ashirin da biyar ba ya shigo yana ta aikin danna waya, hango ummie zaune cikin daya daga kujerun palon ya sa shi cewa “barka da dare ummie,” kallonshi tayi tace “yauwa Adeel daga ina kake at this hours” ta fada tana kallon agogo, sosa kai yayi yace “amm dama ummie wani abokina ne yake, sai kuma yayi shiru tace “ya kamata kasan ka girma dai adeel, you have to be very carefull da abokan banzan da kake muamala da…. Ta mike tana kallon akwatunan suheer da buba ya ajiye a kasa tun ahigowan su dazu tace “biyoni bangaren yayan ka da wannan”, adeel yace “ummie baki muka yi ne, and what the use of guest room da za a ajiye su a bangaren ya rasheed? ” salon asa su cikin uku , wani kallo ta watsa mishi take yayi shiru.

Suna haurawa yana ta mata surutu amma ba jinshi ma take ba domin tayi nisa a tunanin da take har wani irin sarawa kanta yake yi, turuss sukayi dukkansu biyu ganin mutum zaune a kasa jikinta sai rawa yake yi, zuwa lokacin suheer ta gama fita haiyacinta dan ba karamin wahala take sha ba sakamakon sarkar da ya sa mata, kamar yadda ya kira sarkar da suna sarkar azaba to tabbas ya amsa sunanshi ko me ya saka a jiki Allah masani sai kuma shi da ya aikata abun, ……Da hanzari ummie ta karasa kusa da ita tana tambayar ta “anan ya barki ko? me ya same ki haka? ba dai dukanki yayi ba ko? duk tausayin ta ya cika ummie dan gani daya ta mata taji yar ta kwanta mata a rai.

Cikin shakewar murya suheer tace “ammi help, help ta fada tana nuna wuyanta da hannu, da hanzari ummie ta mikar da ita tsaye ta na taba wuyan amma bata ji komai ba hakan yasa ta yaye hijab din, zaro ido tayi ganin makoshin suheer yayi jajur yayi rudu rudu kamar harbin kunama, shaninka da farin fata sosai abun ya bayyana, da sauri ummie ta juyar da ita ta tana kokarin sunce sarkar amma ta kasa tace “me wannan ? garin yaya kika daura sarka yar karama haka gashi tana kokarin nutsewa cikin jikinki?, suheer dai ba bakin magana domin ita kadai tasan abunda ta keji a hakanma tana dannewa, matsowa adeel yayi yana kallon shiny skin dinta da duk ya kumbura, tace “subhanallah ummie ina ga mu yanke kawai inba haka ba nitsewa zaiyi cikin naman jikinta, but who is she ummie? cikin tsawa tace “stop questioning me and do the right thing adeel? da sauri ya fara laluben aljihunshi kana ya fitar da wani nail cuttern da ya gyara farcensa dazu ya daidaita saitin chain din ya danne da karfi, take kuwa ya tsinke ya fado kasa wani irin ajiyar zuciya ta sauke tana jin wani irin relieve yana shigar ta, kura mata ido adeel yayi without blinking, especially cikakkun kirjinta wanda sukayi dam dam gaban rigar atamfar ta kamar zasu pasa shi, cikin yin kasa da murya yace “plsss ummie who is she?”……..
????????AUREN~FANSA????????

   BY

ASMA’U MAI ANGUWA

  (Ummu  fadeela)

Typing????

Book two

Page 61 / 62.

…Ummie tace “Adeel! wuce kayi bacci,”badon yaso ba ya wuce kasa yana ta waiwayen suheer,a ranshi yace “kai wannan itace dream girl nawa ai Allah yasa yat uwar su ummie ne ta kawo mata ziyara, ai bazanyi kasa a guiwa ba gobe zan samu daddy da maganar aure”,

Sai kuma ya tsaya a bayyane yace “wait, amma meyasa aka kaita bangaren ya rasheed?” kamar tababbe ya kuma cewa “to kai ina ruwanka,? da haka ya bude dakinshi dake first floor ya shiga ya fada gado yana hasaso irin kyawun suheer musamman cikakkun kirjinta da yafi tafiya da hankalinshi.

Kamo hannunta ummie tayi tace cikin sanyin murya “da akwai ciwukan da basa taba warkewa, kamar dai ciwon dake raina, kana akwai wasu bakin cikin da basa gushewa duk yadda kaso su wuce dole wataran sai memory din ya dawo maka,…Ta dan ja numfashi tace” nasan dana ya hada miki dukka biyun wato da ciwon da kuma bakin cikin, saidai ina rokonki da ki yafe masa, watakila zaki iya ganina a matsayin maison kanta dayawa tunda na roki ki yafewa dana,…duk da bansan yadda lamarin aurenku ya kasance ba, amma na tabbata zaki ji dadin zama da rasheed dina dan yana da kyawawan halaye da kuma sauke hakkin duk wanda ya kusance shi, wadannan bad habit da ya ke yi situation ne ya sa, amma sam ba halinshi ba ne ba nasan wata rana zaki fada min kyawawan halayenshi da bakinki, amma for now kiyi hakuri da yanayin da kika ganshi i assure you zakiji dadin zama dashi, bazan tambaye ki yadda aurenku ya kasance ba amma ina da yakinin kece hasken da na dade ina mafarki cikin rayuwar rasheed,” sai kuma ta sake ta kana ta hada hannunta wuri daya alamar roko cikin raunin murya tace “plsss ki taimaka min kar mugun halin da rasheed ke gwadawa yasa ki gujeshi, da akwai ciwo mai tsanani cikin rayuwar shi, ya rasa gatan uwa da na uba a lokacinda yake tsananin bukatan”…..Sai hawaye shaaa hakan yasa ta kasa karasa maganar.

Dago kumburarrun idonta tayi tana kallon ummie dake share hawayen ta, ita dai matar nan ta daure ta da jijigoyinta ta kasa fahimtar inda maganganunta ya dosa, da farko tace rasheed ba mugu bane yana da kyawawan halaye amma a zahiri ita bata ga wani abu makamancin kyan hali tattare da shiba sai kuma….Katse mata tunani ummie tayi ta hanyan janyo hannunta zuwa cikin palon, binta kawai suheer keyi amma ba don taso ba sai don girmama matar da a haife ma ta girmi amminta nesa ba kusa ba.

Palon tsit ko ina tsab sai tashin kamshi yake yi dan rasheed ba baya ba wurin son kamshi yana iya kashe ko nawa ne wurin sayen abu mai kamshi hakan yasa hadadden palon ke ta tashin kamshi ta ko ina,…… tunda ya shigo yayi abunda ya saba kafin ya kwanta ya shirya cikin wasu black pyjamas kana ya peshe jikinsa da turare lungu da sako kana ya hau gado ya kwanta, saidai wani irin zogi goshinsa ke masa ga wani irin kumburi da yayi cikin lokaci kadan, hakan yasa ya tashi ya taro ruwan zafi a dan karamin baf ya fito ya zauna a bakin mirror ya ringa tsoma karamin towel cikin ruwan yana matse goshin har ya ji ya dan sassauta mishi sannan ya shafa man zafi a wurin ya koma kan gado ya shige cikin duvet yana kashe haske hadi da lumshe ido, saidai duk yadda yaso yayi bacci hakan gagararsa yayi.

Kamar almara yaji ana knocking masa kofar bedroom, da mamaki yake kallon kofar waye zai shigo masa bangarensa yanzun nan, jin ana ci gaba da bugun ne ya taso cikin nutsuwa yace “whose there?” .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button