FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

Hawa yayi kan gadon ya soma janye mata gyale

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. me.. me.. kake yi haka? Don Allah kayi haƙuri”. Tafaɗa da rawan baki tana son ƙwatan kanta

Falla mata wani marin yayi da yasa dole ta nutsu waje ɗaya, ta saki wani marayan kuka tamkar ranta zai fice

Be dakata ba sai da ya cire mata gaba ɗaya kayan ta, tuni idanun sa sun juye, sai ƙara hautsina yake yi da tsantsan tsanar ta

Ita kuwa numfashi kawai take sauke wa, tana addu’a a zuciyar ta sabida abun da ke shirin faruwa da ita, domin ko kaɗan baza ta iya jure wa ba, ita da take amsar wa ƴaƴa mata haƙƙin su idan aka yi musu fyaɗe, shi ne yau ita za’a yi wa

“Ya Allah ka taimake Ni”. Tafaɗa a ƙasar ranta hawaye na ci gaba da kwaranya a fuskar ta tamkar an kunna famfo.

       Tofar da yawu yayi ya mirgina ya tashi, zuciyar sa tamkar ta ƙone sabida baƙin cikin abinda yake shirin aikata wa, bayan yasan ita wace ce, taya ma yayi wannan tunanin gangancin da yake son haɗa jiki da ita?

Tsaki yaja yana kallon ta da jajayen idanun sa, ganin yanda take rufe jiki, sai ya saka hannu ya janyo blanket ɗin yana cewa, “ƴar iska! Uban wa kike son ɓoye wa jikin naki? Bayan da kin gama tallata sa a waje meye kuma yayi saura? Babu abinda zai burge Ni a nan bare inyi sha’awar ki, gwara ma tun wuri ki sauya tunani. Na tsane ki! kuma wlh sai kin yi dana sanin aure na, sai na azabtar dake yanda ko an ce su sake bani auren ki sai sun yi kuka”.

Kuka sosai Ɗahira take yi, tana riƙe da blanket ɗin da ya riƙo ƙam, ta hana sa janye wa

Tsaki ya kuma ja ya fice a ɗakin, har ya shige ɗakin sa, sai kuma ya dawo cikin nata ɗakin

Wani irin zabura tayi cike da tsoro tana kallon sa

Shi kuwa ko bi ta kanta be yi ba, ya sanya hannu ya cire keey ɗin ɗakin, sannan ya janyo ƙofan ya rufe ta ta waje

Wani marayan kuka ta saki har da shashsheƙa, sosai ta takure kanta tana ta kuka, tafi awa a haka bata dena kukan ba, sai da taji gaba ɗaya jikin ta ya ɗau zugin zafi kafin ta haƙura. Lallaɓa wa tayi ta sauko daga kan gadon, har ta ɗauki rigan ta zata mayar, sai kuma ta ajiye ta shiga Toilet, ruwa me zafi ta haɗa ta gasa jikin ta, daƙyar take iya yin komi, tana yi hawaye na kwaranya a fuskar ta, sai da ta gama ta ɗauro alwala ta fito, wani doguwar rigan ta saka mara nauyi me ruwan ƙasa, ta saka Hijab ta tayar da Sallan magriba da ya wuce ta, sai ta haɗa dana isha’i

Har ta idar da sallan kuka take yi, ko kaɗan ta kasa yin shiru. Ta daɗe tana roƙon Allah kafin ta sallame sallan, ta kifa kanta a gwiwowin ta taci gaba da rera sabon kukan ta

Maganar Fadila da tayi mata tun ana gobe bikin su, shi ne ya dawo mata a rai. “Ta sani cewa dole ne sai tayi haƙuri da rayuwan auren ta, amma bata taɓa tunanin wulaƙancin da zai mata zai kai haka ba, yanzu har da yunƙurin mata fyaɗe a matsayin ta na matar sa ta sunna kuma ƙanwar sa. Sannan yake jifan ta da munanan kalamai, wai wani irin tsana ne yake mata? Me ta tare masa ne? Me tayi masa?”

Sai ta ɗago kai tana share hawayen fuskar ta da ya gama kumbura yayi suntum, kasancewar ta fara gaba ɗaya tayi jazur sawayen yatsun sa sun fito, cikin rawan murya a fili take cewa, “ga shi tun ba’a yi nisa ba na tuna maganar ki Fadila, amma ba na tunanin wannan auren zan jure azabar shi har na ba wa maƙiya na kunya, wlh bazan iya ba sam”. Ta ƙare maganar ta da fashe wa da sabon kuka

Buɗe ƙofan da taji ana ƙoƙarin yi ne, yasa tayi tsit tana bin ƙofan da kallo hawaye na kwaranya a saman fuskar ta, wanda tayi zaton shi ne ya shigo

Shima a kanta ya sauke idanun sa, sosai yaji wani sanyi a ransa duba da yanda ya ganta, ci je leɓe yayi a ransa yace, “kaɗan ma kika gani, sai na wahalar da rayuwan ki, sai na wulaƙanta ki”.

Takowa yayi ya isa gaban dressing mirror inda ya ƙilla idanu ya ga wayan ta. ɗauka yayi kawai ya fice a ɗakin, ya sake rufe ta, domin ba ya son ko kaɗan ta gudu ta kai ƙaran sa, shiyasa zai mata horo da haka, kuma nan ba da daɗe wa ba zai san abun yi, domin ba ya so a fuskanci komi sai ya gama gana mata azabar da ya tanadar mata, yayi wa kansa alƙawari sai tayi dana-sanin rayuwan ta.

    Ita kuwa Ɗahira ko ci kanka bata ce masa ba har ya fice, domin wani irin baƙin ciki da zallan tsanar sa ke nuƙurƙusan ta, shiyasa baza ta iya tambayan sa ina zai kai mata waya ba.

     Ta jima a nan zaune tana kuka, gaba ɗaya ta fita hayyacin ta, har wajen ƙarfe 10:30pm. tana nan a haka, zazzaɓi me zafi ya rufe ta, dole ta rarrafa ta isa inda ta ajiye sauran maganin da tasaka a kawo mata jiya, ta ɗauka ta isa ga Fridge ta samu ruwa, sai dai bata sha ba sai da ta kora drinks ɗin da ta gani a ciki, domin ba ƙaramin yunwa take ji ba, ga shi mugun can ya rufe ta, tana tunanin wannan wani irin mugu ne da zai rufe ta a ɗaki? To me yake nufi da hakan? Shi ne bata sani ba.

     Tana gama shan maganin ta kwanta, sai dai ta kasa barci sai juye-juye take yi, daƙyar barci ɓarawo ya sace ta.

      Washe gari koda ta farka da safe, sabida yunwan dake cin ta ta nufi ƙofa don ta fita ta nemi abinci, amma sai taji ƙofar a garƙame, wani irin jijjiga ƙofan ta hau yi tana kiran sunan sa, nan da nan hawaye suka soma zuba a kyakykyawar fuskar ta da ta gama kumbura, ta sauya kamanni. dama ba ƙwarin jiki ne da ita ba, sai ta zube a nan ta hau rusa kuka, sosai take kuka tana kiran sunan sa ya zo ya buɗe ta.

      Amma Usman yana zaune a Parlour Yana jin ta be ko motsa ba, illa gyara kwanciyar sa da yayi ya ci gaba da latsa wayan sa, sai ma da yaji ta ishe shi sai ya kunna t.v ya ƙure ƙaran

Hakan ya tabbatar wa da Ɗahira yana nan zaune yana jin ta, wani irin kuka ta saki tana zame wa ta kwanta a wajen, ta ma rasa wani irin tunani zata yi, illa zuciyar ta dake ta faman zugi tamkar ta faso ƙirjin ta, “ashe ya shirya mata mugunta ne shiyasa ya ɗauke wayan ta, domin kar ma ta nemi wani ta waya”

Kukan ta tasha ta tashi zaune, shiru kawai tayi tana tunani hawaye na zubo mata, “me zata yi masa ta huce? Tana ga baza ta iya zaman auren nan ba, dole ne yau ta fita ta koma gida, dole ne kowa ya san halin da take ciki, da dai ta zauna a gidan sa ta gummaci a raba auren nan tun yanzu, ta matuƙar tsanar sa! kullum sake jin tsanar sa take yi a rai, domin ba shi da tausayi ko kaɗan.

        Miƙe wa tayi riƙe da cikin ta dake faman ciwo, ta nufi Fridge ta buɗe, drinks ta ɗauka tasha sosai, ta kwanta saman gado tana ta faman tsiyayar da hawaye.

    Wasa-wasa wunin ranan currr Usman ya ƙi buɗe ta, tun tana ɗaukar abun da wasa har taga ta kusa mutuwa saboda yunwa, domin bata da abun sha sai drinks, gaba ɗaya cikin ta ya gama ƙulle wa

Shi kuwa yana Parlour ko jirgau be yi ba, sallah kawai yake tayar dashi, duk wanda ya zo neman ta sai yace musu “tana barci”. Har da masu zuwa ganin ɗaki ƴan cikin anguwa, da friends ɗin ta na wajen aiki, duk sai da Usman ya kora su, aka aiko Fadil da abinci, ya amsa ya rufe ƙofan, ya kuma je ya ajiye be ci ba be kai mata ba.

     A haka Ɗahira ta kwana a mawuyacin hali, ga yunwa ga zazzaɓin da koda yaushe yana jikin ta, sakamakon damuwa da kukan da take wuni yi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button