FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

    Bayan ta gama ta zare Hijab ɗin jikin ta, sannan ta sauya kaya zuwa Arabian gwon baƙa da kwalliyan stones, sosai rigan ta haska fatar ta ta ƙara mata kyau ainun, duk da sosai zaka ga raman da tayi matuƙa, amma kuma ta sake kyau saboda hutu da ta ɗan samu waɗannan satikan ba tare da ta taɓuka komi ba

Tana gama wa ta fito Parlour, zaman ta tayi tana jiran kuma next me zai ce tayi. har ƙarfe ukun ta gota be fito ba

Sai uku da rabi sannan ya fito cikin shirin sa, sosai yayi kyau kamar ka sace sa ka gudu, shigan dai da ya saba na ƙananan kaya shi yayi, wandon me ruwan ƙasa jeans, sai farar riga da aka yi harafin U a gaban rigan da coffee colour, kayan sun yi masa kyau sosai sun kuma haskaka skin ɗin sa, musamman ma da yayi amfani da coffee Cumbas sai ya ƙara haɗe wa, kansa ba hula sai kwantaccen gashin kansa baƙi siɗik da ya sha gyara har zuwa sajen sa suna shaining. Shima yana jaye da ƙaramar Trolly wanda tafi na Ɗahira ƙanƙanta, ba kaya ya zuba ba abubuwan buƙatar sa ne a ciki, irin su laptop da sauran su, saboda  yana da komi a can, kayan sawan sa ma na can daban ne

Jan Trollyn yayi ya nufi ƙofa zai fice

Ganin haka itama Ɗahira sai ta fito ta biyo shi, tana fita ta ganshi tsaye bakin ƙofan, sai tayi saurin jan Trollyn ta tayi gaba

Shi kuma komawa ciki yayi rai a haɗe ba tare da ya kalle ta ba, jin ƙai ya hana sa furta komi bare ya saka ta taje ta kashe kayan wutan gidan, ya gummaci shi yaje yayi da ya furta mata

Har ɗakin ta sai da yaje ya kashe komi na na’ura, sannan ya fito, ya rufe gidan ya nufi parcking space, inda Ɗahira ke tsaye tsakankanin motan ta da na shi; rana sai faman gasa ta take yi, dayake ba inuwa a wajen, sai faman jan tsaki take yi cike da takaicin sa, “don me ya saka ta ta fito sannan ya shanya ta a waje ya koma ciki? Miskilin mutumi kawai”. Ta sake jan dogon tsaki tana ɗago kai, sai ta ganshi gab da ita yana taho wa, da sauri ta ɗauke kai daga kallon sa duk da shi ba ita yake kallo ba, amma sarai yaji tsakin da tayi, shiyasa ya sake tamke fuska kamar hadarin kaji, irin ba mutuncin nan

Boot ya buɗe ya saka Trolly ɗin sa, sannan ya bar shi a buɗe ya shige motar sa

Hakan yasa itama Ɗahira ta saka nata a ciki, sai ta rufe ta zo tayi tsaye a gefen motan tana tunanin inda zata shiga

Horn ya danna mata da ƙarfi, dole yasa ta buɗe gaba ta shige tayi zaman ta, shi kuma yaja motan yayi bakin Gate Yana sake cin magani, sai dai miskilanci ya hana sa tanka wa bare ya faɗa abinda ke ransa

Ita kuwa duk a takure take da ganin su waje ɗaya cikin mota, tunda hakan be taɓa faruwa ba

Haka zalika shima hakan yake ji, shiyasa ya ke tsula gudu shaf-shaf suka kai, don kawai ya ƙosa ta fice masa a mota.

    Suna kai wa airport wani abokin Usman ɗin ya zo ya tarbe su, shi Usman ɗin ya saka yayi musu komi da za su buƙata, ko passport da za’a yi wa Ɗahira sai dai ya samo picture ɗin ta a wayan Fadil.

        Jira kaɗan suka yi aka kira su, suka shiga jirgin. Kujeran su na side ɗin juna ne, ita tana ɓarayin dama a kujeran hanya, sai wata a gefen ta a lungu. Shi kuma yana gefen hagu ne a lungu, shima yana tare da mace ce a gefen nasa. A haka jirgin nasu ya tashi ba tare da magana ta sake shiga tsakanin su ba, tamkar ma dai ba tare suke ba, domin babu wanda zai ce ma suna da alaƙa da juna in ba kaman da suke yi ne zai tona asirin su ba.

      Ɗahira lumshe idanun ta kawai tayi ta jinginar da kanta saman kujeran, ba yau ne karon farkonta na hawa jirgi ba, shiyasa bata nuna ƙauyanci ko wani tsoro ba, sabida ita ɗin wayayyiya ce, lokacin da suka gama secondary School gaba ɗayan su yaran gidan Kaka ya biya musu kuɗin hajji suka je suka sauke farali.

      Ɗahira ko kaɗan bata ji daɗin tafiyan nan ba, domin baƙin cikin ta bata yi sallama da su Abbu ba, ya kamata ace ya bari sun dawo kafin su tafi, amma kuma babu hali, but tun farko da ya faɗa mata da wuri tun jiya ya kamata taje cikin gidan tayi wuni tare da yin ma kowa sallama cikin natsuwa. Amma kuma Allah ya haɗa ta da murɗaɗɗen mijin da babu me iya saka shi bare hana shi, ita gaba ɗaya ma tsoro ya kamata don bata san me zai faru ba idan suka je inda babu kowa nata, yanda yake da baƙin halin nan bata san ya zaman nasu zai kaya ba.

.

To mu ma zamu bi ku muga ya za’a kaya. Shin wani irin zama zaku yi a can ɗin? Meye a zuciyar Usman?

wanda yaga yana da kuɗin jirgi sai ya biyo mu ato, don Ni ba Ni dashi gaskiya, bazan iya biya muku gaba ɗaya ba. ????????????
????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

\F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

.

        EPISODE Forty One

            Kafin jirgin su ta sauka, tuni Ɗahira da Abokiyar zaman ta sun zama ƙawaye, domin sosai suka sha hira a tsakanin su, inda har suka yi sauyin number, Ɗahira ta amshi Numban nata cikin takarda kasancewar babu wayan ta a hannu

Ita yarinyan ne ma ta rubuta mata a wani memo ta bata, sai ta kwashe nata cikin wayan ta. Matashiyar budurwan wacce zata yi sa’anni da Ɗahira, tana karatu ne a can Turkey, kuma tana zaune ne wajen Sister ɗin ta dake aure a can tare da Mijin ta, sunan ta Zakeeya. Kasancewar ƙasa ɗaya za su je shiyasa hiran nasu tayi tsaho har suka zama kamar sun san juna.

             Jirgin na sauka a ƙasar Turkey, cikin birnin Istanbul, sallama suka yi akan za su nemi juna bayan sun natsa, in yaso sai su san muhallin juna su riƙa ziyartar junan su, duk da ita Ɗahira bata sanar mata asalin abinda ya kawo ta ƙasar ba, hasali ma ko ce mata su biyu ne tare da Mijin ta bata sanar mata ba

Koda suka sauka jirgi ma, ita Zakeeyan ta soma mata sallama ta wuce, har tayi mata tayin tafiya a motar su, amma tace, “a’a suna tare da wani ne”. Da haka suka yi sallama.

           Ɗahira jan Trollyn ta tayi ta isa inda Usman ke tsaye yana tare Taxi, shi be ce mata komi ba duk da ya ga yarinyan da suke ta hiran, motan kawai ya hau, itama ta shiga baya suka zauna waje ɗaya, babu me motsin kirki cikin su har suka isa muhallin Usman ɗin, Plate ne gidan ƙarami na zaman mace ɗaya, kuma mallakin Usman ne, tunda anan ya sauna lokacin da yake aiki.

         Fita suka yi suka shiga gidan, Ɗahira na biye dashi ita dai tana ta kallon abubuwan burge wa, gaba ɗaya anguwan ya tafi da imanin ta, shiru babu wani hayaniya, zai yi wuya ka haɗu da mutum ma, dama ita Ƙasar Turkey Yana ɗaya daga cikin ƙasashen dake matuƙar burge ta, musamman mutanen ciki ma’abota addinin musulunci, da shigan da suke yi.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

             Tunda Hajja Fatu ta dawo tacid da mummunan labarin nan na tafiyan su Ɗahira ƙasar waje, sai hankalin ta yayi mugun tashi, domin bata da labari ko kaɗan, ko su su Big Dady da suka sanar wa matan su da safe Kaka ya faɗa musu, lokacin sun je gaishe shi. To sai suka dawo suka sanar wa matan su, yayinda Abba kuma ya wuce Hospital, tunda ya san cewa Hajja Fatu tuni ta tafi asibitin, kuma da ya je can be samu ya sanar mata ba har sai da suka dawo, lokacin su ma sun ji labarin har sun tafi, sai sukai musu fatan alkhairi kawai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button