FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

\????.????.????????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

               HADHISI
An karbo dga Aisha Allah ya ƙara yarda agareta tace ” Manzon Allah s.a.w ya aureta tana da shekara shidda,kuma yatare da ita tana da shekara Tara,kuma Allah ya karbi ransa tana er shekara sha takwas. Muslim ya ruwaito

.

       EPISODE Thirty Two

         Ɗago kanta tayi tana kallon sa, sai tayi saurin ƙirƙirar murmushi tace, “No, I’m not crying, abu ne ya faɗa min a ido shiyasa”.

Duk da be yarda ba, sai yace, “Eyya sorry! Amma dai ba tafiya zaki yi ba?”

“I’m going Yaya Sulaiman, har da gidan Shakira zan je, and Mama says” I’ll be back soon “.

“To babu damuwa, ki gaida mutanen gidan don Allah”.

“Insha Allah, they will”.

Hannu yasa cikin aljihu ya fito da kuɗi yana faɗin, “amma shi ne Yusran bata zo ta taka miki ba?”

Bata ce mishi komi ba, tunda bata san me zata ce mishi ba

Sai ya miƙa mata kuɗin har 20k Yana faɗin, “ga shi babu yawa kiyi haƙuri”.

Girgiza kanta tayi tace, “a’a wlh bazan amsa ba, ka bar shi Yaya Sulaiman”. Tana faɗan hakan ta wuce sa ta bar wurin

Da kallo ya bi ta da shi har ta kai wajen motan ta, kafin yaja numfashi yana mayar da kuɗin cikin aljihun sa, ƙofan ya buɗe ya shiga ciki da sallama

Yusra dake zaune har yanzu a inda take, tana faman karkaɗa ƙafafu tana latsa waya, ɗago wa tayi tana amsa sallaman nasa idanun ta a kansa

Shi kuwa a kan Centre table ɗin ya sauke idanun sa, zuciyar sa sosai take ɗarsa masa tabbas Yusra ce tayi wa Ɗahira wani abun, domin ya san cewa Yusra ba ta shiri da ita, tunda sau nawa take faɗar magana a kanta, kuma sannan ba ta son ko kaɗan yayi maganar ta a waje, idan yayi kuma ta dinga kushe ta kenan

Kallon ta yayi yace, “meyasaka Ɗahira ta tafi tun yanzu?”

Taɓe baki tayi tace, “can ta matse mata nima ban sani ba”.

Waro ido yayi kanta yana sake gasgata abinda ke ransa, sai kuma ya juya yana kwaɗa wa me aikin nasu kira. Tana fitowa ya tambaye ta “ina abincin nan da na ga Ɗahira tana ci? Yanzun nan daga fitan ta har kin kawar da Plate ɗin?”

Jiki na rawa matar tace, “wlh ranka ya daɗe! Uwar ɗaki na ce ta sanya Ni na ɗauka na mayar tunda abincin ka ne”.

“Kina nufin tana zaune a nan ta saka ki kika ɗauke?”

Jiki a sanyaye ta duƙar da kanta ƙasa saboda uwar hararan da Yusra ta banka mata, ta amsa mishi da “eh. Amma a gafarce Ni yallaɓoi, ba laifi na ba..”

“Je ki abun ki Baaba”.

Da sauri ta wuce ta koma kichen

Sai ya mayar da idanun sa kan Yusra dake ci gaba da karkaɗa ƙafafun ta, tamkar ma bata damu da abinda yake tambaya a kai ba, yace da ita, “Yusra wai Ni shin in tambaye ki? Ɗahira ba ƴar uwan ki bace?”

Ɗago kai tayi tana kallon sa, sai ta turo baki ta soma magana

Ya katse ta da faɗin, “amsa nake so”.

“Ƴar uwata ce mana”.

“Ok ƴar uwan taki ce ta zo gidan nan, kika wulaƙanta ta ko? Shin kin san kuwa abinda kike yi? Da kuka fa ta bar gidan nan”.

Shiru tayi masa

Cike da ɓacin rai yace, “yayi miki kyau! ki ci gaba da abinda kike yi, Ni babu abinda ya shafe Ni, amma ki sani ranan da zaki yi nadama na nan zuwa”. Yana gama faɗar maganan nasa yayi cikin ɗaki da sauri

Tsaki taja kafin ta miƙe tabi bayan sa.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

           Murza sitiyarin ɗin motan take yi zuciyarta na ƙuna, sosai take jin ƙunci da abinda Yusra tayi mata, numfashi kawai take sauke wa duk socond baƙin ciki na ƙara wanzuwa a zuciyar ta, nan da nan kanta ya soma mata ciwo sabida damuwa da tuno abinda tayi mata ya haifar mata, sosai take dana-sanin rashin amayar mata da ƙuncin da ta saka mata, sabida ta san ita zai cuta, amma kuma ta ga ita ta kawo kanta shiyasa be kamata ta biye mata har wani saɓani ya shiga tsakanin su ba, but she promised she would never see her again in her home.

Ta so koma wa gida, sai kuma ta ga be dace taƙi zuwa gidan Shakira ba, can ta wuce duk da bata san gidan ba, sabida kwatancen akwai wahala sosai in dai ba ka taɓa zuwa bane, dole ta kira Baffa ya sake mata kwatancen gidan kafin ta gane

Itama gidan nata babu laifi tunda ita kaɗai ce, amma kuma na Yusra yafi girma da haɗuwa, mijin ta Sahabi aiki yake yi a Companin wutar lantarki.

       Sanda ta shiga gidan da sallama, Shakira na zaune a Parlour tana cin abinci tana kallo, ganin ta yasa ta tashi da fara’an ta ta rungume ta

Murmushi Ɗahira tayi, cikin sanyin murya tace, “ƴar uwa nayi missing ɗin ki sosai da sosai”.

Dariya Shakira tayi tace, “ai wlh baki kai Ni ba sister, tun sanda Hajja ta kira Ni tace kina nan zuwa na zauna a nan zaman jiran ki, meyasa ma kika fara zuwa wajen wancan mara mutuncin? Tunda kin san ba shiri kuke yi ba, Allah yasa dai ta amshe ki hannu bibbiyu bata miki wulaƙacin da ta saba ba, ba Ni nasha don Allah ya kuka kwashe?”. Ta ƙare maganar har da gyara zaman ta tana zuba wa Ɗahira idanu

Shiru Ɗahira tayi, nan maganar da Fadila ta faɗa mata ya faɗo mata, hakan yasa ta saki murmushin yaƙe tace, “ke dai Shakira, daga zuwa baza ki bari na huta ba sai ki soma min gulman wata?”.

Hannun ta ta watsa saman cinyoyin ta tana faɗin, “ai wlh ke dai bari Sister, na damu dake ne wlh, domin nasan halin Yusra yanda ta tsane ki, ruwan gidan ta ma baza ta bari ki sha ba”.

“Uhm to babu abinda ya faru tsakanin mu, ta amshe Ni hannu bibbiyu, har abinci na ci”.

Ƙure ta da ido Shakiran tayi, sai ta taɓe baki kamar dai ba haka ta so ba, tace, “na ji ki amma dai ban yarda ba, domin wlh ina ji a jiki na akwai abinda ya faru a gidan ta, uhm Ni zan faɗa miki wace ce Yusra a kan tsanar da tayi miki”.

“Ya isa don Allah, Ni dai ba na son zancen nan, wlh kai na ciwo yake yi, daƙyar ma na ƙariso”. Ɗahira ta ƙare maganar da dafe kanta, sosai take takaicin wannan sabon halin da ta gano na Shakira, “meyasa ma tun farko ta kasa gane ita ɗin me fuska biyu ne? Yanzu da ba don Fadila ta faɗa mata halin ta ba, haka zata zauna tana bugan ruwan cikin ta, tana nuna tamkar ta damu da ita, amma kuma a baɗini ba haka bane, Allah ya kyauta ya ƙara nuna mana maƙiyar mu a fili..

Maganar Shakiran ne ya dawo da ita guntun tunanin da ta afka

“Bari in sawo miki abinci ki ci”.

Har ta miƙe Ɗahira tace da ita, “bar shi kawai, Ni bazan iya cin komai ba”.

“Kenan dai da gaske ne Yusran ta cika miki ciki da abinci?” Shakiran ta faɗa cikin dariya, sai dai a zuciya baƙin ciki ne tamkar ya karta

Murmushi Ɗahira tayi tace, “ina mijin naki mu gaisa tunda rowan sa kike min?”.

Dariyan ta sake kwashe wa dashi tana faɗin, “wlh kuma kin yi rashin Sa’a ne, domin yanzu ya fita, shaf kuma na manta ban ce masa ya tsaya zaki zo ba, sai ku gaisa”.

“Haka kawai ki tsayar da shi don zan zo? A’a gwara ma da baki yi ba, wataran zamu haɗu ai, nima ba daɗe wa zan yi ba yanzu zan tafi”.

Hararan ta Shakira tayi tana miƙe wa tace, “kan bu..! Wlh babu inda zaki je yanzu, daga zuwan ki? Ki bari zuwa anjima don Allah”. Ta ƙare maganar sanda ta isa gaban Fridge ɗin ta, drinks ta ɗauko mata, ta haɗo da Cup ta kawo gaban ta ta ajiye akan Centre table da ta janyo, tsiyaya mata tayi ta miƙa mata

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button