FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

Yanda ka san t.v haka Ɗahira take bin ta da idanu, har sai da ta dire Aya kafin ta tashi zaune tana bin ta da kallo sosai, ko kaɗan ba ta jin daɗin Jikin ta, kuma har ga Allah ba ta son ta biye mata, amma kuma gani take yi idan har ta bar ta ta tafi bata mayar mata da martani ba, to, tabbas nan gaba ma zata dawo tayi mata irin wannan cin mutuncin, kuma zata ga kamar tsoron ta take ji, don haka ta saki guntun murmushi tana kallon ta tace, “wa kike da suna? Yusra ko? Ni ba sa’an yin wasan ki bane, tun wuri ki kama kanki, domin shiru-shiru ba hauka bane, wlh ina ƙyale ki ne kawai don Ni ba Kaza bace da zan zauna kullum ina sa’insa da ke, na san mutuncin kaina; na kuma san kima ta, amma wlh muddin kika sake shigo min gida na, kika yi min irin wannan halin karnukan, zan baki mamaki Yusra, zan nuna miki Ni ba’a sha na a warke, domin zan nuna miki ainihin hauka na wlh”.

Shewa Yusra ta saki tana tafa hannu tace, “an yi miki duk abinda zaki yi ki yi, ai Ni dama so nake yi ki ɗau mataki sai in San kin cika ke tatacciyar mara mutunci ne, kuma ke baki isa ki hana Ni zuwa gidan ɗan uwa na ba wlh, kin yi kaɗan, nonsense…”

“Wai hayaniyan me nake ji ne? What’s going on here?” Cewar Fadila da ta shigo da sauri, dama Breakfast ta kawo musu shi ne ta jiyo kamar hayaniya

Ɗahira tace, “Ask her to come and find me in my room,”

Tsaki Yusra taja tace, “wlh mu zuba dani da ke”. Tana faɗa ta juya ta fice.

Ƙarisowa Fadila tayi bakin gadon tana zama tace, “wai me ke faruwa ne? Me ya haɗa ki da ita?”

“Babu komi Fadila, kin san halin ta ba tun yau ba, ban san me na tsare mata ba ita da Yayan ta suka bi suka tsane Ni, ban san me nayi musu ba”. Ɗahira ta ƙare maganar cikin damuwan da ya nuna a muryan ta

Ajiyan zuciya Fadila ta sauke, sai kuma tace, “ki yi haƙuri da duk halin su, Ni ban san meyasa Yusra take wannan ɗabi’an banzan ba, amma yanzu ba ta Ita zaki yi ba, ta Mijin ki zaki yi, duk hanyar da ya dace shi zaki bi domin samo soyayyar shi, ke ba yarinya bace Ɗahira, kin san abun kuma da ya dace, batun tsana ko rashin sa duk be taso ba yanzu, yanzu kun zama ɗaya ke da shi, aljannan ki kawai zaki nema, kar ki soma ki biye mishi, na san zaki iya ƴar uwa, haƙuri shi ne zai sa ki cin ma Nasara kinji? Domin auren ku muna fata mutu ka raba ne”.

Murmushi Ɗahira ta saki tana jin hawaye na son cika mata idanu, sai tayi saurin kawar da kai tana ɗan rufe idanun ta tare da komar da su

Fadila tace, “yanzu ina Angon naki? Ga abinci can na kawo muku sai ki je ki tashe shi. Amma kin ban mamaki fa”.

Kallon ta Ɗahira tayi da son ƙarin bayani

“Kya waro min Ido mana, ji be ki don Allah mana, kin zauna har sha biyu da rabi baki yi wanka kin shirya ba, ta hakan ne zaki dai-dai ta gidan ki?”

Wannan karon dariya Ɗahira tayi, sai ta tashi kawai ba tare da tayi magana ba, domin sosai take jin jikin ta babu daɗi

“To Ni bari in tafi, zuwa anjima zan sake leƙo ki, zuwa gobe insha Allahu duk zamu tarkata, na san ma yanzu su Momy suna nan shigo wa”. (Tana nufin mahaifiyar K.B Hajiya Ikram) tunda ta koma can sai ya zamana itama Momy take ce mata kamar sauran ƴaƴan ta, saɓanin a baya da suke kiran ta Gwaggo Rabi.

Har Fadilan zata fice, sai Ɗahira tace mata, “ta zo mata da maganin ciwon kai”.

Amsa mata kawai tayi Sannan ta fice

Ita kuma ta shiga wanka, sai da ta fito ta shirya cikin atamfa baƙa da kalan fari da coffee, ɗinkin riga da zani raffer, tayi kyau sosai, sai dai yau komi bata shafa a fuskar ta ba duk da kasancewar ta me son kwalliya, ɗankwalin kawai ta ɗaura ta fito Parlour

Da kallo kawai take bin ko ina, har ta isa kan dainning ɗin, duba abinda aka kawo musu tayi, sai kuma ta juya ta nufi ɗakin da ta gani kusa da na ta, tsaya wa tayi a bakin ƙofa tana tunanin shiga ko a’a, don ta san nan ne ɗakin Usman, sosai gaban ta yake faɗi, don har yanzu bata san wani irin zama za su yi ba

Bismillah tayi kawai ta tura ƙofan da sallama, bayan tayi Nocking ba’a amsa mata ba. Sai dai babu kowa ciki, sai da ta gama ƙare wa ɗakin kallo gunun ban sha’awa irin nata komi da komi, sai dai kayan ɗakin ta ya fi yawa tunda ita mace ce, amma har ta colours ɗin ciki iri ɗaya ne

Fitowa tayi ta koma kan dainning ta hau yin breakfast ɗin ta, sai dai har ta gama a tunani tayi Breakfast ɗin

Ɗaya daga cikin ƙannin K.B suka kawo mata maganin da tace a kawo mata, amsa tayi tasha ta zauna a kan kujera tana faman tunani

A haka sauran mutanen gida sukai ta shigo wa ganin ɗaki, da masu tafiya da waɗanda sai gobe za su tafi, ƴan Maiduguri dai duk yau suka watse

Daga ƙarshe su Shamsiyya da Shakira, Firdausi, Salma da sauran sa’annin ta duk suka cika sashin, suna ta hira

Tun Ɗahira ba ta biye musu har dai ta saki jiki ana ta yi da ita, tuni ta wartsake abun ta

Suna ta tsokanar ta wai “daga aure ango ya tafi ya bar ta,” masu kare mata suna yi, har da Shakira Iyayen gulma, ita dai sai dai ta bi su da dariya kawai.

     Sai magriba duk suka watse suka bar ta, ta shiga tayi sallan magriba, sannan ta dawo Parlor, tunda nan ya ɗan fi haske, da wayan ta ta haska tayi zaman ta tana ci gaba da faman tunanin ta, babu abinda ke tsaya mata a rai, sai yanda za su yi zama da wanda ya tsane ta; itama kuma ta tsane shi

Kafin a kira sallan isha’i aka kunna musu gen, tunda duk generator ɗin su haɗe yake dana Part ɗin Baffa

A lokacin ne aka sake kawo musu abincin dare, tana amsa ta ajiye saman dainning ta wuce ɗakin ta ta rufo ƙofa, alwala tayi ta gabatar da sallan isha’i, sannan tayi shafa’i da wutri, ta roƙi Allah buƙatun ta, sannan ta sauya kaya zuwa rigan barci doguwa tayi kwanciyar ta, da haka tana tunani har barci ya ɗauke ta.

             *

           Kamar jiya, haka ma yau Usman sai ƙarfe 01:00am. Ya dawo gidan. Ko kallon ɗakin ta be yi ba ya shige nasa, wanka yayi ya sauya kaya zuwa na Barci, dama ya rigada yayi sallan sa a masallaci, sai yayi kwanciyar sa, tare da kitsima abubuwan da yake son aiwatar wa, don samun mafita daga wannan kaddararren auren.

     Washe gari haka ya sake tsallake wa ya fice a gidan, shi fa sam ganin ta ne ba ya son Yi ma, shiyasa yake fice wa. Ga shi Big Dady yace masa kar ya soma ya ga ƙafafun sa a Hospital idan har ba two weeks yayi ba.

       A yau duk sauran mutanen da suka zo biki suka watse, dama duk yawanci ƴaƴan Kaka ne su Hajiya Ikram da Hajiya Laila, sai ƴaƴan su wasu  da ba su tafi ba, sai kuma ƙannin Kakan, su Hajiya Baseera da Hajiya Hannatu (Ihsan). Duk dangi na kusa ne. Kuma duk yau suka gama watse wa

Aunty Zulaiha CE kawai ta kai yamma, itama don tana jiran mijin ta ne, da zata tafi sai da tazo har Part ɗin Ɗahira, a nan take ce mata “ta shirya taje Part ɗin su Usman ta gaishe da Hajiya, idan da hali ma ta zauna a can sai zuwa dare ta dawo”

Tana tafiya ta shirya kamar yanda tace mata, doguwar riga abaya baƙa ta sanya, me kwalliya sosai a gaban rigan na flower, sai ta yane kanta da gyalen abayan, ta saka turare a jikin ta tare da takalmi ta fito riƙe da wayan ta

Tana fito wa Part ɗin ta suka haɗa idanu da Baffa dake zaune saman farandan gidan sa, ya haɗe ƙafafu ya ƙura wa Part ɗin nata idanu yana faman tunani. Ganin ta yasa ya sauke ƙafafun ƙasa yana mata murmushi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button