FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

Numfashi Ayush taja, kafin tace, “hmm yanzu kin yarda da Ni Ko?”

“Ƙwarai kuwa.. shiga mota mu je, ina da hanyar da za mu ɓullo masa, idan ya san wata ai be san wata ba, na saba haɗuwa da irin waɗannan guy ɗin masu murɗaɗɗen hali, kuma mun ci galaba a kansu”. Ta yi maganar tana taunan cwhengum

Murmushi Ayush tayi, kafin suka koma cikin motan, Safra taja suka bar Hospital ɗin.

.

Ko Me Za su shirya? ???? Muna dai biye da su ai.
????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

\F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

               NASIHA
Muna iya lura cewa ga al’ada in an Kira talaka zuwa fadar sarki yakan gyara fuska, ya yi ado don ya sami kyakkyawar maraba daga Sarki. To, in haka ne, ina ga in ya tashi zuwa tsayuwa gaban Ubangijin sa? Bawan da aka neme shi ya zo gaban Ubangiji, Sarkin sarakuna, mamallakin mamallaka, lalle kam ya fi kamata ya gyara kansa saboda wannan muhimmin muƙami. Ya kamata ya gyara kansa ta tsarkake tufafin sa da jikin sa, ya fito cikin kama mafi kyawu, kamar dai yadda aka umurci musulmi duka a cikin suratul A’ARAF, aya ta 31:
“ya ɗiyan Adam! Ku riƙi ƙawar ku a wurin ko wane masallaci”
Allah yasa mu dace.

.

         EPISODE Thirty Three

“Kina da kuɗi a tare da ke? Domin kai tsaye wajen Malami na za mu wuce”.

Kallon ta Ayush tayi, sai kuma ta girgiza mata kai alamun “A’a” kafin tace, “Malami kuma Safra? Wanne irin Malami? Me kuma zamu yi a can?”

Dariya tayi still tana taunan cwhengum ɗin ta tace, “neman biyan buƙata mana Ƙawata, Ai dole sai da haka, don wlh bari kiji, irin waɗannan Guy ɗin ba naki bane, kee wlh bazan yi kaffara ba, idan har kika ce ta haka zaki jawo hankalin sa, babu taimakon Malamai, to, zaki dauwama baki yi aure ba, domin wlh sai kin ruɓe a gidan ku. Yanzu dai za mu wuce wajen Malam, inyaso zan ranta miki kuɗi idan muka dawo ki bani”.

Ayush dai ta kasa cewa komi illa kallon titi da take yi, tana me tunani a zuciyar ta, “anya wannan hanyar da ta ɓullo wa kanta me ɓulle wa ne? Domin tasha jin yanda mutanen da suke zuwa wurin boka suke ƙare wa, to amma dogon burin ta fa? Hakan na nufin muddin bata nemi taimako wajen su ba, to, har abada baza ta taɓa auren Usman ba?..”.

         Kai tsaye hanyar Zaria suka nufa, sun kusa shiga Zarian, sai suka karya kwana suka bi wata hanya, tafiya miƙaƙƙa suka yi a cikin hanyar me kama da jeji, domin ko kaɗan babu gida gaba bare baya. Sun yi tafiya sosai kafin suka soma hango ƙauyaku, inda suka sauka a wani ƙaramin gida da aka zagaye shi da kara, sai bukka da aka yi su da yawa a wajen, shiga suka yi gidan, inda Ayush sai kalle-kalle take yi tana biye da Safra dake tafiyan ta kai tsaye, ba tare da wata fargaba ba, ga duk kan alamu ta saba da zuwa

A bakin wani bukka dogo suka dakata, inda Safra ta hau faɗin, “an gaishe ka Malam, an gaishe ka Malam”.

Daga ciki dariya ne ya biyo baya, inda yace, “Hajjaju Safra da baƙuwar ta, maraba da zuwa, za ku iya shigo wa”.

Shiga Safra tayi, inda Ayush ke biye da ita

Yana da faɗi cikin bukkan, babban mutum ne fari sol yake zaune a gaban wani ƙaton ƙwarya baƙi, yana ɗaure da zanin atamfa a jikin sa yayi tamkar yanda ƴan Saudiya suke yi idan za su yi aikin hajji, sai gashin kansa me yawan gaske tamkar na mace, ya zubo masa har kafaɗun shi

Da kallo ya bi su dashi har suka zauna, kafin yace, “an sanar min da zuwan ku tun kuna hanya, kuma na san abinda ya kawo ku”.

Ayush ce kawai tayi mamaki da kalaman sa, ban da Safra da ba yau ta soma zuwa ba

Kallon Ayush ɗin yayi yana faɗin, “yanzu me kike so ayi masa?”

Kallon Safra tayi, itama kuma ta gyaɗa mata kai alamun “ta sanar masa”

“Malam ina ƙaunar sa matuƙa, kuma so nake yi a saka mishi ƙauna ta yaji duk duniya babu wanda yake so face Ni, ina son ya zo min da buƙatar auren sa”.

Tsare ta da ido yayi tamkar be san me take cewa ba

Sai ta kalli Safra a tsorace, sabida ba ƙaramin tsoro jajayen idanun sa suke bata ba, musamman da ya ƙure ta da su tamkar zai cinye ta

Hannun ta Safra ta kama tana son kwantar mata da hankali

Muryan sa suka ji yana cewa, “kee yarinya! Idan har aka zo nan ba a shigo min da tsoro, tun wuri ki dena jin tsoro na, idan ba haka ba, to zan saka miki wasi-wasi a zuciya, kuma duk abinda zan miki baza ki taɓa ganin dai-dai ba”.

Da sauri Ayush ta gyara zaman ta tana cewa, “kayi haƙuri, bazan sake ba”.

“Da yafi miki”. Ya faɗa yana taɓa hannun sa a cikin ruwan dake gaban sa cikin ƙwarya, zane ya soma yi na ɗan mintoci, kafin ya ɗago yana kallon ta yace, “leƙo nan”.

Matso wa tayi ta tura kanta ta yanda zata ga cikin ƙwaryan, Usman ta gani zaune a Office ɗin sa, yana shingiɗe a kan kujera idanun sa a rufe, kujeran na faman juya sa

“Wannan shi ne ko?”

Da sauri ta gyaɗa masa kai tana faɗin, “eh shi ne Malam”.

Ci gaba yayi da zanen sa na ɗan wani lokaci, kafin ya ɗago yana duban su yace, “kina da rabon auren sa, sai dai a nan gaba, domin na ga gagarumar matsala tana kunno wa daga dangin sa, suna shirin aura masa ƴar uwan sa nan ba da jima wa ba. Kuma na duba duk yanda za’a yi, babu ta yanda za’a hana auren nan, dole ne sai ya aure ta”.

“Malam kana nufin dai sai ya auri wata kafin ya aure ta?”

“Eh haka nake nufi”.

“Amma meye mafita Malam?”. Safra ta sake tambayar sa

Numfashi yaja kafin yace, “wannan yarinyan ƙaddaran sa ce, kuma dole ne sai ya aure ta babu yanda za’a yi, bazan iya muku aiki ba yanzu har sai sanda aka yi auren nasu, sannan ku dawo akwai abin yi, a nan ne nake da daman raba su ke kuma ki shiga, in har ba haka ba kuwa, babu ta yanda zaki aure sa tana cikin gidan sa”. Ya ƙare maganar da nuna Ayush da duk ta gama firgita da jin abinda yake faɗa

“Yanzu Malam babu abinda zaka iya yi a kai? Ya kamata kayi wani abun, domin mun san zaka iya ne”.

Cikin amon muryan sa yace, “babu abinda zan iya a kai yanzu, duk abinda kuke so ku dawo bayan auren su, a nan ne zan iya muku komi, ku tashi ku tafi”.

Da sauri suka tashi sabida jin tsawan da ya danƙara musu, suka fice suka nufi motan su, hawa suka yi suka bar wajen, babu me magana cikin su har sanda suka fito bakin titi

Da damuwa a fuskar ta tsantsa Ayush tace, “yanzu ya za mu yi? Ga shi mun zo wajen Malamin, memakon samun mafita, sai faɗa min abinda ya ɗaga min hankali yayi, kuma ya ƙi mana aikin”.

Numfashi Safra taja kafin tace, “ke a naki tunanin, wace ce yarinyan da kike ganin za’a haɗa su aure?”

“No bazan taɓa sanin hakan ba gaskiya, domin Familyn su babba ne, kinga babu ta yanda zan yi in gane wacce zai aura, kuma kwanan nan duk ƙannin sa suka yi aure na cikin gidan su, illa mutum ɗaya ce wacce yanzu tana gida bata yi aure ba, ban san kuma meyasa ba”.

Murmushi Safra tayi tace, “tabbas ina ji a jiki na, ita ce za’a haɗa su aure, sai dai baza mu fara aiki a kan hakan ba, har sai mun tabbatar da maganar Malam, kar ki damu idan sun san wata basu san wata ba, tunda Malam ya gaza wannan aiki, uhmmm makircin mu shi ne zai yi aiki a nan”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button