FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

“Ba shi nake nufi ba, taya zaki aure sa idan baki aikata abinda nace miki ba? Bari kiji; yarinyan dake tare dashi tamkar wata garkuwar shi ce, akwai bala’o’i da yawa da ake jifan sa dashi, amma kuma albarkacin ta yana zuwan masa da sauƙi, ya rage naki ki je duk wajen wanda zaki je ya kusance ki baya ga shi”.

Zata sake magana Safra ta katse ta da faɗin, “to babu damuwa Malam, insha Allahu zaka ji mu ako yaushe, yanzu ba ya gari, za mu ɗau lokaci kafin mu sake dawo wa”.

Gyaɗa kansa kawai yayi yaci gaba da surƙullen sa

Sai Safran ta kalli Ayush ta raɗa mata “ta fito da kuɗin a ba shi”.

Babu musu ta zuge jakan ta ta fito da kuɗin ciki gaba ɗaya, dubu ɗari biyu ne, ta ajiye masa

“Ranka ya daɗe! Ga kuɗin, muna godiya sosai”.

Ɗago kai yayi ya kalli kuɗin, sai kuma ya kalle su yace, “za ku iya tafiya. Fatan Nasara”.

Tashi suka yi suka fice, inda babu me magana har sanda motan su ta fito daga hanyar ƙauyen suka hau titi

“Yanzu Ni ya zan yi? Kai na ya ƙulle Wlh, ta ya zan aikata Zina abun da ban taɓa yi ba? Sannan kuma taya zan je gidan sa ba da budurci na ba?”

Dariya kawai Safra tayi, sai dai bata ce komi ba taci gaba da tuƙin ta

Hakan yasa Ayush ta sake kallon ta tace, “kin yi shiru? Don Allah ki bani shawara, ga kuma wani babban aikin; wai tsigo gashin kansa, mutumin da ba shi a ƙasa, ko yana nan ma ta ya zan tsigo gashin sa?”.

A wannan karon ma dariyan Safra ta sake kwashe wa dashi, sai kuma tace, “ashe har yanzu baki waye ba? Wlh duk ɗauka na ke fa bugaggiyar wayayyiyar nan ce”.

Sake juyo da kanta sosai Ayush tayi tana kallon ta, sai dai ta kasa cewa komi

“Ke yanzu don kawai yace miki ki je ki kusanci wani shi ne ya zama abun tashin hankali? Ina ga fa ba abun ɗaga hankali bane, kuma gashin kansa duk yanda za’a yi mu samo ai dole ne zamu samo, sai dai dole sai mun bari ya dawo nan, sabida ko mun je can bamu da dabaran da za mu iya aiwatar wa bare mu samu, amma anan akwai hanyoyi da dama, kar ki damu ƙawalli zan taimaka miki har sai burin ki ya cika, tunda jini na ya haɗu dake Wlh ko me kike so zan taimaka miki, ki share batun nan, duk sanda aiki ya tashi da zaran ya shigo gari zan haɗa ki da alhazawan da sai kin jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, domin sai wanda ranki ya kwanta dashi zaki darza, sannan kuma uhmmm kuɗin da zaki samu ko? Hhhhh ba’a magana, Allah lokaci ɗaya zaki faso gari, daga ranan ma kin samu sana’ar yi, ke da kanki zaki koma neman su, ga ki kina auren The Young handsome Guy, ga kuma kuɗi ya zauna miki, kin zama Hajiyan kan ki, Allah zaki ce na faɗa miki”.

Shiru Ayush tayi a wannan lokacin ma, sai dai tana kallon Safran, tambayar dake yawo a ranta “ita meyasa bata nemi mazan ba sai ita zata haɗa ta da su?” In fact ma ta sha jin tana cewa “Maza ba sa burge ta” sannan ma bata taɓa jin tayi maganar namiji ba in ba yanzu ba, ashe tana da alaƙa da su? Duk da tasan Safra ƴar gata ce tana wadaƙa da kuɗi, amma bata san muhallin da zata ajiye ta ba, iyayen ta ne masu kuɗin? Ko kuma samari take bi suke ba ta? Shi ne bata sani ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56

Leave a Reply

Back to top button