FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

“Baba wlh abun Usman sake gaba yake yi ba baya ba, kamar shi har sai an zauna ana faɗa mishi dai-dai da wanda ba dai-dai ba? Nan ya bar mu muna zaman jiran sa tsawon lokaci, duk sabida shi aka ƙi cewa komi, amma kuma ya zo yana wani sabga daban bayan yasan da cewa magana me muhimmanci ne ya tara mu”.

“Well enough to stop talking, ban san ka da wannan halin ba Noor Kar ka soma ka ji ko?” Kaka ya sake faɗa idanun sa kan Big Dady

Gyaɗa kansa yayi, kana yace, “to Baba Allah ya huci zuciyar ka”.

Murmushi Kaka yayi, yayinda su Abba da Abbu suka amsa da “Ameen, sai haƙuri ai”.

Kaka ya ce, “to ina jin ku, ya muka kwana a maganar yaran nan ne? tunda yau dama na ce zamu sake zama akan maganar”.

Abba ne ya ce, “ai Baba duk na tambaye su kuma na ce su turo mun su, kuma sun zo mun yi musu tambayoyi da Yaya (Yana nufin Big Dady) sannan na bincika duk na gano inda yaran suke, har na saka ayi min bincike a kansu. Uwata kuma da Usman har yanzu ba su ce komi ba akan maganar, shi kuma Baffa ɗazu Mahaifiyar tashi take faɗa min Sa’adatu ta wurin ƙanwar ta Hajiya Amina yake so”.

Kaka yace, “to Masha Allah Baba na”. Sai ya mayar da kallon sa ga Ɗahira da ke gefen sa ya ce, “Matata har yanzu abokin takaran nawa be shirya bane da baki gabatar da shi wajen Iyayen naki ba?”

Shiru Ɗahira tayi kanta a ƙasa

Sai da Big Dady yace, “Daughter you’re talking, are you okay? No problem?”

Bata ɗago kai ba tace, “Daddy, I don’t have anyone to introduce me to.”

“Baki da wanda zaki gabatar kuma?” Cewar Big Dady da Abba da suka haɗa maganar a tare

Sai kuma Big Dady ya ƙara da faɗin, “ko dai kin tsaya ruwan ido my Daughter? Amma maganar babu wanda zaki gabatar ai be taso ba”.

Jikin ta a sanyaye tace ,”Daddy wlh da gaske nake yi, wanda muke soyyayya da shi ya ce “ya fasa aure na, sabida Mahaifiyar sa ta zaɓa mishi wacce zai aura”.

Daga Aunty Amarya har Abbu da su Big Dady sai da jikin su yayi sanyi, haka zalika Kaka da yayi zugum yana kallon ta ya kasa furta komi

“Yanzu Uwata babu kuma wanda zaki iya gabatar wa ne?” Cewar Abba da yayi maganar a sanyaye

Gyaɗa kanta tayi, don haka kawai taji hawaye ya cika mata ido, a ganin ta abun da kunya a tara su a gaban jama’an gidan ace ta kawo zaɓin ta, amma kuma bata da shi, babu wanda zata iya nuna wa a matsayin gwanin ta, kamar ta ƙatuwar budurwa da ita, a ƙalla yanzu kaɗan ya rage ta cika 26 cif-cif…

Muryan Kaka ya katse mata tunanin ta, sai ta saka hannu tana share hawayen da ya zubo mata tana ci gaba da sauraron shi

Tambayan Usman yayi kamar yanda yayi mata

Usman ɗago kai yayi yana kallon kakan, fuska babu walwala a daƙile ya ce, “Babu”.

“Meye kuma Babu?” Abba ya tambaye sa

“I mean har yanzu babu wacce nake so”.

Shiru gaba ɗaya parlour’n ya ɗauka, ana jiran aji wani yayi magana a kan hakan, amma babu wanda ya iya cewa komi, har Kaka kuwa, kowa juya maganar nasa yake yi a mizanin hankalin sa

Kaka kallon Abbu yayi ya ce, “Takwara kun yi maganar da Yayar taku?” (Hajiya Ikram, Yana nufin akan Khabeer da ke son Fadila)

“Eh Baba, Yaya yayi maganar da ita”.

Big Dady yace, “mun yi maganar, har mun tattauna da mijin ta, babu matsala tunda su ma a shirye suke, za’a haɗa gaba ɗaya dana Isma’il da Shamsiyya”. (Sauran yaran Hajiya Ikram, su uku kenan zata aurar itama, har da K.B)

Gyaɗa kansa Kaka yayi yace, “Masha Allah gaskiya nayi farin ciki matuƙa, Allah ya sanya albarka gaba ɗaya”.

“Ameen ameen”. Suka amsa gaba ɗaya

“Yanzu duk abinda kuka ga ya dace sai ayi, kun san dai idan za’a saka ranan nace muku kar ya wuce wata ɗaya? Sai ayi komi a tsanake zuwa watanni biyu, na ƙara lokaci, a lokacin idan Fodio da Matata sun kawo nasu sai a haɗa baki ɗaya, don baza ayi babu su ba. Kai kuma Fodio kayi ƙoƙarin samo mata tun kafin Ni in zaɓa maka kana ji ko?” Kaka yayi maganar ta sigan barkwanci

Be ce komi ba kamar yanda kuwa babu wanda yayi tunanin zai ce.

 Daga nan dai aka bar zancen aka kama wani, inda waɗanda suke da abun yi suka bar wajen.


Ɗahira bata wani tada hankalin ta ba akan maganar, ta bar wa Allah zaɓi, a ganin ta idan ta saka damuwa kanta zata cuta, tunda dama bata iya saka damuwa a ranta ba, da zaran ta saka, to shikenan ta dinga ciwo kenan, duk idan ka ga tana ciwo to tabbas da akwai abinda ke damun ta ne, ba ta iya jure wa damuwa ko kaɗan a ranta, bata da dauriyan hakan, domin zuciyar ta ba ta iya ɗauka, shiyasa ba ta shiga sabgar kowa idan har be shafe ta ba, sabida ta san matsalar kanta.


  Aunty Amarya har ɗaki ta kira ta, tayi mata nasiha akan hakan

Amma sai Ɗahira ta nuna mata babu komi, har da fara’an ta

Hakan ya kwantar wa da Aunty Amarya hankali matuƙa, ko babu komi taji daɗi a yanzu, tunda ta san dole ɗiyar ta zata shiga wani hali na rashin masoyi, tabbas rashin Masoyi abu ne me ciwo ga duk macen da ta isa aure amma babu ma nemi, sai dai Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi.

      ⚫⚫⚫


 Fannin Usman ma, da dare Daddy ya Kira sa ya titsiye sa akan maganar, a cewar sa "ai wannan shirmen banza ne, shirmen hofi. Ta ya zai ce be da wacce yake so duk girman sa, shekara kusan 33 yana musu wasa da hankali". Tsiya-tsiya sosai Big Dady yayi masa, kuma ya ba shi umarnin "lallai-lallai ya kawo mata zuwa nan da lokacin da Kaka ya ce, idan ba haka ba, zai ɗau mummunan mataki a kansa"

Hajiya na zaune tana jin su, sai dai bata ce komi ba, tunda itama ai tana ƙaunar ganin ɗan nata yayi aure, shi ne babban ɗa a gidan, amma har yanzu be yi aure ba, duk da a ganin ta ai ba wani shekaru ne masu yawa da shi ba, amma ta yanda za’a ganshi da girma, ƙannin sa su ƙara ganin girman sa, ai sai idan yana da mata, itama zata so ta ga jikokin ta ta wajen shi, ai abun kunya ne ma ace yanzu Yusra zata yi aure shi be yi ba, sannan ga ɗaya ƙanwar sa can a ɗakin miji har da ɗan ta, shi ƙaton banza ya zauna.

 Shi kuwa Usman ko a jikin sa, tunda a ganin sa dai babu wanda ya isa yayi masa auren dole, don haka be tashi yin aure ba yanzu sai sanda yayi niyya, duk a cikin mata har yanzu be ga wacce tayi dai-dai da ra'ayin sa ba, yana da burin ra'ayin auren mace zaɓin shi da koda yaushe zuciyar sa take raya masa, kuma har yanzu be dace da kalan ta ba, don haka sai sanda ya same ta sannan ne zai yi aure, mata yanzu ba sa gaban sa, shiyasa ya ɗauki maganar Kaka ba ta da wata muhimmanci, bare shi rayuwan boko ya saka wa kansa, har yanzu gani yake yi be kai matakin da har zai iya ajiye mata ba, ɗawainiya ya hau kansa tun da ƙuruciyar sa ya tsufa da wuri.







        ⚫⚫⚫


 Baffa kuwa sosai ya shiga damuwa a wannan ranan, har kuka sai da ya sha ya ƙoshi, ya kuma gode wa Allah, ga shi yana ji yana gani zai bar zaɓin shi babu yanda ya iya, yana kallon wacce yake ƙauna bata da wanda zata iya gabatar wa face shi, amma kuma Mahaifiyar shi tayi masa iyaka da ita.


  Ya tuna sanda ya je har ɗakin ta yana kuka ya sake mata maganar "ta amince ya auri Ɗahira, in yaso duk wacce take so ya aura, shi wlh zai aure ta, koda kuwa mata huɗu zata haɗa masa, idan har da Ɗahira to ya amince".

Amma sai buɗan bakin Hajja tace, “kai Al’ameen ka ji Ni da kyau, Ni Ɗahiran ce ba na so ka aura, bazan taɓa haɗa tsatso da A’ishah ba, domin kuwa na tsane ta a raina, ban taɓa faɗa maka hakan ba, amma yanzu sabida maganar nan ka saka ina bayyana maka sirrin dake raina, to wlh idan har ka kuma sake tayar da maganar nan ma, ban yafe maka ba”.

Kuka sosai Baffa ya fashe da shi, be iya furta komi ba sabida tsaban tashin hankali, wai yau Mahaifiyar sa ce take furta masa kalmar nan duk a sabida wani dalili nata mara tushe, ko a mafarki be taɓa tunanin akwai abinda zai iya bayyana wa mahaifiyar sa yana so ba, ta kasa mishi, sabida ya san tana ƙaunar sa, duk abinda yake so to itama tana so, hakan be taɓa faruwa ba, shiyasa yake ganin abun tamkar almara. ranan ya sha kuka kamar babu gobe, har zazzaɓi ya kwana da shi a ranan. Allah ya ɗaura masa ƙaunar Ɗahira kamar ransa, amma ga shi a lokaci ɗaya ya rasa ta, abinda be taɓa tunani ba ko da a mafarki, ya rigada ya saka wa ransa ita ɗin tashi ce, tunda be taɓa tunanin akwai wata matsalar da zai shiga tsakani ba, ko da ma akwai, to, sai dai a wajen Ɗahira, ita ma kuma be taɓa tunanin zata iya cewa ba ta son sa ba, tunda ya san girman son da take mishi, ya san Ɗahira a kansa zata iya yin komi sabida farin cikin sa, shaƙuwar su ya wuce misali, babu ɓoye-ɓoye a tsakanin su.
[6/5, 7:39 PM] Oummu Ɗahirah: ????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL.

بسم الله الرحمن الرحيم


???????????????????????? ????????????????????????’???? ????????????????????*
®Ɗ???????????? ???????????????????????? ???????? ????????????????????✓

???????????????????? ???????????????????????? ????????✍️

????????????????????????????: ????????????????????????????????????????????????

     \????.????.????????/

????????????????????????????????????????
???????? ???????????????????????????????? ???????? ???????????????????????? ???????? ???????????????? ɗ????????????. ????????????????’???? ????????????????????????.

    *EPISODE Twenty Seven*


  "Dakata da Allah Ayush! Wani taimako kike so in miki ban da wanda nayi miki? Kin tambaye Ni Numban sa na baki wannan kuma ya rage naki, in yaso ki je ki same shi da soyayyar ki, in kuma kin kasa Wannan kuma damuwar ki ne, amma kar ki ƙara zuwa min da banzan maganar nan taki akan Ni ce zan sanar mishi, ina ruwana a ciki?" Shakira take maganar cikin fusata

Ayush dake zaune a gaban table ɗin ta, idanun ta sun cika da ƙwalla, hannu ta saka ta share tana kallon ta tace, “fine naji, sabida na gama miki amfani shiyasa kike son watsa min ƙasa a ido, don kawai na nemi taimakon ki akan nawa soyayyar? Babu damuwa”. Ta ƙarishe maganar tana miƙe wa zata bar Office ɗin

Da tsaki Shakira ta raka ta, bata ce komi ba ta mayar da hankalin ta kan wayan ta, sai yanzu ma take dana sanin amince wa tayi ƙawance da local irin wannan, don da farko a tunanin ta ƴar masu kuɗi ne irin su, shiyasa tayi saurin amince mata, amma yanzu gaba ɗaya dana-sanin yin ƙawance take yi da ita, ta bar ta ne kawai saboda tana mata aiki a kan Baffa da Ɗahira, amma kuma yanzu tunda komi ya ƙare a tsakanin su baza ta iya juran raini wajen ta ba…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button