FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

.

plz I don’t get a lot of comments, if you don’t like it please tell me in Dena, don ba nan kaɗai nake yi ba, can da suka fi buƙata sai in riƙa musu su kaɗai, ta comments ɗin ku kawai zan san kuna so aci gaba.

kar ku manta Vote and share.
[5/29, 7:11 AM] Oummu Ɗahirah: ????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL.

بسم الله الرحمن الرحيم


???????????????????????? ????????????????????????’???? ????????????????????*
®Ɗ???????????? ???????????????????????? ???????? ????????????????????✓

???????????????????? ???????????????????????? ????????✍️

????????????????????????????: ????????????????????????????????????????????????

     \????.????.????????/

????????????????????????????????????????
???????? ???????????????????????????????? ???????? ???????????????????????? ???????? ???????????????? ɗ????????????. ????????????????’???? ????????????????????????.

    *EPISODE Twenty*


  Da sannu rayuwa taci gaba da gudana, zuwa wannan lokacin Familyn Dr. Al'ameen suna ta shirye-shiryen zuwa Kano ne Bikin Salma (Ƴar Hajiya Laila), yanzu haka saura wata ɗaya

Kaka da kansa ya ba da odan kaya ya raba musu, wai wanda zasu ci biki dashi, matan kaɗai, daga iyaye har ƴan matan, har da su Aunty Zainab da Aunty Zulaiha sai da ya saka aka aika musu dashi, kala bibbiyu ne atamfa da Swiss less, kuɗin su kuwa zai kai dubu ɗari ko wanne, daga gani kasan kayan masu uban tsada ne, sun yi murna matuƙa, nan da nan kowa yakai ɗinki inda zai iya kai wa

Kafin ranan bikin kuwa tuni an amso musu, ranan Alhamis ƴan matan suka shirya tafiya, matan gidan kuma sai gobe juma’a za su taho, su kuma su Big Dady ranan ɗaurin auren asabar za su je, gaba ɗaya har dasu Usman, sannan kuma su dawo a ranan.

   Tun 11:00am. Suka gama shirin su, ko wacce da jakan ta a hannu, har haraban gidan iyayen su mata suka rako su

Drever ya amsa jakunan nasu ya saka a bayan mota

Yusra ce ta shiga gaba, su kuma su uku a baya, drever’n yaja motan suka ɗau hanya cike da ɗoki

To dama ba wai sun saba zuwa sosai bane, kasancewar Boarding school suka yi a A.B.U Zaria, shiyasa ba su da lokacin kansu bare su riƙa ziyarce-ziyarcen ƴan uwa, kuma suna gamawa suka soma aiki, wannan dalilin ne yasa sun daɗe rabon da su je Kano, gwara-gwara ma Katsina, hutun ƙarshe da suka samu kafin su gama school a can suka yi, sai kuma suka ƙarisa sauran a Maiduguri, Kano ne dai sun shafe kusan shekaru biyar rabon da su je.

     Zuwa ƙarfe 02:00pm. Tayi musu a Kano, Direct family house ɗin *General Isah Basheer Isah (Walid)* suka nufa, wanda a yanzu ake kiran sa da Granny

Gate aka wangale musu drever yaja motan zuwa ciki, be tsaya ba sai a ɓangaren su Salma, kasancewar gidan babba ne me Part-part, da ƴaƴan sa guda hudu maza da jikokin sa waɗanda suka yi aure su wajen uku duk a cikin gidan suke da zama, kuma kowa da na shi Part ɗin, sai na Granny ɗin da matar sa da suke ce mata INNA Haja.

 Tun kafin ma su fito daga motan su Salma suka fito tarban su, dayake sun san da zuwan su, ƴan mata ne kusan su goma kuma duk jikokin Granny ne, a ciki har da ƴaƴan yaran sa mata da sukai aure a wani wajen

Sai kuma Shamsiyya da itama tazo tun jiya

Nan da nan suka karaɗe ɓangaren da murna da ihun ganin juna, daga baya kuma suka ɗunguma zuwa ciki

Hajiya Laila na zaune a parlour’n ta tana jiran isowar su, ganin su yasa ta washe bakin ta kafin ta fara musu maraba

Gaba ɗaya wajen ta suka isa suna gaishe ta cike da tsananin farin ciki a fuskokin su

Bayan sun gama gaishe-gaishen ne ta tashi taba su waje, nan kuwa suka ƙara ɓarke wa da Surutu ana hiran yaushe gamo, Sarkin surutu Firdausi tuni ta soma zuba ko haɗiye miyau ba tayi, tana ɗire aya take ɗaukan wani

Yau har da Fadila ba’a bar ta a baya ba, domin tayi zaman ta cikin ƴan uwa ana ta hiran da ita

Sai daga baya ne ma da Hajiya Lailan ta fito, take musu tsiya “ko abinci basu ci ba sun zauna suna ta zuba zance”

Salma ita da su Shamsiyya suka tashi suka haɗo musu abincin, duk sun baje a parlour’n suna ci suna ci gaba da hiran su cike da nishaɗi.

  Ƴaƴan Hajiya Lailan ne guda biyu maza, Bashir (Abba) da kuma Yaseer suka shigo cikin parlour'n, yanzu haka ko wannen su da iyalan sa, shi Abban ne babban jikan gidan

Gaishe su suka yi cikin girmamawa, su ma suka amsa cike da fara’a da nuna farin cikin su na ganin su, har da tambayan su Baffa da Usman tare da sauran ƴan gida, duk suka amsa musu da “lafiya lau sun ce a gaishe su,” daga nan suka wuce ɗakin Mahaifiyar su suka bar su nan suna ci gaba da hiran su

Ɗahira ce ta kalli Fardausi da ta cika su da Surutu, don ita ce ma ƙarfin hiran, cikin tsokana take ce mata, “Ni wlh da an haɗa ku gaba ɗaya Dady ya aurar daku, ko gidan ma sun huta da surutun ki, yarinya ko haɗiye yawu ba ta yi”.

Dariya gaba ɗaya aka kwashe dashi

Ita kuma Firdausin gyara zaman ta tayi har da karkace ɗankwalin kanta tana faɗin, “me kuke ci na baka na zuba? Ai wlh marriage is time and I’m here to do, amma wlh bazan yarda a haɗa Ni da Salma ba, dole sai na zauna nima na taɓa ƴan matanci na Ni kaɗai, haka kawai ai bazai yiwu ba”.

Hararan ta Salma tayi tace, “dalla yi mana shiru, Ni wlh ban san ma meyasa Dady ya ƙi tilasta miki fiddo da mijin ba, uwar ma me zaki sauna yi musu bayan ba kya cas ba kya as”.

Itama dai Firdausin hararan nata tayi tace, “eh naji dai, baza ai mana auren tare ba ƴar baƙin ciki, wlh nima yanda kika fara aiki kafin kiyi aure, nima bazan yi ba sai na soma aiki na”.

Tsaki kawai Salma taja tana sake kwaɗa mata harara

Firdausin ramawa ta kuma yi, har da murguɗa baki

Dama sun saba kasancewar saƙo da saƙo suke, bare kuma dama Salma tana jin haushi an ce ta fito da miji a haɗa da na sauran yayyin su biyu maza da za ayi musu aure, ita kuma Firdausi da sauran ƴan matan ba’a ce musu ba, hakan yasa take jin haushi tunda ba’a haɗa su gaba ɗaya ba

Su dai sauran sai dariya suke musu, basu tashi ba sai da aka kira sallan la’asar, sai ma lokacin ne su Ɗahiran suka tuna basu yi azahar ba, ganin ƴan uwa da hira ya shagaltar dasu

Ɗakin su Salma suka wuce, wasu daga cikin su kuma suka koma nasu Part ɗin, sallan suka gabatar kafin Ɗahira ta miƙe tana kallon Firdausi dake zaune kan sallaya, tana latsa wayan ta da aka kira time ɗin tana sallah

“Fido tashi ki raka Ni mukai gaisuwa wajen Granny da ƴar tsohuwar matar sa, tun kafin ma ya aiko”.

Ɗago kai Firdausi tayi tana dariya tace, “wlh nima dai naga haƙurin sa da be aiko a kira ki ba”.

“Ko dai be san ta zo bane?” Cewar Haneefa dake zaune itama kan dadduman

“He knows, tunda Ni naje na shafa masa labari har ɗakin sa yau za su zo”.

Ɗahira ta murmusa tana faɗin, “Let’s go. Please, I’m too tired to see him, because I’m missing him.”

Salma tace, “oh wa yaga Ɗahira matar tsofaffi, Ni na kula ma tsofaffin nan duk sun fi son ki, Anya ba da ɗaya za ayi ba between Kaka and Granny?”

Dariya suka kwashe dashi sauran cike da shaƙiyanci.

  Fadila da Shakira ma duk tashi suka yi suka bi bayan su Ɗahira don su gaida Granny ɗin, a Parlour suka tarar da Yusra dake zaune ita da Hajiya Laila, nan suka yi mata bayanin "za su je gaishe da Granny ne daga nan su je sauran ɓangaren su gaishe su," har da Yusran suka tarkata  suka tafi.


 Part ɗin Granny suka soma zuwa, lokacin Inna Haja na sallah a ɗakin ta

Koda suka leƙa suka ga tana sallah ne sai suka nufi ɗakin Granny, yana zaune kuwa yana duba ƙur’ani, shima idar da sallan sa kenan, dayake ba ya iya fita sabida ciwon ƙafa da yake fama dashi, duk da ba’a Wheel chair yake zaune ba, kuma yana iya tafiya amma ba me nisa ba

General Isah Basheer Isah (Walid) kenan, tsoho me ran ƙarfe, kai da gani kasan an zuba ƙaƙƙarfan jarumi sanda yake matashi, har yanzu kuma idan ka kalle sa zaka ga zubin jarumtar sa, don daga gani kasan da sauran ƙarfin sa sosai, sai dai kawai tsufa ne da yayi, ga furfura da duk ya cika masa kai, kasancewar sa ba me barin gemu ba shiyasa babu komi a wajen sai ƙananun gashi farare kaɗan-kaɗan.

  Shigowar su yasaka ya ajiye ƙur'anin yana ɗago kansa tare da cire medical Glass ɗin sa, fuskar sa yalwace da murmushi yake amsa gaisuwar da suke masa tare da bin su ɗaya bayan ɗaya yana kallo

Cikin tsokana Firdausi tace, “wai kuwa ka gane su Granny? Ko sai na maka bayani tunda naga idanun naka sun tsufa da yawa?”

Dariya yayi kafin yace, “ke kam baki da kirki Nana Firdausi, yo idan har bazan gane su ba kema ai bazan iya gane ki ba”.

Gaba ɗaya fashe wa da dariya suka yi, ban da Firdausi da ta kwaɓe fuska tana ma Granny shagwaɓa.

     Nan ya soma tsokanar su Ɗahira bayan ya tambaye su mutanen gida, suka zauna suka biye masa suna ta kwasan dariya

Itama Inna Haja da ta idar da sallan, ɗakin ta shigo ta zauna ana yi da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button