FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

             ⚫⚫⚫

          Direct Hajja part ɗin Hajiya ta wuce, can kuwa ta gan su zaune da Yusra ran su duk a ɓace, musamman ma Yusra da take ta zagin Ɗahiran, tana aibata ta, sannan a cewar ta, “sam bazai yiwu Ɗahira ta auri Yayan ta ba, duk hanyar da zata bi sai tabi don ganin ta hana wannan auren”.

         Shigowar Hajja a dai-dai lokacin ne Aunty Zainab ta fito daga ɗakin Hajiya take ce mata, “ke wace iriyan sakarya ce? Do you know what you are saying? Ɗahiran ƴar uwan ki kike aibata ta? Wai shin Yusra me ta tare miki ne da kike tsanar ta?”

Turo baki Yusra tayi tace, “wlh Aunty baki san halin wannan munafukar bane, sam na tsane ta sabida ko kaɗan ba ta da hali me kyau..”

“Will you shut up your mouth?” Aunty Zainab ta daka mata tsawa

Hajja tace, “to ai gaskiyar ta ta faɗa, shin ke baki san kitumurmuran da A’isha da ɗiyar ta suke ƙulla wa ɗan uwan ku bane? Wlh muddin kuka sake ya aure ta tabbas sai A’isha ta shanye shi”.

“Haba Hajja wai don Allah me bayin Allan nan suka tare muku ne duk kuka bi kuka tsane su?What is wrong with this marriage? Ke kanki kin san Aunty Amarya ba mayya bace bare ta shanye shi, kawai kin ɗaura mata karan tsana kuna ta aibata su”.

Wannan karon Hajiya ce tayi magana da cewa, “Zainab, shut up before I hurt you. Shashashan Yarinya ana faɗa miki Gaskiya kina kare su, to Ni sam ko da babu abinda za su yi masa, ban amince da wannan auren ba, sabida ba na son shi da ita”.

Kallon mahaifiyar nata kawai Aunty Zainab take yi, sosai ranta ya ɓaci da irin wannan abubuwan da take ji yau a gidan su, “wannan wani irin tsana ce? Mene ne aibun su da ake ganin laifin su? Kai sam bazai yiwu ba, baza ta zira ido ta ga gidan su na ƙoƙarin rabewan kai ba, dole ne ta sanar da Dady”. Juyawa tayi ta shige ɗakin Hajiyan, ta sumfuci Jinior dake barci ta goya shi, ta ɗauki gyalen ta da jakan ta ta fito, bata bi ta kansu ba ta wuce ta bar gidan.

        Ita kuwa Hajja zama tayi tana ta ƙara ingiza Hajiya a kan “lallai-lallai kar ta yarda da wannan auren, kar ta soma ayi wa ɗan ta auren dole tunda shima ba ya so”.

Nan ake yin ta fa.. chakwakiya.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

           Shi kuwa Usman tsaban ɓacin rai da jin maganar nan, yana fita daga General parlor barin gidan yayi, tuƙi kawai yake yi ya rasa ina zai je sai faman huci yake yi, yayi tafiya me nisa kafin ya tsaya yana gangarawa gefen titi, a zuciye ya buga sitiyarin motan yana cewa, “impossible.. I will never marry this girl, I hate her! I hate her so Much! zan iya kashe ta ma idan har na ganta a gida na”.

Gaba ɗaya idanun sa sun kaɗa sun yi jazur, tamkar zai haɗiya zuciya sabida ɓacin rai, jijiyoyin kansa sun fito raɗo-raɗo, haka ya kama gashin kansa ya matse yana me kiran sunan Kaka, sai kuma ya matse bakin sa cikin amon muryan sa yace, “wlh muddin kuka haɗa auren nan sai na kashe muku ita, gaba ɗaya sai kun yi dana-sanin haɗa Ni aure da ita”. Ya ƙare maganar da dukan sitiyarin motan da mugun ƙarfi yana ihu, sai kuma ya kifa kansa saman motan yana me sakin numfarfashi, cikin slow voice yace, “I hate her! Then I will killed her”.

.

.

Hmm akwai jan aiki fa.. kuna ganin su Kaka ba su yi ganganci ba? Wani irin hali Ɗahira zata shiga? Shin maƙiyan ta suna yin nasara kuwa?
????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

\F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

.

        EPISODE Thirty Five

         Usman be dawo gidan ba sai dare, yana shigowa parlor ya tarar da Hajiya na zaune tana tsimayen shigowar sa, domin kuwa a lokacin wajen ƙarfe 12:00pm ne na dare

Yana shigowa tayi zumbur ɗin zuwa wajen sa, cikin tashin hankali tace, “Ina ka je ne tun ɗazu ina buga wayan ka ban samu ba?”

Kallon ta kawai yake yi amma be ce komi ba, gaba ɗaya ransa a ɓace yake har yanzu, zuciyar sa gaba ɗaya ba ta masa daɗi, shiyasa ma ko kaɗan bazai iya buɗe bakin sa ba, bare yayi magana

Zata sake yin magana, sai suka ji muryan Big Dady yana cewa, “Ka dawo?”

Gaba ɗaya kallon sa suke yi kamar yanda ya kafe su da ido, yana tsaye a bakin ƙofar ɗakin sa

Shiru Usman yayi yana me kawar da kai daga kallon sa

“Dama kai nake jira, daga ke har shi a gidan nan zan yi mummunan saɓa muku, muddin kuka ce za ku ja da maganar auren nan, duk abinda kike faɗa min a kan a janye auren nan, to wlh muddin ina numfashi sai an yi sa, sakaran banza sakaran hofi, kuma wlh idan har baka dena nuna wa Daughter irin tsanar nan ba, Ni da kai ne a gidan nan, zan ga uban da tayi maka ka tsane ta”. Yana ƙare maganar ya juya ya shige ɗakin sa

Usman be bari ya ƙara Socond ɗaya ba shima ya wuce ɗakin sa da sassarfa, yana jin Hajiya na kiran sa amma ina sam ya ƙi waigo wa

Itama cikin ɓacin rai ta nufi ɗakin Dadyn, tana shiga ta tarar da shi zaune gefen gado yana shirin kwanciya, ta ƙarisa wajen sa tana cewa, “wai me kake nufi da zaka saɓa mana a kan maganar nan? Ina ce yaron nan ba ya ƙaunar yarinyan? Kowa yasan da cewa jinin su be haɗu ba a gidan nan, kuma kafi kowa sani, amma sabida tada zaune tsaye ake son tauye wa ɗana haƙƙin sa, Ni fa bazan goyi bayan gaskiya ko ƙarya ba, Ni ɗana kawai na sani, abinda yake so shi nake so, tunda ya nuna ba ya son haɗin nan, kun hana sa ya faɗi ra’ayin sa, amma ai fuskar sa ta nuna muku ba ya so, to wlh bazai yiwu ba, a kan ɗana babu abinda bazan yi ba”.

“Wato kina so ki nuna min wuyan ki ya isa yanka Asiya? Har Ni kike tsayawa a gaba na a kan wannan maganar kike son gaya min magana ko? To kar ki fasa, ki je kiyi duk abinda za ki yi, amma aure ne babu fashi, tunda kuka nuna ba ku son auren nan, to yanzu ne na ɗau ɗammaran sai ya aure ta, wlh bari kiji ko bayan raina bazan taɓa yafe wa ba muddin Usman be auri Ɗahira ba, idan kin ga ba’a yi ba kuwa, to ɗayan biyu ne, ko Allah ne be yi nufin matar sa ba ce, ko kuma Baba ne ya hana, shi ne kawai zan iya bin umarnin sa a duniyar nan, kuma ki ɓace ki bani wuri kar ki sake tanka wa tun kafin raina ya ɓaci”.

Dole Hajiya ba don ta so ba ta juya ta wuce ɗakin ta, amma a ranta ta ɗau alwashin muddin ɗanta ba ya son auren nan, to itama baza ta taɓa son Ɗahira ba, sai ta muzguna wa rayuwan ta.

                   ⚫⚫⚫

       A wannan dare a cikin Usman da Ɗahira babu wanda yayi barcin farin ciki, zan iya cewa gaba ɗayan su a zaune suka kwana.

          Washe gari ma Ɗahira da zazzafan zazzaɓi ta tashi, sosai hankalin Aunty Amarya ya tashi, gani take yi wani abu zai sami ɗiyar ta, tunda ta san halin ta, abu kaɗan ke ɗaga mata hankali ya fitar da ita cikin kamannin ta. Tasa Abbu tayi gaba tana kuka a kan “ya taimaka a warware auren nan, tunda dai Ɗahira ba ta so, be kamata su yi wa ɗiyar su auren dole ba”. Gaba ɗaya tarikice wa Abbu ya rasa yanda zai yi da ita, dole ya fito ya barta cikin ɗakin ya nufi ɗakin Ɗahira

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button