FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

         \????.????.????????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

TARIHIN FARILTA SALLAH
”’An farilta sallolin nan biyar ne gabanin ƙaura, watau hijira, da shekara ɗaya da rabi. Sallah ce kaɗai ibadar da aka farilta ta a sama a daren Isra’e, kamar dai yadda aka ruwaito a hadisin nan na Anas. Da farko an umurce shi da Sallah guda hamsin ne; da sannu aka dinga rage su har suka zama biyar a bisa roƙon da shi Manzon ya yi wa Ubangijin sa. Da suka zama biyar, sai Allah ya ce masa su biyar ɗin nan, dai-dai suke da hamsin.
Malamai da yawa sun yi bayanin yadda sallar ma’aikin Allah, mai tsira da aminci, take gabanin Isra’en.
Wasu malaman sun ce, “Gabanin Isra’e, babu wata sallah wadda aka farilta sai sallar dare (Ƙiyamul lail) wadda aka umurci ma’aiki da yin ta ba da iyakataccen lokaci ko adadi ba, kamar yadda yake a suratul Muzzammil, ayoyi huɗu na farko:
“Ya wanda ya lulluɓe! Ka tsayu domin yin Sallah a cikin dare (duka) face kaɗan, rabin sa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi, ko ka ƙara kansa…
Ma’aikin Allah ya kasance yana yin sallar a kashi biyu cikin uku na dare ko a rabin sa ko kuma sulusin sa. Musulmi suka dinga yi tare da shi kamar shekara guda har suka gaji; daga nan sai Allah ya shafe ta don jin ƙan su.
An ruwaito cewa sallar da Musulmi suke yi gabanin tafiyar dare suna yin ta ne kafin faɗuwar rana da kafin ketowarta kamar yadda yake a sallah littafin Almanhalil Azb. Gabanin ƙaurar Annabi zuwa Madina raka’o’in sallah bibbiyu ne, bayan ƙaura ne suka zama hurhuɗu, illa magriba da ta kasance raka’a uku, ita kuma sallar subahi ta tsaya a kan biyu saboda dogon karatun da ake yi cikin ta. Buhari da Ahmad sun ruwaito daga Nana A’ishah cewa, “an farilta sallah raka’a bibbiyu, bayan ƙaura ne aka mai da ita raka’a hurhuɗu, amma an bar sallar tafiya a kan raka’a ne bibbiyu, sai sallar magriba ita ko da ma raka’a uku-uku ce.”
Allah ya sa mu dace.”’

.

        EPISODE Thirty One

        Tunda Sa’adatu ta shiga parlour’n Hajja, ta tarar da ita zaune, sai ta ƙara volume ɗin kukan ta tana nufan kujera kusa da ita ta zauna

Kankace me Hankalin Hajja ya tashi, nan ta soma tambayan ta ba’asin kukan nata

Sa’adatu ta sanar mata da abinda ke faruwa, daga zuwa gaishe da Ɗahira Da Baffa ya matsa mata tayi, har maganganun da ya faɗa yanzu

“Lallai kam Baffa yana son Wasa Dani a gidan nan, amma bari miƙo min waya ta in Kira sa”.

Tashi Sa’adatu tayi ta miƙo mata wayan daga kan Centre table, ta ba ta

Kiran sa tayi ta ba shi umarnin zuwa yanzu

Be daɗe ba kuwa sai ga shi ya shigo parlour’n da sallama

Tsaban tsiya ya ci ran Hajja, ko sallaman ma basu amsa ba, ta hau masa faɗa, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba

Ganin abun yayi yawa, sai ya ce, “Hajja wai me tace miki ne da kike min irin wannan faɗan?”

“Uwar ka tace min, nace uwar ka tace min, wallahi tallahi Baffa ka fita ido na in rufe, idan ba haka ba zan mummunan saɓa maka a gidan nan, tunda kake baka taɓa gaya min magana ba, amma a kan wancan shegiyar yarinyan naga alamu kana so ka bijire min, to wlh kar in sake ganin ka raɓe ta, idan ba haka sai na..”

“Hayaniyar mene ne haka nake ji wai?” Cewar Abba da ya fito daga daƙi daga shi sai Singlet da dogon wando, da alamu dai barci yake yi Hajja ta tashe shi da hayaniyar ta

Daga Baffa har Sa’adatu duƙar da kansu suka yi, sun kasa cewa komi, sai Hajja ne da ta cika maƙil da fushi tana shirin magana

Ya katse ta da faɗin, “ya isa, ku tashi ku tafi gidan ku”.

Tashi suka yi daga Baffan har Sa’adatu suka fice

Sannan ya juyo kan Hajjan yace, “wai ke Fatima me kike so ki zama ne? Me Baba na yayi miki da kike son hana sa kwanciyar hankali shi da matar sa? Duk abinda kike faɗa ina ji, wlh idan har baki fasa shiga sha’anin auren su ba, to watarana zaki ji kunya, kuma da kike son raba sa da ƴar uwan sa, kar in ji kar in gani, domin zan mummunan saɓa miki kema, wannan ai rashin hankali ne, tukuna ma me Uwata tayi miki ba kya ƙaunar ta?”

Shiru Hajja tayi don bata san me zata ce ba, shaf ta manta da yana ciki da tun farko bata ɗaga muryan ta yaji ta ba

Ƙwafa yayi kafin yace, “ki ci gaba kar ki fasa”. Ya juya ya shige ɗaki

Sosai ran Hajja ya ƙara ɓaci, a ranta ta ɗau alƙawarin muddin tana numfashi sai ruwan sha ya gagari A’isha da ɗiyar ta.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

       Ranan Monday Ɗahira ta koma bakin aikin ta, saboda sosai jikin ta yayi sauƙi

Shima Baffa ranan ya koma, tunda sati biyu kenan da auren su

Nan hankalin Sa’adatu ya tashi matuƙa, domin gani take yi, Baffa ya koma bakin aiki ne duk sabida ya ga Ɗahira ta koma aikin ta, kuma tasan a can dole su riƙa haɗuwa, wannan abun duk ya dame ta, taje ta sanar wa Hajja

Hajja tace, “ta bar su, zata saka musu idanu, kuma zata yi wa Baffa gargaɗi sosai” domin ita kanta Hajja yanzu ba ta ƙaunar alaƙar Baffa da Ɗahira, hanya mafi sauƙi take son samu don raba su, sam ba ta ƙaunar su ci gaba da yanda suke kamar da, tunda yanzu a ganin ta yayi aure, hakan zai cuta wa Sa’adatu.

       Baiwar Allah Ɗahira, ko kaɗan ma bata san wainar da suke toya wa ba, babu ruwan ta, abinda ta saka a gaba shi take yi, a ranan ma da ta dawo aiki ta shirya zuwa gidan su Shakira, tunda ko sau ɗaya bata je ba, da biki bata da lafiya, kuma Aunty Amarya ne ma ta matsa mata taje ɗin, kar ace tana baƙin ciki ne mutanen gida su yi wani fassara daban, shiyasa yau da wuri ta tashi a aiki, zuwa ƙarfe ɗaya da rabi ta dawo

Wanka kawai tayi ta shirya cikin farin Less me ɗige-ɗigen baƙi, riga da skert aka yi mata, wanda yayi mata cif a jikin ta, ya kuma ƙara haska mata white skin ɗin ta, sai ta yafa baƙin gyale bayan tayi ɗaurin ɗan kwalin ta normal, sai dai fuskar nan ya sha make-up, sabida Ɗahira ba baya ba wajen son gayu, musamman na kwalliya, takalmi me tudu tayi amfani da shi fari, ta ɗau HangBag ɗin ta ta rataya ta fito

Umma ce kaɗai zaune a parlour’n

Tace mata, “Umma zan je gidan su Shakira ne”.

Sai Umma ta wangale baki tace, “ahh to Masha Allah, yau kenan zaki leƙa su? To ki gaishe su”.

Murmushi Ɗahira tayi tace, “insha Allah Umma za su ji”. Tana gama faɗar haka ta shige ɗakin Maman ta

Taɓe baki Umma tayi tana kawar da kanta daga kallon bayan Ɗahiran, a ranta tace, “gulma ajali! ba ma asan me zaki je yi ba, Allah dai ya tsare min ɗiya ta ba a nan kusa take ba bare ace za’a je mata”. Sai kuma ta miƙe ta nufi cikin gidan inda zata je kai wa Hajja rahoto.

     Ɗahira na shiga tace ma Aunty Amarya “ta shirya zata tafi”.

Shi ne take tambayan ta “baza ta ci abinci bane?”

Tace mata “sai ta je can, zata ci a gidan su”.

Daga haka Allah ya kiyaye hanya Aunty Amarya tayi mata, ta bata saƙon gaisuwa, sannan ta fito. Motar ta ta hau ta bar gidan.

            Gidan Yusra ta soma zuwa, tunda babu nisa da su, babu ƙarya gidan ta ya haɗu matuƙa, babba ne sosai tunda mijin ta yana da kuɗi sosai, Costume ne shi, ya taɓa aure kuma sun rabu da matar tuni, har ɗiya yana da ita, sai dai tana wajen Mahaifiyar sa ne

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button