FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

Bayan ta gama ta dawo Office ɗin ta, cire Labcoat ɗin tayi ta rataye a Hanger kafin ta nufi cikin Toilet ta ɗauro alwala ta fito ta gabatar da sallan azahar

Bayan ta idar ta tattara komi nata ta fito ta rufe Office ɗin, ta hau lifter ya kai ta downstairs

Inda motan ta yake fake ta nufa cikin tafiyan ta kamar baza ta taka ƙasa ba, wayan ta na maƙale a kunnen ta suna waya da Baffa

Mota ta gani a bayan nata ta yanda babu yadda za’ayi ta wuce sai an ɗauke, kallon motan tayi, ta gane me shi, sai ta tsaya kawai tana waige-waige tana ci gaba da wayan ta, wajen mintuna 5 kafin su gama call ɗin ta nufi jikin motan ta tatsaya tana kallon hanya, ga rana sosai yana gasa ta

Tsaki taja tana buɗe motan ta shiga tabar ƙafafun ta a waje, shiru tayi tana jingina bayan ta a kujeran, idan zata ce ranta be ɓaci ba ƙarya tayi, tabbas Yusra ta soma shigan mata hanci da ƙudundune, me zai saka ta’ajiye mota a bayan nata tunda tasan koda yaushe zata iya fice wa? kuma ba wai babu sauran wajen parcking bane tsaban iskanci ne da neman magana

Kusan mintuna 20 da zaman ta, har ta gaji ta fito da ninyan zuwa har Office ɗin ta tayi mata magana, sai ta hango ta ta taho tana shirin buɗe motarta ta shige

Kallon ta kawai Ɗahira take yi kuma sarai tasan ta ganta, amma dayike ita ɗin ƴar wulaƙanci ne ta ɗauke kanta tana tamke fuska ta shige taja motar a guje tabar cikin asibitin

Numfashi Ɗahira ta sauke kafin itama ta shige cikin nata motan, tana ji a ranta idan har ta sake mata haka tabbas zata fuskanci fushin ta, ko kaɗan ba ta juran wulaƙanci shiyasa ba ta shiga harkan da ba nata ba

Motan taja itama ta fice cikin Hospital ɗin.

          ⚫⚫⚫



       *ONE MONTH*


       A cikin wannan watan abubuwa da dama sun faru.

Ɗahira ta dage sosai wajen aikin ta ko kaɗan ba ta wasa dashi, ta saka abun a ranta don haka sosai ta jajirce wajen taimaka wa Hospital ɗin nasu

A yanzu ta dena komawa gida har zuwa dare take kaiwa, aiki take yi tuƙuru wajen taimakon mara su lafiya

Da farko mahaifin ta yayi mata magana akan ta dena cika ma kanta aiki, tunda dama ita dutyn safe take yi zuwa rana

A cikin su huɗun ita da Shakira da Yusra dutyn safe suke yi, ita kuma Fadila na rana zuwa dare, sannan kuma akwai masu yin dare zuwa safe

Fadila fannin zuciya ne aikin ta, don haka bata cika samun patients ba a farko that’s why take komawa gida idan bata da aiki, in ta zo ta duba patients ɗin ta sai ta koma gida

Koda Abbu yayi ma Ɗahira magana a kan ta dena cika ma kanta aiki, sai tace masa “ai zata iya,” sannan tana yi ne don taimakon jama’a tunda babu abun da zata yi a gida gwara ta zauna ta taimaka

Hakan yayi musu daɗi sosai, musamman ma Kaka dasu Big dady, kullum saka mata albarka suke yi, sun tabbatar ita ɗin jajirtacciya ce aikin kawai ta saka a gaba

Yanzu ko kaɗan bata da lokacin da suke fita da Baffa sai dai jefi-jefi zai zo ya ɗauke ta su je restaurant su ci abinci

Baffa yanzu sosai suka shaƙu da Ayush don ko yaushe suna tare, a waya ne ko a gida, wasu idan suka gansu suna tunanin ko soyayya suke yi, sai dai shi kawai ya ɗauke ta a friend ne ko kaɗan ba ta ransa, Ɗahira ce har yanzu yake gani a matsayin Masoyiya

Itama ɗin Ɗahiran tana yawan ganin su da Ayush ɗin, sai dai bata taɓa mashi maganar ta ba

Yanzu masoyin ta na Ɓoye sosai kullum sai ya turo mata text ɗin nan, safe, rana da dare, idan ma be turo ba har ba ta jin daɗi, sosai yanzu take jin sa cikin ranta, kuma kullum sai tayi yunƙurin kiran layin amma a kashe, but bata taɓa tunanin itama ta tura masa text ba

Burin ta a yanzu tasan masoyin nata, sabida a yanzu zuciyar ta ta yarda dashi; soyayyar sa ne tsantsa a cikin ran ta.

_______________

      Yau ta kasance Sunday, kuma yau ne taron Familyn su kasancewar duk ƙarshen wata suna taruwa a General parlour aci abinci tare, masu matsaloli su faɗa a magance musu

Breakfast ne kawai kowa ke yi a part ɗin sa, Lunch kuma da dinner sai su haɗu aci tare, haka za su zauna ayi ta hira tunda babu me zuwa aiki a ranan

Wani lokacin ma har su Aunty Zainab suna zuwa, Aunty Zulaiha CE kawai bata cika zuwa ɗin ba sabida tana nesa sosai, amma idan ta sami lokaci tana ziyartan taron

Gaba ɗaya matan gidan suke haɗuwa ayi girki kala-kala da soye-soye, a babban kichen ɗin gidan suke haɗuwa tare da masu aiki su taya su

Yau ma hakan ta kasance duk sun haɗu suna ta girke-girke

Sauran yaran gidan kuma duk suna General parlour suna ta hiran su

Su Big Dady kuma suna ƙaramin parlour’n dake kusa da General parlour, anan suka zauna suna hira da nishaɗi

A cikin yaran in ka cire Fadila dake part ɗin su babu wanda ba shi ciki, ita dama bata cika son zuwa hiran ba, iyakan da an gama abinci zata zo taci ta tafi abun ta

Kaka shima na ɗakin sa yana karatun Jarida be fito ba, be son su ishe sa da surutu that’s why ya zauna cikin ɗakin sa

Ɗahira na zaune gefen Baffa suna hira suna kallo cikin waya sai dariya suke yi

Gefe can kuma Yusra da Shakira ne su ma suka buɗe tasu shaftan, Fadil ya zauna tsakiyan su sai zuba musu surutu yake yi, su kuma idan ya’ishe su wannan ta mangare shi ta nan, wancan ta mangaro shi ta nan, kuma yaƙi tashi a wajen shi a dole sai dasu zai yi hira

Yau dai su Aunty Zainab babu wacce tazo cikin su.

………. ………. ………. ………

      Babu jima wa aka soma shigo wa da abincin ana jera wa a dainning table ɗin cikin parlour'n dake can gefe, babba ne me cin a ƙalla mutane ashirin

Bayan an gama an hallara a lokacin ne itama Fadila ta shigo ta zauna cikin su, kowa ya zuba abinda yake so

Ɗahira kuwa tana can cikin Parlour tare da Kaka dake zaune kan Wheel chair ɗin sa, dama haka take yi idan har ba ya son zuwa kan dainning ita take zama kusa dashi tana taya sa hira, idan ta ɗibo masa abinci sai su zauna tana taya sa hira suna ci har su gama

Yau dai shima Baffa ɗauko nashi abincin yayi ya dawo kusa dasu yana ci yana saka musu baki

Haka Familyn suka kasance yau cike da nishaɗi

Bayan kowa yaci ya sha aka dawo parlour aka zauna, nan su Big Dady sukai ta tambayan matsalolin mutane, daga nan kuma Kaka ya soma yabon Ɗahira da ƙoƙarin ta kan aiki, haka su ma su Big Dady sai yaba mata suke yi suna saka mata albarka

Abbu da Aunty Amarya hakan ya saka su farin ciki matuƙa

Hajja Fatu kuwa baƙin ciki kamar ya karta, haka ma Shakira sai dai ko kaɗan basu nuna a fuska ba

Hajiya kam babu ruwan ta duk da itama ba wai yabon yayi mata daɗi bane, Umma ma dai na ciki na ciki

Fuskar Yusra kamar zai fashe saboda baƙin cikin yanda iyayen nasu suke yabon Ɗahira, ko kaɗan ta kasa ɓoye abin da ke zuciyar ta, sai cika take yi tana batse wa babu wanda ya kula da ita

Anan Big Dady yake faɗa musu Usman zai dawo gaba ɗaya gobe, iyayen sun yi farin ciki amma ban da yaran don sun san halin sa ba ya da mutunci bare ɗaukar raini, yanzu zai zo duk ya takura musu

Daga nan aka ci gaba da hira, masu abun yi sun tashi sauran kuma sun zauna

Fadila ce farkon tashi ta koma part ɗin su.

______________

   Ɗahira ce ta shigo cikin ɗakin nasu

Fadila dake waya tabi ta da kallo, sai kuma tayi dariya tana faɗin, “ga ta nan yanzu ta shigo ai”.

Cire wayan tayi a kunne tana kallon Ɗahiran da ta nufi wajen gadon ta tace, “Ga shi za ku gaisa da Yaya K.b”.

Murmushi Ɗahira tayi ta’iso wajen ta’amshi wayan tana kangawa a kunne kafin ta zauna gefen gadon Fadilan

“Yaya na”. Tafaɗa tana dariya

Shima daga can dariyan yayi yana faɗin, “ƴan mata kin ɓuya da yawa fa”.

“Haba ko dai ka ɓuya? Kaji min wannan mutumin”.

Dariya yayi sosai yana faɗin, “Allah Ni ina nan ke ce dai kika ɓuya”.

“Ai dama kai ba ka son laifin ka,
so how are you, how everyone?”

“Alhmadulillah. how about you?”

Ɗahira murmushi tayi tace, “lafiya sumul kamar yanda kuke, ina Shamsiyya?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button