FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

“Put on the Hijab and follow ME”. Abin da ya faɗa kenan ya juya ya fice

Shiru tayi tana tunani, tamkar baza ta yi abinda yace ba, sai kuma ta tashi ta buɗe wardrobe ɗin ta ta zaro dogon Hijab maroon Colour, ta saka a jikin ta ta nufi ƙofa ta fice.

     Yana zaune a Parlour, ganin ta sai ya tashi ya nufi ƙofa ya fice

Bata yi wani tunani ba tabi bayan sa, a haka suka ƙarisa cikin gidan su

Kai tsaye Part ɗin Kaka suka wuce, inda suka same sa kamar ko yaushe yana zaune a kujeran sa yana karatun jarida

Ganin su ba ƙaramin farin ciki ne ya ɗarsu a zuciyar sa ba, nan da nan ya washe baki yana musu maraba

Tuni Ɗahira ta isa wajen sa ta rungume sa, sai ta fashe da kuka tsaban farin ciki, domin ji take yi tamkar an ciro ta a kurkuku yau ta sami sake

“A’a Mata ta ya haka? Ko duk kewar nawa ne da kika yi?”

Bata yi magana ba illa ɗago kai da tayi tana kallon sa

Sai ya sakar mata murmushi yana cewa, “kin ganki kuwa? Duk kin sauya gaba ɗaya kin rame, halan ciwo kika yi?”

Usman dake tsaye bakin ƙofa kamar an dasa shi, ya harɗe ƙafafu yana kallon su, yayi saurin cewa, “to ba dole ka ganta ta rame ba tunda ta rabu da hanjin rayuwan ta, ko rashin ganin ka zai saka ta rama, ga ta nan dai ku gaisa ka ba Ni ita zamu wuce”.

Dariya Kaka yayi yace, “ban san sanda ka lalace ba Fodio”. Sai kuma ya mayar da kallon sa kan ta yace, “to mata ta Ubangiji Allah ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya, abinda zan ce kawai ki kula da kanki kinji? Kuma ki yo min tsaraba sosai kar ki ce kin manta dani”.

Kallon sa kawai take yi da mamaki, sai kuma ta buɗe baki da ninyan tambayar sa

Usman ya katse ta da faɗin, “tashi mu je, You are wasting my time”.

“Kai dai ja’irin yaro ne Usman, tafiyan da ba yanzu za ku yi ba shi ne duk kabi ka ishe ta, ka bari mana mu gaisa sosai mana”.

Shi Usman gani yake yi kamar zata iya ɓallo masa ruwa, shiyasa yayi saurin taho wa yaja hannun ta suka fice

Da sakakken baki kawai tabi sa tana kallon ikon Allah

Suna fita ya yi saurin sakin hannun ta kamar ya riƙe ƙaya, domin abinda yaji kamar ana jan sa da electronic, be kalle ta ba yace, “ki mai da hankali ki sanar da su game da zaman mu, wlh sai na ɓalla miki rayuwa biyu”.

Idon ta ta waro kawai tana kallon sa, “to wannan ko dai ya samu taɓin hankali ne?” Tafaɗa a ranta tana me sake ƙwalalo idanu waje

Kallon ta yayi ganin kamar ba ta bin shi a baya, yanda idanun sa suka shige cikin nata sai yayi azaman ɗauke kai, domin ba kaɗan ba ya tsani su haɗa ido, wani irin faɗuwar gaba ne me haɗe da tsoro yake riskan sa a koda yaushe, shiyasa ya tsane ta sosai. Daure wa kawai yayi ya dalla mata harara, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya juya yaci gaba da tafiya

Sai tabi bayan sa kawai tana kitsima abubuwa a ranta, sai kuma maganar Kaka ya dawo mata, “to ina za su je ne da Kaka yake musu addu’a?”. Babu me ba ta amsa dole taci gaba da bin bayan sa. Part ɗin su taga sun bi, sai farin ciki tsantsa ya cika ta

Suna shiga suka ci karo da Aunty Amarya zaune a parlour’n ita kaɗai, babu kowa ma sashin, tunda Abbu yana Hospital, Fadil kuma yana school, sai Kuma Umma da ta tafi anguwa

Da gudu Ɗahira ta ƙarisa wajen Maman ta tana me kiran sunan ta tare da fashe wa da kuka

“A’a mene ne haka kuma? Wannan wani irin sakarci ne?” Aunty Amarya tayi maganar tana riƙe ta

In a tears, Ɗahira she said, “I miss you Mama! Miss U so Much.”

Murmushi Aunty Amarya tayi, sai ta kalli Usman da ya samu wuri ya zauna har da harɗe ƙafafu yana latsa waya, tace, “ashe za ku yi tafiya? Ɗazu nake ji wajen Abbun su”.

Sai lokacin ya ɗago kai ya kalle ta, guntun murmushi ya saki kafin ya bata amsa a taƙaici, yana me gaishe ta

Ta amsa cikin fara’a tare da sanya musu albarka, da musu fatan alheri

Ɗahira fa kanta ya gama ƙulle wa, “da wannan mutumin ne za su yi tafiya? To zuwa ina?” Wannan tambayoyin ne bata sani ba, duk da tana son tambaya sai kuma ta fasa. Tana ɗago kai suka haɗa ido dashi, ya sakar mata wani kallo da sai da gaban ta ya faɗi, da sauri ta ɗauke kai tana mayar wa wajen Maman ta

Aunty Amarya tace, “So take care of your self? May God protect you and bring you peace.”

Daga ita har shi babu wanda ya amsa. Illa miƙe wa da yayi yace, “tashi mu je. Za mu tafi Mama”.

“To madalla, a dai ta addu’a Allah ya tsare”. Aunty Amarya tafaɗa cikin fara’a

Usman fa ya kasa ya tsare ya ƙi tafiya sai da Ɗahira, don shi gani yake yi kamar zata faɗa mata wani abun, shi kuma ba ya son kowa ya fahimci komi yanzu ba tare da ya wulaƙanta rayuwan ta ba, inyaso sai a saka shi ya sake ta da hujja, domin ya san muddin su Big Dady suka san wani abu, za su hana sa tafiya ko ina ne, sannan za su saka mishi ido, haka kuma zai ci gaba da zama da ita ba halin saki.

      Ɗahira ko jirgau bata yi ba don ba ta da ninyan tashi ma. Sai da Aunty Amarya tace mata, “ta tashi su tafi”. Kafin ta miƙe cike da ƙunan zuci tabi bayan sa, tamkar ta koma ta sanar wa mahaifiyar ta halin da take ciki, sai kuma ta ga hakan be dace ba, gwara taci gaba da haƙuri, Allah shi zai mata maganin komi, da sannu Allah zai saka mata. Idan Allah yayi auren su ba daɗaɗɗe bane nan kusa za su rabu da yardan Allah

    Kai tsaye Part ɗin Hajiya suka wuce, inda suka tarar da ita a parlour

Da sauri Ɗahira ta duƙa har ƙasa ta gaishe ta

Tsaban takaici ma Hajiyan bata amsa ta ba, illa ɗaure fuska da tayi tana kallon Usman tace, “na ji wani zance wai za ku tafi Turkey yawon cin amarci? Har yaushe ta shanye ka da zaku tafi cin amarci da ita? Yaushe ka soma son ta ma?”

Usman be tanka ba, don be da ma alaman tankawan

Ɗahira kuwa tuni ta sad da kanta ƙasa tana maimaita kalaman Hajiyan tamkar karatu, domin ta kasa ma fahimtar me take nufi

Tsawan da Hajiyan ta daka wa Usman ne ya dawo da Ɗahira cikin tunanin ta, da sauri ta ɗago kai tana kallon Hajiyan

“Ke tashi ki wuce”. Yayi maganar idanun sa a kan Ɗahira fuska babu walwala

Tana mayar da idanun ta kansa, ya ɗauke nashi idanun daga gare ta

Ta san babu da wanda zai yi sai da ita, don haka ta miƙe ta fice ta nufi hanyar gidan su.

     Kai tsaye ɗakin ta ta wuce ta zube saman gado, shiru tayi tana faman tunani, “ta fa kasa gane me mutanen gidan suke nufi, shin da gaske ne tafiya za su yi da shi ko kuma fahimta ne bata gama yi ba? Amma kuma ga abinda Mahaifiyar sa tace, ma’ana dai da ita yake son tafiya? Anya?” Sai kuma ta miƙe zaune kamar an zare mata laka, a ranta take tambayar kanta, “shin meyasa yake son yin tafiya da ita? Sai dai idan akwai abinda ya shirya yake son aiwatar wa a game da ita, idan ba haka ba mutumin da ya tsane ta ba zai taɓa tafiya da ita wani waje ba. Tabbas a cikin zuciyar ta ta kasa yarda babu komi a zuciyar Usman”.

Shigowar sa cikin ɗakin ne yasa tabi shi da idanu

Fuska a ɗaure ba tare da ya kalle ta ba yace, “ki shirya kayan ki.. by 03:00 pm. We’ll go”. Da gama maganar nasa ya juya da ninyar fice wa

Amma sai tayi saurin cewa, “Where are we going? Ni fa I don’t understand.”

Be ce mata komi ba bare ya juyo, ya ficewar sa.

    Ɗahira ta jima a nan zaune bata iya tsinana komi ba, sai kuma daga baya da ta ga bata da sauran dabara sai ta miƙe ta soma shirya kayan ta a cikin ɗan ƙaramin akwati, ba wani kaya da yawa ta zuba ba tunda har yanzu bata tantance inda za su je ba, duk da ta ji su Kaka ɗazu sun faɗi yawon cin amarci, amma ta san yanda suke zaune shiyasa ma bata saka maganar a rai ba, ta san sai masoyan asali ke irin wannan tafiyan amma ba su ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button