FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

Sosai taga ya sauya mata, gaba ɗaya ya rame ya rage haske, sai ƙasumba da ta ga ya ajiye, kamar dai ba shi ba ɗan gayen nan

Murmushi tayi masa itama, tana ƙarisa wa inda yake ta gaishe shi

Amsa wa yayi yana cewa, “amarya ba kya laifi.. ko da kin kashe ɗan masu gida”.

Dariya tayi tana ɗan rufe fuskar ta tace, “kai Yaya ka dena don Allah ba na so. Ina Sa’ada tana nan mu gaisa?”

“A’a ta fita, tana Part ɗin Hajja”.

“To bari inje Yaya”.

Daga nan ta wuce tayi ƙofan da zai sada ta da gidan su

Da kallo Baffa yake bin ta dashi, sai ya lumshe idanu yana jin hawaye na cika masa idanu. har yaushe zai jure da abinda yake ji? Yanzu ta zama matar ɗan uwan sa amma soyayyar ta ƙara wanzuwa yake yi a ransa

“Ya Allah ka cece Ni, ya Allah ka bani baiwar Allan nan idan har alkhairi ne ita a rayuwa ta..”

“Da wa kake yi ne haka?” Cewar Sa’adatu da ta tsaya gaban sa tana kallon sa, sai dai bata san me yake cewa ba

Buɗe idanun sa yayi yana kallon ta, sai kuma ya kawar da kai yana miƙe wa ya shige cikin parlour’n su

Itama bin bayan shi tayi fuskar ta tuni ya nuna damuwa, yanzu sam Baffa ya dena kula ta, sai tayi magana sau dubu be amsa mata ba.

               ⚫⚫⚫⚫⚫

     Da sallama Ɗahira ta shiga Part ɗin Hajiya, sai dai babu kowa a ciki, sai ta samu wuri ta zauna tana aza idanun ta kan t.v dake aiki

Kamar shuɗewar mintuna biyar sai ga Hajiya ta fito riƙe da Plate a hannun ta daga kichen. Ganin Ɗahira sai tayi kicin-kicin da fuska ta nufo cikin parlour’n

Da sauri Ɗahira ta zamo daga kan kujeran, ta zauna a ƙasa tana gaishe ta

Sai da ta zauna ta ɗan kalle ta a fizge, kafin tace, “Lafiya”.

Jiki a sanyaye Ɗahira ta sake duƙar da kanta ba tare da ta sake cewa uffan ba

Itama Hajiya bata sake kula ta ba, ta soma cin abincin ta.

      Har ta gama Ɗahira bata ɗago kai ba, tunanin kawai yanda zata iya rayuwa da su take yi, da kuma yanda suka tsane ta, nan da nan taji idanun ta sun ciko da hawaye, bata ankara ba taji sun soma zubo wa, saurin saka hannu tayi ta share tana ɗan ɗago kanta tabi Hajiyan da kallo, wanda ta fito daga kichen ajiye Plate ɗin; ta wuce ɗakin ta

Ɗan ajiyan zuciya ta sauke tana me lumshe idanun ta. sallaman Usman da yayi ciki-ciki ne ya saka ta ware ido sai a kan sa

Wanda shima ya sauke nasa idanun yana bin ta da wani irin kallon da ta kasa fassara shi.
????????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

         \F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

        EPISODE Thirty Nine

     Saurin ɗauke kanta tayi daga kallon sa, ta duƙar da kanta tana jin gaban ta na matsanancin faɗuwa, ko kaɗan ba ta ƙaunar su haɗa idanu, saboda kallon da yake mata sosai yake cutar da ita.

     Takowa yayi ya shige ɗakin Hajiya

Sai a lokacin ta sake ɗago kanta, ta ɗan kalli hanyar da ya bi, sai kuma tayi zugum ita kaɗai a parlour’n, ta rasa me zata yi, kar kuma ta tafi tayi laifi, sai ta tashi kawai ta shige kichen ɗin Hajiyan, duba wa tayi ko akwai wanke-wanke tayi, amma ƴan ƙwayoyi ne. Dayake ɗazu kafin su Aunty Zainab su wuce duk sun wanke.

     Wanke sauran tayi ta kife ta fito tana gyaran mayafin ta, sai kawai idanun ta suka faɗa cikin na Usman dake zaune saman dainning, saurin ɗauke kai tayi tana takowa ciki ta zauna a ƙasa kusa da kujera, bata sake ɗago kai ba bare ta kalli inda yake. Har ya gama tana nan a haka, sai da tajiyo sahun ƙafafun sa ya wuce ya nufi ƙofa kafin ta ɗago kai tabi shi da kallo, ƙare masa kallo kawai take yi har ya fice, kafin ta saki ajiyan zuciya tana ɗago hannayen ta ta soma murɗa su tana tunani

Fitowan Hajiya yasa ta ɗago kai ta bi ta da kallo

Ita Hajiya ma tayi tunanin ta wuce tun ɗazu, shiyasa bata ce mata komi ba tayi ninyan juyawa

Sai Ɗahiran tayi saurin ce mata, “zata tafi”.

Kanzil bata ce mata ba ta shige ɗakin ta

Sai jikin ta ya sake yin sanyi ƙalau, miƙe wa kawai tayi ta wuce gidan su, gaba ɗaya ranta babu daɗi, bata san tun yaushe Hajiya ta sauya mata ba, amma da sosai suke mutunci da ita.

     Tana shiga parlour’n suka sake haɗa ido da Usman dake zaune yana latsa waya, ya ɗago kai yana kallon ta

Janye idanun ta tayi da sauri, ta nufi hanyar ɗakin ta

“Zo nan”. Yayi maganar tamkar ba da ita yake yi ba, yana ci gaba da latsa wayan sa

Ɗan juyowa tayi tana kallon sa, sai kuma ta taka ta nufe sa, durƙusa wa tayi gaban sa tace masa “ga ta”.

Tamkar ba da shi take yi ba, be ɗago ba bare ya kalle ta, sai ma sake tamke fuskar nan nasa da kullum take a haka yayi, ya ɓata lokaci a haka be ɗago ba, be kuma ce mata komi ba

Ɗahira har ta gaji, sabida durƙuson da tayi ƙafafun ta sun soma mata zafi, jure wa kawai take yi, amma gaba ɗaya ba ta jin zata iya jure irin wannan wulaƙancin nasa, “don me ya kira ta kuma yayi banza da ita?” Sai kuma ta miƙe kawai ta nufi ɗakin ta

Bata san cewa yana biye da ita a baya ba, tana isa bakin gadon ta sai ji tayi an janyo ta baya, kasancewar gyalen ta ya riƙe ya shaƙe mata wuya, babu shiri ta waro ido waje tana kallon sa

While shima kallon nata yake yi fuska babu fara’a, cikin izgili da taƙaman sa yace, “kin dai ƙi jin magana ta? Sai da kika shigo gida na ko? To yau zan nuna miki banbancin Ni da kwaratan ki, sai kin gummaci zaman wuta da zaman gida na, domin sai na ɗai-ɗai ta rayuwan ki, sai kin yi dana-sanin zuwan ki duniya”.

Tuni Ɗahira ta soma hawaye sabida shaƙan da yayi mata, bata so yin magana ba, sai kuma tace, “meyasaka ka tsane Ni ne Ya Usman? Me nayi maka ne? Ko na tare maka wani abun ne?”

“Uban ki ki kai min! Na ce ubanki ki kai min”. Sai ya zaro mata idanun sa da suka juye suka yi ja yace, “na tsane ki! na tsane ki! Na tsani na buɗe ido na ganki, taya ma zan bari kiyi rayuwa a ƙarƙashi na?”

Sosai wannan karon Ɗahira take kuka, jin yanda ya zagar mata uba, babu abinda yafi ƙona mata rai sama da haka, sai ta saka ƙarfi ta janye gyalen ta idanun ta na zubar da hawaye

Bata ankara ba sai ji tayi ya falla mata mari, kafin kace me ya sake sakar mata wani, sai ya tura ta saman gadon yana cewa, “yau sai na kashe ki ko zan huta a rayuwa na”.

Sosai Ɗahira ta gigice da marin da yayi mata, lokaci ɗaya ta zaro ido ganin ya nufo ta gadan-gadan, wani ƙara ta saki tana me miƙe wa a saman gadon ta wuntsila can ɗaya side ɗin, sai gata ta faɗo ƙasa tim, duk da haka bata haƙura ba ta miƙe da sauri tana neman wajen ɓuya, gaba ɗaya ta fita hayyacin ta lokaci ɗaya, saboda ba kaɗan ba marin da yayi mata ya gigita ta, har kumatun ta sun kumbura

Sake fashe wa tayi da kuka da ta gansa kusa da ita

Janyo ta kawai yayi ya wurga ta saman gadon, ko kaɗan babu tausayi a lamarin Usman, domin sosai yake sake jin wutar tsanar ta na ƙara ruruwa a zuciyar sa, ji yake yi idan be kashe ta ko ya wulaƙanta rayuwan ta ba, bazai taɓa sukunin zuciya ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button