FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

    Da safe ta gwada buɗe ƙofan, sai taji ya buɗu, da sauri ta koma ta saka Hijab a saman kayan barcin ta ta fito da zumman zuwa gidan su ta faɗa wa iyayen ta komai, domin baza ta iya zama cikin uƙuba ba.

      Sai dai tana zuwa ƙofan Parlour ta ganshi a garƙame, lumshe idanuwan ta tayi hawaye na zubo mata, cikin muryan kuka tace, “Allah na roƙe ka, ka fitar dani daga hannun wannan azzalumin bawan naka”. Sai ta fashe da kuka. Juyawa tayi ta koma kan kujera ta kwanta tana ta rera wa, sai da tayi ma’ishi wanda daƙyar ma take iya numfarfashi saboda yunwan dake cin ta. Tashi tayi ta nufi saman dainning ganin cololi an jera, sai dai tana buɗe wa tsami ya bugo ta, sabida abincin tun na jiya ne da aka aiko mata, juya wa tayi ta koma kichen, a wahalce ta gama girka indomie, a kichen ɗin ta zauna ta hau ci hannu baka hannu ƙwarya, duk jikin ta rawa yake yi, babu abinda take yi sai zubar da hawaye, gaba ɗaya tausayin kanta ya kama ta, “yanzu idan a haka zata ci gaba da rayuwa ya zata yi? Babu dole fa auren nan.”

Sai da taji ta cika cikin ta fam kafin ta haƙura, tasha ruwa ta tashi ta fito, kan dainning ɗin ta nufa ta kwaso komi ta kai kichen, sai da tagama wanke gaba ɗaya cololin kafin ta wuce ɗaki, wanka tayi ta sauya kaya ta haye kan gado.

       Tun daga ranan haka Ɗahira take rayuwa, kullum tana gwada fita amma ina ƙofan rufe yake, ba ta da aikin yi sai dai ta kwanta tayi ta faman tunani, tun abun na damun ta har ta haƙura, ga shi ya raba ta da wayan ta bare ta kira Maman ta, gaba ɗaya tayi kewar su, kullum tana zaune cikin kaɗaici, ko kallo ba ta yi, sabida tun farko ma bata saba ɓata lokacin ta wajen kallo ba, ga shi ba ta sanin sanda Usman yake shigo wa da sanda yake fita, wataƙil ma ba a gidan yake kwana ba, shiyasa ta tashi tsaye wajen kai wa Allah kukan ta, shi ne ya jarabbe ta da wannan ƙaddararren auren, kuma shi ne zai fid da ita, domin bata da tsimi ko dabara, idan Allah yayi nufin Mijin ta me shiryuwa ne ya gane kuskuren sa, ita me iya biyayya ne ta zauna dashi kamar yanda iyayen ta suka zaɓa mata, amma muddin yaci gaba da wulaƙanta ta, to, dole ne zata sanar wa su Kaka a raba auren, domin baza ta iya zama ba.

         A haka har suka yi sati biyu da auren nan. A ranan da suka cika sati biyun ne, Usman ya koma aiki, har Office Big Dady ya Kira sa yace masa, “ya kamata ya bar matar sa taci gaba da zuwa aiki”. Be ce masa komi ba illa gyaɗa masa kai da yayi

Sai da ya dawo Direct ya wuce wajen Kaka

Kaka na murnan ganin sa yana cewa, “ina ya baro matar nasa? ya hana ta zuwa ta gaishe shi tunda aka yi aure”.

Taɓe baki yayi yace, “Ni Kaka zuwa nayi in sanar maka zamu tafi hutun amarci (Honeymoon) Ni da ita”.
????????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

         \F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

         NATSUWA A SALLAH
Manzon Allah mai tsira da aminci, ya ce, “sallah ba kome ba ce illa miƙa wuya da tawali’u…” Kuma ya ƙara da cewa, “Bawa bai samun ladan sallar sa sai gwargwadon abinda ya hankalta daga sallar.” Watau, gwargwadon natsuwar mutum cikin sallah gwargwadon darajar da yake samu gun Allah. Don haka ne ma ma’aikin Allah ya ce, “Allah ba ya juya wa Bawa baya yana cikin sallah matuƙar bai waiwaya ba; idan ya waiwaya kuwa, sai Allah ya bijire masa.”
Babu abin da yake kawo waiwayo cikin sallah kuwa sai gafalar Bawa da muƙamin Ubangijin sa, watau ya zama tamkar wanda ya tsaya yana ganawa da Ubangijin sa alhali zuciyar sa tana shagale da wani abin dabam. A kan wannan matsala ne Allah yake ce wa Manzon sa, da al’ummar sa ma, a cikin suratul A’ARAF aya ta 205:
“Kada ka kasance daga gafalallu.”
In muka lura sai mu ga cewa ta ya ya kuwa gafalalle zai iya tunawa da muƙamin Ubangijin sa yana cikin wannan hali na rashin kula har wani abin tsoro ya auku? Bugu da ƙari, daman can ga shi Allah ya yi umarni a cikin suratul Ɗ.H., aya ta 14 da cewa:
“Kuma ka tsayar da Sallah domin tuna Ni”.
In mutum ya Yi haka, ana fata ya rabban ta.
   Allah yasa mu dace.

.

        EPISODE Forty

     Washe baki Kaka yayi yace, “to to kai da Ɗahiran ce za ku tafi hutun?”

“Eh mana Kaka”. Yayi maganar yana yatsina

“To Masha Allah Abu yayi daɗi, masha Allah”. Kakan ya sake faɗa cike da farin ciki, domin ba kaɗan ba yaji daɗin hakan, tabbatan dai suna zaman lafiya. Sai kuma ya sake kallon Usman ɗin yace, “But when are you going? And what country are you planning to go to?”

“Tomorrow evening .. We will go to Turkey .. because can nake da gida.. na fi son zaman can”. Yayi maganar tamkar ba ya so

“Masha Allah.. to Allah ya Kai ku lafiya, zan sanar da iyayen naka ko, ita kuma zuwa goben ya kamata tayi wa kowa sallama”.

Tashi tsaye Usman yayi yana faman taɓe baki, kafin yace, “ai ba sai kace ba Kaka, she will come to greet you”.

“Ja’irin yaro ka ganka ko? Kai dai ba’a yin abun arziƙi da kai Fodio”. Cewar Kaka yana murmushi

Shi kuwa be ma bi ta kansa ba ya bar ɗakin. Kai tsaye Part ɗin iyayen shi ya wuce, babu kowa a Parlour, sai ya wuce ɗakin sa ya ɗauro alwala, da zai tafi masallaci ne suka ci karo da Hajiya, gaishe ta yayi ya wuce da sauri sabida har an gama kiran sallan magriba, kafin ya kai za su iya tayar wa.

    Sai bayan isha’i ya koma gidan su. Yana shiga parlour’n ya mayar da ƙofan ya rufe, kai tsaye ɗakin sa ya wuce ya yi shirin kwanciyar sa, zama yayi kan gado ya ɗauko Lapton ɗin sa yana dannawa, a haka har dare yayi nisa, sannan ya kwanta barci.

          Itama Ɗahira tuni tayi barcin ta, tunda babu abinda take yi sai kwanciya, iyakan tayi girki iya bakin ta ta cinye ta ɗauraye abun da ta ɓata ne, dayake ba shigo musu ake yi ba ko shara ba ta yi tunda babu inda yake ɓaci, ɗakin ta kawai take kakkaɓe wa ta share.

           TOMORROW

      Tana kwance a kan gadon ta tayi ɗai-ɗai, daga ita sai shimi fara da gajeren wandon sa shima fari, ta rufe gashin kanta da hula me raga-raga ja, babu abinda take yi sai tunanin ta yanda za’a yi ta koma aikin ta, zuwa yanzu ya kamata ta koma bakin aikin ta ko don ta riƙa ɗebe kewa, tunda babu abinda take yi yanzu a gidan.

      Buɗe ƙofan da aka yi yasa ta ɗago kanta tana aza manyan idanuwan ta a kansa, saurin kau da kai tayi daga kallon sa

While shima tunda ya shigo ya sauke ido a kanta, ya ɗauke kansa yana jan dogon tsaki tare da haɗe rai

Tsakin kamar a tsakar kanta yayi, itama sai taci magani zuciyar ta cike da baƙin cikin ganin sa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button