FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

Ɗahira bata yi musu ba, ta amsa ta soma sha

Ita kuma ta koma ta zauna tana ce mata, “ɗazu muka yi waya da Fadila ai, take tambaya na baki zo ba har yanzu? Shi ne nace mata ai yau Hajja ta kira Ni ta sanar min zuwan naki”.

Murmushi kaɗai Ɗahira tayi tana ci gaba da sipping Juice ɗin ta, a ranta jin ta kawai take yi, kuma ta san manufar ta, shiyasa ma ko magana ba ta son Yi, Allah-Allah take yi ta bar gidan ma, sabida gaba ɗaya haushin Shakiran take ji, ga kanta dake faman sara mata zuciyar ta duk babu daɗi, duk surutun da Shakiran take mata ba ta tanka ta, har dai ta gaji itama ta dena, sai suka koma zugun suna kallo

Nan Ɗahira ta tashi tace mata “zata tafi,” har waje ta rako ta tana bata saƙon gaisuwa wajen mutanen gida. Motan ta na fita ta koma cikin gida da sauri ta wawuri waya don kiran YUSRA.

                 ⚫⚫⚫

         Sanda Ɗahira ta isa gida, tana shiga parlour’n su ta tarar da Aunty Zulaiha da Fadil zaune, da fara’an ta ta isa kusa da ita tana faɗin, “laa Aunty kin zo ne?”

Itama cikin fara’an tace da ita, “wlh kuwa, ina zuwa ai Aunty Amarya tace min kin fita zuwa gidan su Shakira da na tambaye ta”

“Wlh kuwa Aunty, Ina Ilham ɗin?”

“Tana wajen Kaka, kinga wanda ya kaita nan ya bar ta can”.

Kallon Fadil tayi tace, “To je ka ɗauko min ita”.

“Kai Aunty Ɗahira ki bari mana zuwa anjima in ɗauko ta, yanzu fa kika dawo”.

Hararan sa tayi sai dai bata ce komi ba, ta tashi tsaye tana faɗin, “Aunty bari in rage kayan jikina sai in zo dai muyi hira, bari in shiga ɗakin Mama”.

Tun kafin ma ta ƙarisa Fadil yace mata, “tana kichen ai”.

Kichen ɗin ta wuce, ta sanar mata ta dawo, ita kuma tayi mata sannu da zuwa, sanann ta wuce ɗakin su ta sauya kaya zuwa jan doguwar riga me taushi mara nauyi, sannan ta sake fitowa, nan ta zauna sukai ta zuba hira da Aunty Zulaiha

Itama Aunty Amarya da ta fito zama tayi tana taya su hiran, lokaci bayan lokaci tana zuwa dubo girkin ta

Tashi Ɗahira tayi tace, “bari dai in je ɗauko ta tunda yaron nan ba zuwa zai yi ba”. Ta ƙare maganar da dungure wa Fadil kai

Turo baki yayi yana cewa, “Kai Aunty! Kai Aunty! Ki bari to yanzu zan je ɗauko ta”.

“A’a ba na so bar shi, ai ina da ƙafa ko?”.

Aunty Zulaiha na musu dariya tace, “ai nima yanzu zan yi haraman tafiya, dama duba ƙanwar Baban Ilham ɗin ya kawo Ni, to shi ne na biyo gida”.

“Eyya kina nufin Maman Sumayya?” Cewar Ɗahiran tana kallon ta

“Wlh ita fa, har a asibiti an kwantar da ita, ai asibitin mu ne ma aka kwantar da ita, baki sani ba ashe?”

“Wlh kuwa ban da labari, wani ciwo take yi?”

“Ciwon ƙoda ne take fama dashi, amma yanzu an sallame ta ai”.

“Allah Sarki! Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne”.

“Amen amen”. Daga Aunty Zulaiha har Aunty Amarya da ta fito daga kishen yanzu suka amsa.

       Ɗahira fita tayi ta wuce Part ɗin Kaka, inda ta same shi a ɗakin sa yana Sallah, Ilham kuma na wasa a ƙasa da kayan wasan da Kaka ya zube mata, dayake ba ya rasa kayan wasa a wajen sa, sabida ita da Jinior ɗan wajen Aunty Zainab, duk idan sun zo suna kawo masa su, sai ya zube musu kayan wasan saboda kar su riƙa masa kuka.

       Ɗaukan ta tayi, ta hau mata wasa tana shilla ta tare da mata rawa

Lokacin da Kaka ya idar ya kalle ta yana murmushi yace, “dayake ai akwai me gadon zinare waje na, ga shi kin biyo ta”. (sunan Umma Ilham ɗin taci, Bilkisu, kuma sunan Mahaifiyar Kaka ne dama Umma taci)

Dariya Ɗahira tayi tana tashi daga kan kujeran ta dawo gefen gadon sa, tunda dama gadon ya fi kusa da wheel chair ɗin sa, tace dashi, “kai Kaka.. dama ai ina zuwa duba ka, kwana biyu ne kawai ban samu na shigo ba, amma yanzu ɗin ma ai sabida kai na zo”.

Murmushi yayi yace, “naga alama ai”.

Dariya ta sake yi tana cewa, “baka yarda ba ko?”

“Na yarda Matata, to ya ƙarfin jikin?”

“Alhmadulillah Kaka, ai yanzu na samu lafiya har na kere ka ma”.

“Ah Masha Allah Abu yayi kyau, fata na kenan dama Matata ta fi ni lafiya”. Ya faɗa yana dariya

Itama tana taya sa

Lokacin ne Aunty Zulaiha ta shigo tana faɗin, “Mata da Miji sun haɗu waje ɗaya, hira ba ya ƙare wa, to na zo ɗaukar ɗiya ta zan wuce”.

“Kai Aunty yanzu fa na zo”. Cewar Ɗahira tana ɓata fuska

Shi kuma Kaka yace, “Ja’ira ko kunya ta ma ba kya ji kin zo ɗaukar ɗiyar ki ko?”

Dariya ta kwashe dashi tana cewa, “Kaka wani kunyan ka zan ji? Tafiya fa zan yi, amma idan kana so in bar maka ita, ai Ni abu me sauƙi ne a waje na, wlh sai in tafi in bar maka, gaba ta kai Ni wai gobaran titi a Jos”.

“To ban ce ba, ɗauki ɗiyar ki ki tafi, me zan yi da wannan mummunan ɗiyar taki?”.

Dariya suka saka gaba ɗaya, ganin yanda Kaka ya taƙume fuskar sa yana kallon Ilham kamar ya ga kashi

Aunty Zulaiha tace, “ai Kaka kai ta biyo wlh, kaima ka sani, kar ka wani tsine ta. Kuma Maman ka ce babu ruwana”.

Taɓe baki yayi yace, “jaaa can da Allah! Ki ɗauki ƴar ki ki wuce kin ji, duk kin cika min kunne da surutu”.

“Shikenan Kaka, kora ta kake yi ko? Babu damuwa ai, dani kake zancen wlh”. Cewar Aunty Zulaihan tana ƙarisa wa ta ɗauki Ilham tana saɓa ta a baya

Dama sun saba irin haka sosai, kusan a jikokin gidan, Kaka da Aunty Zulaiha sun fi wasan jika da Kaka, idan suka haɗu waje ɗaya bakin ɗayan su ba ya shiru.

Tashi Ɗahira tayi, tace wa Kakan “zata je ta raka ta”. Sannan suka fice tare.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

           WASHE GARI
                12:30pm.

             Shigowar motan Usman ɗin cikin asibitin, yasa Ayush buɗe motan Safra tana leƙa wa, sai kuma ta juyo ga Safran dake latsa waya tace da ita, “Ga shinan ya shigo”.

Ɗago kai Safra tayi, tana bin waje da kallo tana faɗin, “ina yake?”

“Wannan motan”. Ayush ta nuna mata motan Usman da ya ƙariso kusa da na su ya tsaya

Da ido Safra tabi motan da kallo, shi kansa motan ba ƙaramin burge ta yayi ba, bare kuma sanda tayi tozali da mamallakin Motan, hohoho ai da sauri ta buɗe motan ta fito tana sake ƙare masa kallo

Itama Ayush fitowan tayi tana bin sa da kallo tamkar zata cinye sa, a duk socond ɗaya ƙaunar sa na ƙara ruruwa a zuciyar ta, sosai yayi mata kyau tare da ƙara mata kwarjini fiye da kullum, yana sanye cikin ƙananan kaya ne, wanda koda yaushe shigan da ya saba yi kenan, sai ƙyalli yake yi, kai da gani kasan hutu da jin daɗi ya zauna masa, kuma duk wanda ya kalle sa ya san cewa ba ƙaramin haɗaɗɗen Guy bane, sosai yake da son gayu fiye da tunanin mutum, shiyasa yake fita daban duk inda ya shiga, yana zama tamkar wani tauraro me haska waje, bare shi Fari ne, ga kyawu na ban mamaki.

       Duk abun nan be ma san suna yi ba, tafiyan sa kawai yake yi ya shige cikin Hospital ɗin, fuskar sa kamar dai yanda take babu fara’a, illa kwarjini da take dashi, wanda idan ka kalle sa dole ne fuskar tasa ta burge ka, duk da kuwa babu ko ɗigon annuri, amma kwarjinin sa shi yake ƙara masa kyau.

“Gaskiya Ayush dole ne ki haukace saboda wannan Guy ɗin, Ni kaina ba ƙaramin tafiya da imani na yayi ba a kallon farko duk da Maza ba sa burge Ni, bare ke da kika saba ganin sa kullum”. Cewar Safra tana kallon Ayush ɗin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button