FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

Babu jima wa wata Nurse ta shigo bayan tayi Nocking an ba ta izni

“Gani Doctor” Nurse ɗin tace hakan bayan ta tsaya a gaban table ɗin Ɗahiran

Lokacin ne ta ɗago kai ta kalle ta, sannan taɗau alluran ta miƙo mata tace, “Yauwa Sister ga shi ki je ɗakin da yarinyan nan da aka kawo jiya take kwance kiyi mata alluran nan, Please yanzu zaki yi mata Dr. Rahab bata kusa ne Ni kuma ban yi sallah ba lokaci ya ƙure, ki kula da ita zuwa sanda zata dawo sabida ako yaushe zata iya farka wa kinji?”

Murmusawa Nurse ɗin tayi sannan tasaka hannu ta’amsa alluran a lokaci ɗaya take faɗin “insha Allahu doctor”. Sannan ta juya ta fice

Ita kuma Ɗahira miƙe wa tayi ta cire Labcoat ɗin ta; ta rataye a Hanger, sannan ta zare Eyeglasess ɗin ta tare da agogon hannun ta ta’ajiye ta nufi cikin Toilet ɗauro alwala.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

         Sai da suka gama kitumurmuran su na abin da suke ƙulla wa a kan Baffa da Ɗahira kafin Shakiran ta sauke ta a bakin gidan su sannan taja motan ta tatafi

Ayush bata shiga gidan ba sai ta nufi cikin anguwan, gidan ƙawarta Rumanatu

Rumanatu ƙawa ce wajen Ayush tun na yarinta, da gidan su Ayush ɗin da gidan su Rumanatu gida ɗaya yaraba su, sun taso makaranta tare komi nasu tare har zuwa matakin da suka kai NCE, inda daga nan ne Rumanatu ta dakata da karatun nata, yanzu haka shekara biyu kenan da auren ta, ta taɓa haihuwa ɗan nata na da wata bakwai ya rasu

Gidan ba wani babba bane gidan Rumanatun but gida ne na masu hali tunda mijin ta yana da ƙumban Susa, shima a anguwan yake da zama da iyayen sa

Ƙofar gidan ta ƙwanƙwasa tunda a rufe yake daga ciki, babu jima wa aka zo aka buɗe mata

Rumanatun ce da kanta, ganin Ayush a gaban gidan ta sai ta kwantsama ihu tana rungume ta tare da faɗin, “Ayushhhh”.

Dariya Ayush tayi itama tana rungume ta ɗin, kafin suka saki juna suka shige ta rufo ƙofan, cikin gidan suka shiga suka yaɗa zango a parlour

“Waiii wata sabon gani ai nayi fushi wlh”. Cewar Rumanatu tana ajiye mata farantin silver da ta ciko da drinks

Dariya Ayush tayi bata ce komi ba ta ɗauki Robbern Coke tana buɗe wa

Rumanatun ta sake cewa, “tunda kin zama big girl me amsar Albashi duk wata ai dole ki guje mu”.

Still dariyan Ayush ta sake yi kafin tace, “wlh kema kin san ba haka bane, tsakani da Allah idan zaki faɗa gaskiya kema kin san bazan taɓa juya miki baya ba, ai ke kin fi ƙarfin haka a waje na”.

Kanta ta ɗaga tana taɓe baki tace, “da dai ban san daɗin bakin ki bane, kar fa ki raina min hankali”.

Kwashe wa da dariya Ayush tayi har da ɗan buga ƙafafun ta

Rumanatu ta harare ta tana faɗin, “ke dai kika sani”.

Ɗan langaɓe kai tayi cikin muryan tausayi tace, “na rantse da Allah ki yarda dani My Ruman, wlh aiki ne ya ɓoye Ni but kiyi haƙuri ban sake wa”.

“To ya na iya, yanzu wuni kika zo min ko kuwa?” Rumanatu tace hakan tana tsare ta da idanuwan ta

Sai da ta yatsina fuska kafin tace, “daga wajen aiki nayo nan fa, wlh damuwa ce dani nake neman me bani shawara”.

“Shegiya ashe ba don Ni kika zo ba matsalan ki takawo ki? ke wlh baki da mutunci Ayush”. Tafaɗa tana dariya

“Ke dai bani shawara kawai ki ajiye wannan a gefe, babban matsala ce dani wlh”.

“To ina jin ki fesa min naji”.

Sai da ta sauke numfashi kafin tace, “wlh wani Guy ne nake faɗa miki na kamu da mahaukacin ƙaunar sa, don bazan iya ce miki son da nake masa me hankali bane, yau rana ɗaya na gansa amma wlh baki ga yanda na kasa samun nutsuwar zuciya ba”.

Dariya Rumanatu ta sheƙe dashi har da tafa hannayen ta, “Wayyo Allah ki ce yau kin samu wanda ya susutar dake? tirƙashi zamu sha biki kenan”.

“Ke ba nan matsalan take ba, bari dai in warware miki komi don ki fahimce ni da kyau”. Ayush taƙarishe maganar tana muskuta zaman ta

Tiryan-tiryan tafaɗa mata komi har shirin su da Shakira

Sai da ta gama Rumanatu tace, “lallai kin taro match baki da ƴan wasa, amma kinga Ni shawaran da zan baki tunda har kin samu Baffa ta hanya me sauƙi haka, ga shi har kun zama friend soyayya ce kawai ta rage wanda hakan ba wani matsala bane a wurin ki na sani, to me zai hana ki ƙyale shi wannan Guy ɗin da kika gani, kinga fa kince min Familyn su ɗaya, kar ki je kiyi saki na dafe”.

Izuwa yanzu fuskar Ayush ya sauya da matsanancin damuwa, cikin sanyin murya tace, “wlh nima haka na gani Ruman, sai dai kuma matsalan yanda zuciyata ta kamu da ƙaunar Usman na haƙiƙa fiye da Baffa, wlh a yanda nake ji a yanzu dai zan iya rasa komi nawa don in mallake sa, Usman ba irin mazajen nan da mata zasu gansa su ƙyale bane, wlh kinji na rantse miki ya wuce gaban kwatance, amma baza ki gane hakan ba sai idan kinyi ido biyu dashi zaki gane irin su ne mazan nan da samun su babban nasara ne a duniyar mu, kin san me? Wlh kyau dai Usman bazai nuna wa Baffa ba, fari ne kaɗai zan iya cewa Usman ya ɗara Baffa domin babu maraban su, amma kuma wayewan su tasha bamban matuƙa, duk da Baffa shima wayayyen saurayi ne wanda duk macen da ta same sa ta gama Sa’a, sai dai abinda yafi jan hankali na akan Usman kasancewar sa yayi rayuwan out side, that’s why dole su bambanta nesa ba kusa ba, uhmmm baza ki gane ba amma wlh zuciyata ta kamu, domin ko wacce zuciya da abun da tafi ƙauna, Ni shi nake so ba wanin sa ba”. Ayush taƙarishe maganar da dafe setting ƙirjin ta

Jinjina kanta Rumanatu tayi tana kallon Ƙawar nata cike da tausayi, domin ba kaɗan ba ta bata tausayi don sosai ta hango iya gaskiyar ta a idanun ta, so babban cuta ne ga duk wanda ya kamu da ita dole ya zama abar tausayawa

“Gaskiya kina cikin wani hali Ayush dole in tausaya miki, domin kuwa nima na shiga wannan halin kafin in auri Musbahu, amma Ni abinda nake ganin ya dace kiyi yanzu, ta yanda kika bi da Baffan ta nan zaki bi da Usman ɗin..”

Tun kafin ta gama kai aya a zancen ta Ayush ta katse ta da faɗin, “Ruman yanda nake faɗa miki Usman ya bambanta da Baffa nesa ba kusa ba, a halayyan su daban ne sosai, a yanda Shakira ta faɗa min ta ce mugun me zafin kai ne, yana da tsananin miskilanci fiye da tunanin mutum, be da harka ko kaɗan, wlh Ni kaina da na ganshi na yarda da hakan don banga alamun zai iya saurarona ta wannan hanyan ba”. Sai kuma ta girgiza kanta taci gaba da faɗin, “Inaa! kwarjinin sa ma bazai bar Ni inje ba”.

Numfashi Rumanatu ta saki tana kallon Ayush ɗin, “To yanzu ya kike so ayi?”.

“I don’t know Ruman, shawaran ki nake nema”.

“Ok Ni dai shawarana a nan kawai kibi sa a social media, idan har ya kula ki sai ki faɗa masa abinda ke zuciyar ki, kar ki tsaya tamkar na wannan ki ce zaki ƙi sanar masa, duk da haka ki bani time sai mu san abun yi ko? Ai shawara bazai gagara ba za mu samu mafita”.

Murmushi Ayush tayi tace, “Yauwa my Ruman shiyasa nake son ki, I know zaki iya wlh, yanzu ki bani Numban ki so that mu riƙa communicate, wancan Numban taki idan na kira ba ta shiga”.

“Wlh kuwa, wayan faɗi tayi shiyasa ai”. Rumanatu taƙarishe maganar nata tana amsar wayan Ayush ɗin ta soma ƙoƙarin saka mata Numban

Daga nan hira suka soma yi don Ayush tace mata “ba yanzu zata wuce ba,” don haka Rumanatun ta miƙe domin ta girka mata wani abun, tare suka shiga kichen ɗin tana taya ta.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

       Ƙarfe 06:01pm. Ɗahira ta gama komi nata ta haɗa kan files ɗin dake gaban ta, sannan ta ɗau jakan ta tare da files ɗin ta fito cikin Office ɗin nata, rufewa tayi tana juyowa shima Usman ya fito daga office ɗin sa riƙe da kai yana yamutsa fuska

Idanun su ne suka haɗe waje ɗaya yayinda gaban ko wannen su yayi mummunan faɗuwa, musamman ma na Usman wanda ya kasa jurewa har sai da ya runtse idanun sa zuciyar sa na masa wani irin ƙunci

Ya tsani wannan yanayin a koda yaushe da yake rinskan sa, that’s why ya tsani ganin Ɗahira sabida duk idan idanun sa zasu shiga nata to tabbas sai ya rasa nutsuwar sa tare da bugawar zuciya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button