FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

.

EPISODE four

Babban haraban asibitin cike yake da mutane bila adadin, mutane ne kamar tsaki kama daga yara manya masu kuɗi da manyan likitoci duk an gayyace su, har ta da gwamna Malam Nasiru El Rufa'i sai da aka gayyace shi wajen, komi ana yinsa ne akan tsari gunun sha'awa

Ɗahira, Shakira, Yusra da Fadila can na hango su wajen zaman su daban, sosai su kayi kyau cikin shigan su na material fari ƙal da akayi masa ɗige-ɗigen Coffee colour, ɗinkin doguwan riga akayi musu fitted, sai suka yane kan su da Goldeen Veil tare da sanya Hill shoes shima Golden, sosai su kayi matuƙar kyau kamar ka sace su ka gudu sai faman haskawa suke yi kamar taurari

Nan akayi ta gabatar da komi cikin girma da arziƙi, daga ƙarshe aka gabatar dasu a matsiyin waɗanda ake taya murna tare da sauran sabbin ma’aikata da za’a ɗiba.

  Wata kyakykyawar Farar mota ce ta shigo haraban asibitin, a hankali motar take tafiya har zuwa inda sauran motocin suke fake, tsawon mintuna 5 kafin aka buɗe motan ya zuro kyawawan ƙafafun sa kana ya fito a hankali yana rufe motan, kyakykyawar saurayi ne da aƙalla bazai wuce 32yrs ba, fari ne tarrr kamar kalatsa shi jini ya fito don har wani ɗaukan idanu yake yi, yana sanye da Milk ɗin riga me gajeren hannu da ya matse sa sosai, sai Blue Jeans tare da sanya Combat a ƙafafun sa shima blue, yana da yalwan gashin kai kwantacce baƙi siɗik tare da ɗan siririn sajen sa, Kallo ɗaya idan kayi wa Guy ɗin zaka tabbatar da ya haɗu ne tako ina, *USMAN NOOR AL'AMEEN* kenan, *(The Younger Doctor)* yaro kyakykyawa me Izza da Son nuna shi wani ne, ma'aboci Son gayu da son hutu

A hankali ya taka ya soma tafiya cike da taƙama ya nufi inda su Big Dady suke.

Har aka gama taron sannan kowa ya soma tafiya gida, sai yamma duk yawancin ƴan uwa suka soma watsewa sai gidan ya rage daga ƴaƴan Kaka sai jikokin shi suka rage waɗanda basu tafi ba, su ma ɗin a gobe duk za su watse su tafi

Washe gari ƙarfe 05:00pm. Na Yamma gaba ɗaya a halin gidan sun hallara a babban parlour bisa umarnin Kaka

Ɗahira ce tafito daga Part ɗin su don ita bata riga ta tafi ba, tana sanye da doguwar rigan atamfa kalan ja da ratsin Milk da ruwan ƙwai, rigan iyakan ta ƙwaurin ƙafafuwan ta kuma sosai tayi mata kyau ta sake fito da tsantsan kyawunta da kwarjinin ta, sai tayi Rolling da ɗan ƙaramin Veil da iyakan sa kafaɗun ta, Slippers ne a ƙafanta tana tafiya tana latsa waya, hira take yi da freinds ɗinta na Facebook sai faman doka murmushi take yi, gab da ta iso ƙofan da zata sada ta da General parlour taji tayi karo da mutum wanda hakan yasaka wayan ta ya zame ya faɗi ƙasa, a hankali ta ɗago kanta tana kallon sa

haka zalika shima ɗin dai-dai da sanda ya sauke nashi idanun cikin ƙwayan idanuwanta da yafi tsana cikin rayuwan sa

kallon sa kawai take yi babu ko ƙyafta idon

While shi kuma ya ɗaure fuska tamau yaja jikin sa ya wuce, gab da zai buɗe ƙofa ya tsinkayi zazzaƙan muryan ta tana cewa

“Ba ka ganin kayar min da waya ne?”

Cak ya tsaya yana juyowa ya kalle ta da tsananin mamaki da ya nuna a face ɗin sa, ita kuwa a lokacin kallon wayan nata da ya fashe take yi cike da tsananin baƙin ciki sannan ta ɗago kyawawan idanun ta tana kallon sa itama fuskarta a ɗaure

A hankali ya tako ya’iso gaban ta still yana ci gaba da kallon ta, duk da ya daɗe be ganta ba kuma tayi masa girma ainun but be yi tunanin cewa ta kai matsayin da har za tayi masa irin wannan maganar ba, shiru yayi yana ƙare mata kallo yayinda itama ɗin shi take kallo batare da ko alaman tsoro ya nuna a fuskarta ba, abinda ya ƙara ba shi matuƙar mamaki kenan, domin yasan ada babu wanda tafi tsoro sama dashi, idan har zata gan shi ko za taji sunan sa tsoro ne da fargaba suke kawo mata cafka, ko kaɗan bata haɗa hanya dashi bare magana ya haɗa su, duk inda akwai shi to ta haramta wa kanta wurin har sanda zai bar wajen

Kuma hakan ya samo asali ne tun sanda ta tashi da wayon ta take matuƙar tsoron sa, ba don komi ba sai tsananin azaban da yake gana mata da tsanar da yake nuna mata afili ko a ɓoye, shi kuwa tun sanda aka haife ta ya haɗa idanu da ita shikenan yaji ya matuƙar tsanar ta, ba don komi ba sai don ƙwayar idanun ta da ya kalla, sabida idan har zai kalle ta sai yaji faɗuwar gaba me tsanani tare da tsoro wanda hakan ne ya saka mishi muguwan tsanar ta cikin ran sa, sosai cikin ƙwayar idanun ta da suka kasance sky green suke bashi tsoro da fargaba, hakan yasa tun tana ƙarama ko ɗaukan ta ba ya yi, da zaran ya ganta duka ne abinda ke haɗa shi da ita, har zuwa kuwa girman ta da ta gane shi ɗin mugu ne, koda laifi sukayi ƴan gidan gaba ɗaya, to ita yake kamawa ya fanshe kaf dukan da zai yi musu akan ta, ko agaban waye babu wanda zai iya hana sa, kuma koda an hana sa sai ya san yanda yayi ya haɗu da ita ya gana mata azaba, Ɗahira ta tashi cikin tsoron sa matuƙa wanda ya haddasa mata tsanar sa fiye da wanda yake mata, kwata-kwata bata ƙaunar sa bata ƙaunar ganin sa koda jin sunan sa ne, ta saka wa kanta shi ɗin maƙiyin ta ne wanda babu wadda tafi tsana a duniya sama dashi

Wajen shekara 9-10years kenan babu shi a ƙasan, yana can ƙasar Turkey yana aiki acan, tun sanda ya tafi karatu ya zauna can sai dai yazo gaishe su, Ɗahira ta dena jin tsoron sa ne don kawai daɗewan da tayi ba ta ganin shi, and sai kuma girma da yazo mata, yanzu baza ta taɓa juran abinda yayi mata a baya ba, domin ita tana ganin ta wuce matsayin da zata zauna wani banza wanda ba iyayen ta ba ya duke ta bare har taji tsoron sa.

  Sauke kansa yayi kan wayan yana kallo, sai kuma ya mayar da idanun sa kanta yana sake ɗaure fuska ya ɗaga ƙafan sa ɗaya ya ɗaura saman wayan ya soma murje ta da ƙaton takalmin sa da ya kasance tamkar irin na sojoji, babu abinda ake ji sai sautin ƙaran fashewan wayan

Ita kuwa Ɗahira sauke idanun ta kan ƙafan sa tayi tana kallon wayan yayinda taji hawaye sun ciko mata idanu sabida tsananin baƙin ciki da yazo mata iya wuya, still ɗago kanta tayi tana kallon sa cike da zallan tsana da ya nuna a cikin ƙwayan idanun nata

shi kuma hawayen da ya gani a idanun nata shi ya saka shi jin wani farin ciki tare da sanyi a ransa, magana ce a bakin sa yake son faɗa mata amma girman kai da Izza sun hana sa buɗe bakin, illa juyawa da yayi ya nufi ƙofa ya buɗe ya shige

Ƙaran rufe ƙofan ne ya saka ta ƙyafta idanun ta wanda hakan ne yasa hawayen ta daman zubowa suka sauka kan kuncin ta, ahankali ta sake mayar da idanun ta kan wayanta da ya gama murƙushe ta duk screan ɗin ya farfashe babu kyan gani, wasu zafafan hawayen ne suka soma sintiri a face ɗin ta, tayi saurin saka hannu ta soma sharewa domin baza ta bama kanta daman nuna raunin ta kan shi ba, dole ne ta nuna masa yanzu ba irin da bane, dole ta nuna masa ba ta tsoron sa, kuma duk abinda yayi mata BASHI ne ya ɗauka dole sai ya biya, don haka ɗaukan wayan tayi ta nufi ciki itama da sauri.

To fa nan ake yinta, bari muga me zai faru?

kar ku manta ku suburbuɗo min Comments ta hakan ne zai bani daman ƙara muku yawan Page.

Plz
Share and Vote.
[5/21, 3:30 PM] Oummu Ɗahirah: ????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTORS
????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu????✓”’

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattpad: UmmuDahirah????

     *\F.W.A????/*

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

.

    *EPISODE Five*

Da shigan ta darect wajen Kaka ta nufa, ta sami waje kan hannun kujeran dake kusa da Wheel chair ɗin sa ta zauna tana sauke kai ƙasa

“Matata lafiya wa ya taɓa min ke?”

Abinda ya saka yayi mata tambayar ya santa idan har tazo wuri dole sai ta tsokane shi, ƙa’ida ne sai taja masa gemu kafin ta nemi wurin zama

Ɗago kanta tayi tana kallon sa sai kuma ta soma wurwurga idanun ta tana kallon mutanen wurin da duk suka nutsu suna kallon ta, a kan Usman dake zaune kusa da Abbun ta ta sauke idanu, yayin da shi kuwa wayan sa yake latsawa ko sanin Allah yayi ruwanta be yi ba

“Tell me my wife. I can’t calm down idan ban san abin da ke damun ki ba?”

Dawo da idanun ta kan Kaka tayi cike da marairaice fuska tace, “Kaka Ya Usman ne ya fasa min waya, kuma ya saka ƙafa ya tattaka shi da gangar”.

Kaka salati yayi yana kallon wayan dake hannun ta kana ya mayar da idanun sa kan Usman da har yanzu yaƙi ya ɗago kansa duk da yana jin abinda ake yi, shi har a lakocin mamakin yarinyan yake yi ainun, “yaushe har ta samu ƙwarin gwiwar da har zata kawo ƙarar sa? Lallai yarinyan nan dole ya koya mata hankali”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button