FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

“Fadil ba ka da kunya ko?” Cewar Ɗahira tana murmushin zancen sa

“Ki ƙyale sa, zan gyara masa zama wlh kafin in tafi, ai kasan hali na?” Fadila ta faɗa tana tsare sa da idanu fuska a kirne

Be sake cewa komi ba ya fice da sauri, don yasan yayi tsokana, gwara ya fece tun kafin ta kama shi

Ɗahira tace, “ga shi har an kira Ni ba mu gaisa ba, bari in dawo sai mu gaisa”.

“Ok Nima Ina Nan zuwa wajen Kakan yanzu ai”. Cewar Fadila tana tashi tsaye

Tare suka fita daga ɗakin.
????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

\F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

*HADHISI *
Aisha (may Allah be pleased with her) was quoted as saying, “The Messenger of Allah (may peace be upon him) married her when she was six years old, and she was nine years old with him, and Allah took her life when she was eighteen years old.” Reported by Muslim.

.

EPISODE Thirty Seven

K.B ne da Aunty Amarya a Parlour’n zaune, ita kuma Umma tana kichen tana shirya abincin ranan da bata kammala ba

“Ƙanwa ta ashe kina ciki kin maƙale ina ta tambayar ki?” Cewar K.B yana kallon Ɗahira da suka ƙariso wajen tare da Fadila

Dariya tayi tace, “Yayana anya baka neme Ni ba dai, Tunda ai Mama ta san ina ɗaki”.

“Aff to ai yanzu ne na soma maganar taki”.

“To magana ta fito fili kenan”. Tafaɗa tana dariya

Zama Fadila tayi gefen sa, don ita Aunty Amarya har ta tashi ta shige ɗaki ma

Gaishe sa Ɗahira tayi

Ya amsa yana cewa, “wai ƙanwa ta ciwo kika yi kika rame haka? Ko dai zullumin auren ne?” Yayi maganar cikin barkwanci

Murmushi kawai tayi

While Fadila tace, “Nima haka na gani yaya, wai ciwo tayi”.

Tashi Ɗahira tayi tace, “bari dai inje in dawo Kaka na kira na sai muyi magana, I have something to talk to you about. yaushe Shamsiyya zata zo ne?”

Taɓe baki yayi yace, “to ki dai kira mijin ta ki tambaye sa, amma bani ba, tunda Ni ga nawa tazo”.

Dariya kawai tayi ta wuce ta bar su nan. Ta san halin K.B idan ta biye mishi babu inda zata je

Part ɗin Kaka ta wuce kai tsaye, tana shiga ɗakin sa da sallama

Ya amsa mata yana zaune kan gadon sa yana duba wani ƙaton littafi na addini

“Taho Mata ta”. Yayi maganar yana kallon ta da murmushi a kyakykyawar face ɗin sa

Taho wa tayi ta zauna gefen sa tace, “Kakus nayi kewar ka”. Ta ƙare maganar da jan gemun sa

“Me too My wife, bayan ma yanzu kin dena nema na, har sai na aika a kira ki kike zuwa, yanzu kenan idan kinyi auren ma haka zaki guje Ni ko?”

“Eyya Kaka wlh No, I will never run away from you, idan ba ka a rayuwa ta ai kamar babu Ni ce”. Tayi maganar tana langaɓe kai

“To amma ciwo kika sake yi ne bani da labari, naga duk kin sake rame wa ne sosai?”.

“kai Kakus, sai dai idanun ka ne suka gane maka haka, amma ai dama can haka nake”. Tayi maganar tana dariya

“Anya ba zullumin rabuwa dani kike yi ba?”

Dariya sosai wannan karon take yi

Shima yana taya ta, sai kuma yace, “faɗa min gaskiya Ɗahira, do you want this marriage or not?”

Kallon sa tayi tana tsayar da dariyan, sai kuma ta yafa wa fuskar ta murmushi tace, “Kaka idan ma ba na son auren ai bazan ƙi muku biyayya ba, kana tunanin zan watsa muku ƙasa a ido ne? Never. Ba na fatan wannan ranan tazo”.

Murmushin jin daɗi yayi, sosai yaji daɗin kalaman ta, amma sai yace, “Mata ta a kan farin cikin ki babu abinda bazan iya ba, ko yau ake ɗaura auren ku kika ce baki so, to zan dakatar dashi, Na san yanda kuke da Fodio, ko kaɗan jinin ku be haɗu ba, tabbas nasan sai kinyi haƙuri dashi kafin komi ya daidaita, amma kuma hakan da nayi shi ne naga ya dace, wannan hanyar ce kaɗai zai sa ku dawo kuna shiri, domin ba na son nan gaba bayan ba na raye iyali na kansu ya rabu, zan so tun ina da rai inga kun shirya kan ku, kun dawo kuna ƙaunar junan ku, wannan shi ne burina, domin ba na jin daɗin yanda tun kina ƙarama yake nuna miki tsana”.

Hannayen sa ta riƙo, idanun ta cike da hawaye, tace, “wlh Kaka zan yi muku biyayya ko waye kuka kawo min a matsayin miji, bare kuma ɗan uwa na. Na rigada na ɗaukar maka alƙawari da kai da iyaye na zan yi zaman auren nan da zuciya ɗaya, fata na kawai Allah ya bani ikon yin biyayya a gare ku da miji na”.

Tafin da Fadila take yi ne yasa suka juyo suna kallon ta, “oh ka ga masoyan asali? an haɗa kai ana ta ƙus-ƙus”. Tayi maganar cikin sigan tsokana, duk da kuwa sai da ta gama jin abinda suke cewa ta shigo

Kaka yace, “Miskila kin fi mahaukaci ban haushi saukar yaushe?”

Dariya tayi tana zama kan drowern gadon tace, “yanzun nan babu daɗe wa Alh. Kaka, ya gida? na same ku lafiya?”

Yana murmushi ya amsa mata da cewa, “alhmadulillah.. Ina Kakan nawa, shi dai ya kawo ki ko?”

“Shi ya kawo Ni, yana waje tare da Ya Baffa”.

“Masha Allah, ya wajen su Rabi’atu (Hajiya Ikram) komi lafiya?”

“Lafiya lau Kaka, suna gaishe ka da kyau-da kyau, sai jibi za su zo su”.

A lokacin ne shima K.B ya shigo, nan suka shantake gaba ɗaya ana ta hira da Kaka, har Ɗahira da ba jin daɗin jikin ta take yi ba, sai dai ta saki jiki sosai tana ta saka musu baki, daga ƙarshe K.B ne ya soma tafiya, tunda dama yau ne zai koma, sai ranan biki ya dawo

Su ma daga baya fitowa suka yi, Fadila ta wuce sashin Hajja don ta gaishe su, ita kuma Ɗahira tayi Part ɗin su

A Hanya suka haɗu da Usman yana taho wa, tunda ta gansa gaban ta yayi muguwar sara wa, tayi saurin kawar da kai daga kallon sa, rabon da ta gansa tun ranan da aka ce za’a haɗa su aure, sai yanzu

Shima dai tunda ya ganta yayi matuƙar ɗaure fuska, zuciyar sa na wani irin tafarfasa saboda ganin ta da yayi

Suna zuwa dai-dai juna yace da ita, “ta biyo sa”.

Sarai Ɗahira taji me yace, duk da kuwa babu wanda zai ce yayi magana, sabida yanda yayi maganar a ciki, kuma kansa na kallon hanya babu wanda zai ce da ita yake yi, ita kuwa taci gaba da tafiya tana jin ƙirjin ta na bugawa da sauri-da sauri

Ji tayi kawai an jawo ta baya an haɗa ta da bango, wanda sai da yasa ta saki ƙara saboda buguwan da ƙashin ta yayi, zaro idanu kawai tayi tana kallon sa kamar zuciyar ta zata faso ƙirjin ta ta fito tsaban tsoro

“Ni nake kiran ki kike banza dani?” Yayi maganar a zuciye tamkar zai kai mata bugu

Runtse ido tayi da sauri jikin ta na rawa

Cikin ɗacin rai yace, “shashashan yarinya ballagaza, sauran maza, tun wuri ma ki je ki ce baki son auren nan, idan ba haka ba wlh sai na halaka ki kika shigo gida na, na tsane ki ba na ƙaunar ki! kuma bazan taɓa son ki ba, ƴar iska kawai”.

Yanda ta ƙwalalo masa idanun ta dake zubar da hawaye, ji yake yi kamar ya saka hannu ya ƙwaƙulo su, sai dai dauriya da yake yi sabida ba ƙaramin jin tsanar ta yake yi ba. saurin janye hannun sa daga riƙe mata kafaɗa yayi, yana matsawa da sauri tare da tofar da yawu, ciki-ciki yace, “ƙazamiya.. wai a rasa ma wanda za’a aura min sai sauran maza irin ki? tirrr dake”. Ya buga mata wani banzan kallo ya wuce da sauri

Zame wa tayi a nan ta haɗa kanta da ƙafafun ta ta soma kuka, kuka me taɓa zuciya, har wani rawa jikin ta yake yi, kalaman sa ne suke yawo a cikin kunnen ta, “me yake nufi kenan? Bayan tsanar da yayi mata yanzu kuma kallon ta yake yi ƴar iska? Har da kiran ta ƙazamiya. Karuwa?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button