FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

Sosai Baffa yayi dariya yana kallon ta yace, “Why did you say that?”
“Uhmm only”.
Murmushi yayi a wannan karon yace, “ke dai ki faɗa abinda ke zuciyar ki”.
Maƙe kafaɗa tayi cike da yauƙin muryan ta tace, “Yaya Ni dai nasan kana min rowan ta ne shiyasa ma baka taɓa nuna min ita ba ko da a hoto ne, but nasan dai kuna fita irin wajen shaƙatawan nan”.
Baffa kallon ta kawai yake yi cike da burgewa, ji yake yi aran sa tamkar yace, “ke ce macen da na taɓa so a RAYUWATA, sai kuma ya girgiza kansa still yana murmushi yace, “My sister kenan, idan har zaki yarda wlh ban taɓa yin budurwa ba”.
Ƙwalalo idanu tayi tace, “kai Yaya dagaske kake yi ko wasa? How can it be said that Handsome Guy and you have no girlfriend? Ko dai yaya kana ɓoye min ne ba ka son na sani?”.
Cikin ido yake kallon ta cike da wani irin salo
Hakan yasaka ta ɗauke kanta tana ci gaba da cin abincin ta cike da yanga da ya zamar mata jiki, komi nata hakan take yin sa
Huro iskan bakin sa yayi be ɗauke ido a kanta ba yace, “Da gaske ƙanwata ban taɓa budurwa ba wlh, akwai wacce nake matuƙar ƙauna sai dai har yanzu na kasa sanar mata”.
Ɗago kai tayi tana kallon sa da mamaki kafin tace, “why?”
“Saboda kwarjinin ta..”
Dariyan ta ya saka shi yin shiru yana sake ƙure ta da idanun sa, sosai take dariya shi kuma yana bin ta da kallo cike da tsananin ƙaunar ta da burge shi da take yi
Sai da tayi son ranta sannan tace, “Yaya har akwai macen da zaka kasa sanar mata ƙaunar ka gare ta sabida kwarjini? Shin me tafi ka dashi ne? Kyau ko nasaba ko kuwa kuɗi? Ni na tabbata Yayana duk kwarjinin ta baza ta kai ka ba, kai dai kawai kace kana jin tsoron ta; abun kuma da ban san ka dashi ba”.
Baffa yace, “baza ki gane bane Sister, duk abinda kika lissafo tana dasu, sai dai kamar yanda nace miki kwarjinin ta da cikan kamalan ta ya zarce duk tunanin namiji ya iya tunkarar ta da soyayya, a kullum idan nayi yunƙurin zuwa gare ta da soyayyata sai inga girman ta da kwarjinin ta bazai bari na sanar mata ba, yanda nake ji a gaban ta da bugawar zuciya da zaran nayi yunƙurin sanar mata sai in kasa, sau ba adadi nayi hakan amma na gaza”.
Kallon Yayan nata kawai take yi cike da tausayin sa har yayi shiru, sannan ta ɗaura da cewa, “How can I help you find her love? Why don’t you let me know who I am; and I promise to tell her, sannan kuma zan taya ka yaƙi har sai ta amince da kai, Yaya ban ga macen da zata ƙi son ka ba komin kyan ta komi kwarjinin ta kuwa, sai dai idan har baka faɗa mata ba, Yaya ka cire tsoro ko fargaba ka sanar mata don Allah”.
Murmushi yayi yace, “na gode ƙanwata, haƙiƙa nasan kina son farin ciki na, sai dai bazan iya faɗa miki ko ita ɗin wace ce ba, but I promise I will try to tell her.”
Murmushi tayi kawai ba tare da tayi tunanin matsa masa akan sanin meyasaka be son sanar mata ba? Ita a komi nata tana ma mutum uzuri maybe yana da dalilin hakan ne
“To yaya na gane, but hurry up and tell her because soon Kaka will start talking about your marriage, kuma ka ga idan baka sanar mata ba za’ayi babu kai haka zakai ta zama a Gwauron ka”.
Baffa laughed and said, “Well shikenan my sister, but ni nafi son nayi aure lokacin da kema za kiyi”.
Zaro idanu tayi tace, “Yaya baka shirya auren ba kenan? Because I don’t have a real boyfriend.”
“Hmm you’re just saying, duk da ban taɓa ganin kin kawo kowa gida ba amma fa ina da tabbacin kina da masoyi don kuwa irin ki ba su rasa masoya”.
Shiru kawai tayi a wannan karon tana murmusawa, sai kuma ta duƙar da kanta tana ci gaba da juya spoon ɗin hannun ta cikin abincin
“Talk to us My dear, when will you show me my son-in-law?”
Ɗago kai tayi tana kallon sa tace, “Yaya Ni bani da gwani har yanzu, amma dai ka taya ni da addu’a”.
Sanyi yaji cikin ransa, cike da nuna tausayawan sa a fuska yace, “My dear Sister, I promise to help you. I pray to God to bless a good husband who loves you so much, kuma Allah yasa nan kusa za kiyi aure baza kiyi nesa damu ba”.
Dariya tayi cike da farin ciki tace, “kamar ka sani Yayana ko kaɗan ba na Son auren nesa sabida ba na Son nayi nesa da ku, sannan ba na son na dena aiki a hospital ɗin mu, Burina yana da nasaba da aiki cikin Hospital ɗin mu, ka ga kuwa ba na so na zama kamar Aunty Zulaiha da tabar aiki lokaci ƙanƙani, tayi nisa babu daman ci gaban ta a nan, nima ina so ayi alfahari dani cikin Family na; ya kasance ina ba da tawa gudunmawa wajen haɓɓaka shi”.
Filled with her love Baffa said, “God fulfill your dream My dear sister”.
“Ameen my brother, we should hurry back because my waking time is near, and I want to check on my patients.”
“To sarkin aiki ba kya gajiya?”
Murmushi tayi kawai tana ɗaukan Holandia tana sha, bayan ta gama ta’ajiye tana kallon sa tace,”Come on, I’m full.”
Ɓa ta fuska yayi yana kallon abincin gaban ta yace, “Baki ci da yawa ba ai?”
Marairaice fuskar ta tayi tace, “Yaya na ƙoshi ne”.
“Ok to tashi muje nima na ƙoshi tunda kin ƙoshi”.
Sai da ya biya kuɗin sannan suka fito suka shige cikin motan yaja suka nufi Hospital ɗin
Suna shiga haraban Hospital ɗin suka fito ya rufe motan suka jera suka nufin cikin asibitin
A reception Ɗahira ta hango aunty Zainab, tayi saurin zuwa wajen ta tana cewa, “Aunty Zainab”.
Juyo wa Aunty Zainab tayi tana kallon ta sai ta faɗaɗa fara’an ta tana faɗin “a’a! my sister. I have been asking Fadila Ni kam ban ganki ba tunda kuka fara aiki”.
Dariya Ɗahira tayi tana cewa, “wlh kuwa Aunty nayi ninyan zuwa har Office ɗin ki, to, aiki yayi yawa I don’t have time.”
Aunty Zainab kallon Baffa da ya ƙariso wajen su ya tsaya yana kallon su tayi tace, “oh ka ga masoya! ina kuma kuka je?”
Ɗahira kallon Baffa tayi suka haɗa idanu, sai ta saki dariya tana mayar da idanun ta kan Aunty Zainab tace, “aunty kenan abinci fa muka je ci da Yaya”.
Smiling, Aunty Zainab said, “Hmm Na ga alam ai”.
Baffa dake faman shafa kansa yace, “kin ji ABU da wata magana don mun fita da ƙanwata za kiyi mana fassara daban?”.
Ɗan waro ido tayi tace, “wai laifi ne don nace masoya kaji min yara?”
Yanda tayi maganar yasa su dariya gaba ɗaya
Still Ɗahira na dariyan tace, “Where’s Jinior?”
“Shigo wa ta kenan itama Fadila ta shigo shi ne ta’amshe shi”.
Baffa kallon Ɗahira yayi yace, “mu je kin ji My sister Kar mu biye mata”.
Hararan sa Aunty Zainab tayi tace, “to babu inda zata je.. kaje kai”.
Shima hararan ta yayi yana cewa, “ke fa kina son raina ni fa, wai ba tare kika gan mu ba?”
“Eh tare na gan ku amma aiken ta zanyi”.
Kafin yayi magana Ɗahira tayi saurin cewa, “Yaya ka je zan zo har Office ɗin ka”.
Gyaɗa mata kai kawai yayi jin wayan sa na ringing, zaro wayan yayi cikin aljihu yana yin gaba abin sa bayan ya ɗaga mata hannu alamun ya tafi
“Hmm Ni dai ina mamakin wannan shaƙuwa na ku, anya.. anya..”?
Ƙwalalo idanun ta Ɗahira tayi tana kallon ta tace, “kai Aunty babu daman Yaya ya nuna wa ƙanwar sa kula wa sai da wani abun? Ni fa na ce miki abinci muka je ci”.
“To ai nima ba fitar da kuka yi bane nake magana, mu je kawai”. Aunty Zainab ɗin taƙarike maganar ta tana yin gaba
Ɗahira tabi bayan ta suna sauya hiran su
Office ɗin Aunty Zainab ɗin suka shiga, bayan sun zauna ta ɗauko mata wasu files ta miƙa mata
“Ga shi don Allah Ɗahira, ki kai wa Dr. Said don ba na son ya sake damu na”.
Amsar files ɗin Ɗahira tayi tana kallon ta tace, “Aunty who is Dr. Said?”