FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

Murmushi me ma’anoni da dama Ayush ta saki tana kallon Shakira tace, “ke dai ki zuba idanu ki gani, da zaran mun haɗu ma zan sanar masa ina ƙaunar sa don ma ya sani tun yanzu”.
Dariya Shakira tayi tace, “Thanks.. sai kuma mu jira muga shirin namu zai yi aiki ko kuwa..”
“Idan ma bazai yi ba sai mu sauya salo”. Ayush tafaɗa itama tana dariyan
Jinjina kanta Shakira tayi cike da jindaɗi sannan tace, “Is it tomorrow when we meet?”
“Yeah insha Allah”. Cewar Ayush tana ɗaukan jakan ta sannan ta buɗe murfin motan
Daga nan sallama su kayi ta fito cikin motan, ita kuma Shakira taja tabar ƙofar gidan su Ayush ɗin
Tana nan tsaye tana ɗaga mata hannu har ta ɓace ma ganin ta, murmushi ta saki tana faɗin, “Uhmm Dama ta biyu kenan, yanzu komi zai soma min daɗi, tabbas Buri na zai yi saurin cika, da wannan shirin naki Ni kuma zan cika tawa Burin”.
Dariya tayi ta shige gidan su
Babban gida ne me sasa biyu, na farkon shi ne na mahaifin ta, inda akwai ɗakuna Huɗu da kichen a bakin ƙofan gidan; sai kuma bayi dake can ƙuryan sasan wanda aka rufe sa da fale-fale
Ƴaƴan Baban su su goma ne maza da mata kuma itace ta Biyar, sannan duk mahaifiyar su ɗaya.
Ɗayan sasan kuma Ƙanin Baban su ne ke zaune da matar sa, yaran sa shida shima maza da mata.
Ba wani kuɗi suke dashi ba amma suna da rufin asiri dai-dai gwargwado, mahaifin su yana ɗauke musu duk wani nauyi da ya rataya akan sa
A cikin ƴaƴan sa mata Ayush ce kaɗai tayi karatu me zurfi har matakin Doctoring, Wanda hakan shi ne burin ta, don tasan shine hanya ta farko da zata iya bi wajen cin ma babban burin ta, wato auren me kuɗi
Tun tana yarinya ta taso tana jin labarin Familyn Dr. Al’ameen Abubakar Khabeer Cindo, kuma sosai take jin labarin Hospital ɗin sa da ya shahara a faɗin Nigeria, wanda idan har za’a yi kwatance, to, da shi ake yi. Wannan dalilin ne ya saka ta ɗaukar ma kanta alƙawarin sai tayi aiki a cikin asibitin sabida ta nuna wa ƙawayen ta da ƴan uwanta tafi su
Zuwan ta asibitin da yanda taga tsaruwan Hospital ɗin tare da Familyn gaba ɗaya sai tayi sha’awar kasancewar ta cikin FAMILYN, burin ta a yanzu shi ne ko ta halin ƙaƙa ta shiga gidan itama ta zama ɗaya daga cikin familyn da su kayi Suna a faɗin Nageria; kuma suke ji da kuɗi da Izza
Binciken Farko da tayi shi ne sanin mutanen gidan, duk da bata samu labari sosai ga jama’an gidan ba amma ta gano Maza biyu ne kaɗai a cikin gidan kuma duk basu yi aure ba, ɗayan yana Aiki a ƙasar Turkey, ɗayan kuma yana aiki a Hospital ɗin su
Sai ta yanke shawaran fara shiga jikin ƴan gidan don samun damar kusanci gare su, abun kuma sai yazo mata da sauƙi office ɗin ta na kusa dana Ƙanwar Baffa ne wato Shakira, don haka ta nemi ƙawance da ita lokaci ɗaya kuma Shakira ta’amince.
A yau ɗin kuma sai ga Shakira ta zo mata da wani aiki akan jan hankalin Baffa ya faɗa tarkon ta duk a sabida a raba shi da Ɗahira, ba tare da Shakiran ta san da cewa Ayush ɗin dama tana neman hanyan da zata shiga jikin ɗaya daga cikin samarin gidan bane; don ta samu ta aure sa.
.
plz kuyi Vote da Comments.
[5/24, 1:37 PM] Oummu Ɗahirah: ????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTORS
????
????????????????????????????????????????
????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????
MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL
بسم الله الرحمن الرحيم
⚖
FEENAH WRITER’S ASSO????®Ɗaya tamkar da Dubu????✓
JIKAR LAWALI CE✍️
Wattpad: UmmuDahirah????
*\F.W.A????/*
SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY
*EPISODE Thirteen*
Ahankali ta buɗe kyawawan idanun ta tana sake lumshewa cike da kasala, hannu biyu ta sanya ta riƙe kanta dake faman sara mata a hankali, tayi wajen mintuna biyar kafin ta soma yunƙurin tashi zaune tana jingina bayan ta da jikin gadon, sake lumshe idanun ta tayi tana soka hannu ƙasan pilon ta tazaro wayan ta ta kunna, sai da tasan ya gama kunnuwa kafin ta buɗe idanun ta tana kallon screan ɗin wayan, agogo ta duba taga ƙarfe 07:45am.
Ajiye wayan tayi tana sakin hamma kafin ta zuro ƙafafuwan ta ƙasa tana shirin sauka taji ƙarar shigowan text message, wayan ta ɗauka ta duba taga Numban jiya ne da aka yi mata Text dashi, da sauri ta buɗe jikin ta na rawa ta soma karanta wa
_ “Aslm alaikum Good morning Sweetie, I hope you are well? Take care of yourself God bless you then work” _
_MASOYIN KI✍️_
Jujjuya maganar take yi cikin ranta cike da tunani kala-kala, sosai take mamakin wannan mutumin da yake iƙirarin shi ɗin masoyin ta ne
“Ko dai ya San ni ne? But who is he? Why bazai fito fili ya nuna min kan sa ba?” Tafaɗa maganar a fili
Ajiye wayan tayi tana ninyan tashi sai kuma ta dawo ta zauna tana ɗaukan wayan tayi dialling Numban, Amma kuma a kashe yake
Shiru tayi tana riƙe da wayan a hannu, ta daɗe tana nan zaune tana faman tunani tare da son gano wanda ke mata wannan text ɗin, ganin zata ɓata lokacin ta tamiƙe ta shige Toilet, wanke bakin ta tayi ta fito ta ɗau ɗan ƙaramin Hijabin ta tasaka a saman kayan barcin ta masu taushi ta fice
Gaba ɗayan su suna zaune a dainning suna breakfast, Abbu ne kaɗai ya miƙe tsaye yana goge bakin sa da tissue alamun ya gama nashi breakfast ɗin
“Abbu Good morning”. Tafaɗi hakan lokacin da ta’iso wajen tana kallon sa da murmushi
Shima murmushin yayi yana kallon ta ya’amsa mata cike da kulawa, sannan ya tambayi “Ya ya ta tashi?”
Ta’amsa mishi tana zama kan kujera kafin ta gaishe da Mahaifiyar ta da Umma
Abbu said, “Fadil, get up and let me drop you off.”
“To Abbu”. Cewar Fadil ɗin yana miƙewa ya nufi ɗakin Umma don ɗauko School Bag ɗin sa
Duk a dawo lafiya sukai ma Abbu ɗin kafin ya fice, Fadil shima ya fito ya bi bayan sa da sauri
Fadila ta soma tashi a cikin su ta nufi saman sofa ta zauna, daga baya kuma Umma da Aunty Amarya su ma suka tashi aka bar Ɗahira ita kaɗai tana karyawa
Bayan ta gama itama miƙewa tayi ta shiga ɗakin su, tana shiga ta cire kayan ta tashiga wanka, bata jima ba ta fito tana ɗaure da Showel a jikin ta
Ƙarisawa tayi ta ɗau wayan ta dake faman ruri, sai da ta zauna kan stool dake gaban mirror kafin ta’amsa call ɗin
“Aslm alaikum Yayana na kaina”.
Sautin murmushin sa ne ya doki kunnen ta kafin yace, “Wa’alaikis salam My dear Sister, kin tashi lafiya?”
“Lafiya lau yaya, kaifa ya kake?”
“Alhmadulillah My dear, har kin fito?”
Girgiza kanta tayi kamar yana ganin ta kafin tace, “a’a Yaya yanzu dai zan shirya in fito”.
Baffa yace, “ok Ni na rigada na fita tun 07:00am. Ina da Theater, but my sister ki je ɗaki na ki ɗauko min takardu dana manta ban ɗauka ba, suna nan akan drower na ajiye su”.
“To Yaya amma ka kulle ɗakin ne?”
“Eh na kulle kiyi amfani da keey ɗin wajen ki”.
Ɗahira tace, “to Yaya”.
“Allah ya kawo min ke lafiya ki kula da tuƙi kin ji?”
Murmushi ta saki cike da jindaɗi kafin tace, “insha Allah Yaya bye”.
Daga nan katse wayan yayi ita kuma ta’ajiye wayan ta soma shafe-shafen ta.
⚫⚫⚫
Yana sauke wayan a kunnen sa ya'ajiye saman table yaci gaba da aikin sa cikin Computer
Nocking yaji ana masa, be ɗago kai ba ya ba da umarnin shigo wa
Buɗe ƙofan tayi ta shigo da siririn sallama me haɗe da kisisina
Hakan ya saka ya ɗago kansa yana sauke idanun sa a kanta, sannan ne ya’amsa mata yana ci gaba da kallon ta
Murmushi tayi wanda ta san yana narkar da duk namijin da ya gani, cikin takun ta da son burge sa ta’iso wajen tana kallon sa still tana murmusawa tace, “Dr. Al’ameen Abubakar Al’ameen”.
Baffa da ya sauke kansa ƙasa yaci gaba da aikin sa, jin ta kira sunan sa sai ya sake ɗago kansa yana kallon ta
Bata bari yayi magana ba tariga sa da cewa, “Can I sit down?”
Be ce mata komi ba illa nuna mata kujera da yayi da hannu
Zama tayi tana kallon sa cike da wani irin salo tace, “nasan baka gane Ni ba ko? I am Dr. Ayush Abdulkarim and I called you yesterday”.
Sai a lokacin Baffa ya ɗan saki fuskar sa kafin yace, “Allah Sarki ai ban gane ki ba, amma fa bakin ki ya riƙe suna na da yawa”.
Ayush cike da yanga tace, “ai ba baki na bane ya riƙe sunan ka ba, sunan ka ne ya zauna a baki na, daɗin sunan ka ke sakawa ba na gajiya da faɗin sunan ko da kuwa na so bari”.
Murmushi kawai yayi yana kallon ta
Ita kuma sai ta gyara zaman ta da kyau tana sake kafe sa da idanu tare da son burge sa tace, “kayi haƙuri da kiran da nayi maka jiya amma zuciyata ce ta kasa haƙuri da son ƙulla alaƙa da kai, idan har baza ka damu ba zan so mu zama friends duk da kuwa nasan nayi maka katsalandan cikin rayuwa, amma gaskiya bazan ɓoye maka ba ka burge Ni ne sosai shiyasa nake son wata alaƙa me ƙarfi ta shiga tsakanin mu”.