FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

“Har kin sallami Maman nawa ne?”
Maganar Abbu ya katse mata tunanin ta, sai ta juyo tana kallon sa, ta ce, “eh, na ga ai kana waya ne, kuma bata ci abinci ba shi ne nace ta je taci. Ko in Kira ta ne?”.
“No. Let her eat her food.”
Koma wa Aunty Amarya tayi ta zauna, don har ta rigada ta yunƙura zata tashi.
⚫⚫⚫
Ɗahira na fita bata ci abincin ba ta koma ɗaki, domin baza ta iya saka komi a bakin ta ba, ko da taci kuwa, baza ta ji daɗin sa ba.
Tana shiga ta haye kan gadon ta ta kwanta, sai dai ta daɗe kafin ta samu barci ya ɗauke ta, gaba ɗaya tunani ya hana ta sukuni, sai daƙyar ta samu tayi barci.
Washe gari da zazzaɓi ta tashi, dole ta sake komawa ta kwanta bayan ta yi sallan asuba, har gari ya waye bata farka daga barcin da ya ɗauke ta ba.
Kowa ya hallara wajen Breakfast amma ban da ita
Aunty Amarya tambayan Fadila tayi “where is she?”
Sai ta faɗa mata, “she was sleeping, she didn’t wake up”.
Har ta ce “taje ta taso ta sabida kar tayi lattin zuwa wajen aiki”
Amma Abbu ya ce, “su bar ta”.
Har suka gama Breakfast ɗin, shi da Fadil suka fice, Umma ta shige ɗakin ta, yayinda Fadila kuma ta koma cikin Parlour ta zauna abun ta tana aikin latsa waya
Aunty Amarya har ta koma ɗaki, sai kuma ta kasa jure wa, don tasan Ɗahira sarai, tunda ta kwanta ba lafiya ba, bare yanda take son Aikin ta, haka kawai yau ranan aiki ba zata ƙi fitowa ba in babu Dalili
Ɗakin ta wuce kanta tsaye don ta duba ta. Tana shiga ta hange ta saman gado ta rufe kanta da blanket, da sauri ta ƙarisa wajen gadon ta saka hannu ta yaye saman kanta, fuskar ta take kallo tana kiran sunan ta
A hankali Ɗahira ta buɗe idanuwan ta da suka yi ja, ta aza su kan Maman ta
“Baki da lafiya ne, me ke damun ki?” Ta jero mata tambayar a yanayin damuwa
Cikin matuƙar sanyin murya da ciwo yake cin ta tace, “zazzaɓi ne ya rufe Ni Mama”.
Cike da tausaya wa take mata sannu, kana tace mata, “ta tashi tayi wanka, inyaso sai ta sha magani bayan taci abinci”.
Babu yanda ta iya haka ta miƙe, da taimakon Aunty Amarya har ta ƙarisa Toilet
Ita kuma Aunty Amarya ta fice haɗo mata Breakfast don ta kawo mata har nan cikin ɗakin. Bayan ta haɗo mata ta kawo mata ta zauna zaman jiran ta.
Kamar shuɗewar mintuna sha biyar Ɗahira ta fito a Toilet, ɗaure take da towel me tsawo iya ƙasan gwiwan ta, sai ta saka wani da ya rufe mata kanta zuwa kafaɗun ta
Tana fitowa Aunty Amarya tace, “yi maza ki shirya ki zo ki karya ki sha magani, kina likita amma kina wasa da shan magani, wataƙil ma tun jiya da kika yi kukan naki zazzaɓin ya kama ki amma kin zauna baki sha magani ba”.
Kallon ta Ɗahira tayi da sauri, sai kuma ta kawar da kanta cike da sanyin jiki ta kariso gaban Sip ɗin kayan su, buɗe wa tayi ta ciro doguwar rigan atamfa. Sai da tagama shirya wa kafin ta iso gaban aunty Amarya dake bakin gadon ta, a ƙasa ta zauna ta tanƙwashe ƙafa ta soma shan tea ɗin da ta haɗa mata, tana yi tana haɗa wa da bread kamar yanda Aunty Amarya ta umarce ta, sai dai tana cin ɗaya biyu taji kamar zata yi amai, ta kalli Aunty Amarya ta marairaice fuska kamar zata yi kuka tace, “zan yi amai bazan iya ci ba”.
“To shanye tea ɗin ki sha maganin”.
Ajiye bread ɗin tayi da ƙwan, ta sha tea ɗin, har sai da takusa shanye wa kafin ta amshi maganin ta kora da sauran
“Ina jin ki, Why are you crying? What’s wrong with you?”
Sunkuyar da kanta Ɗahira tayi don bata san me zata ce mata ba
“Ina magana kin yi shiru, meyasa zaki zauna ki saka damuwa a ranki har kiyi irin wannan kukan da ya haddasa miki ciwo? Bayan kin san halin kanki abu kaɗan ne yake haddasa miki ciwo idan kin saka damuwa?”.
Matso hawaye Ɗahira tayi, har yanzu ta kasa yin magana tunda bata san yanda za’a yi ta faɗa ma Mahaifiyar nata matsalan ta ba
“Ko sabida ya ƙi zuwa ne kike kuka?”
Ɗaga mata kai tayi, kafin ta cire kunya ta sanar mata komi
Ajiyan zuciya Aunty Amarya ta sauke, cike da tausayin ɗiyar ta tace, “ki yi haƙuri haka Allah ya so dama ba shi ne wanda zaki aura ba, Allah ya musanya miki da wanda ya fi shi, amma ki dena saka damuwa a ranki kinji? ki fauwala wa Allah komi, ai Kakan ba cewa yayi zai zaɓa muku wani ba idan baku kawo wanda zaku aura ba, don haka ki dena saka maganar auren nan na damun ki”.
Gyaɗa mata kai tayi
Sai da ta sake tausan ta kafin ta fice ta bar ta
Sosai maganar Maman ta ya sanya ta jin sanyi a ranta, dama ita yanzu damuwar ta yanda kowa zai kai zaɓin sa, amma ita ban da ita.
A haka ta saki jikin ta a ranan taci gaba da walwalan ta, sai dai bata je aiki ba ta bar wa gobe.
[6/3, 5:48 PM] Oummu Ɗahirah: ????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????
????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????
MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL.
بسم الله الرحمن الرحيم
⚖
???????????????????????? ????????????????????????’???? ????????????????????*
®Ɗ???????????? ???????????????????????? ???????? ????????????????????✓
???????????????????? ???????????????????????? ????????✍️
????????????????????????????: ????????????????????????????????????????????????
\????.????.????????/
????????????????????????????????????????
???????? ???????????????????????????????? ???????? ???????????????????????? ???????? ???????????????? ɗ????????????. ????????????????’???? ????????????????????????.
*EPISODE Twenty-Five*
Kamar yanda Hajja Fatu tace zata kira Hajiya Amina su yi magana, hakan kuwa tayi, sun gama ƙulle-ƙullen su a waya, kafin suka yi sallama akan zata turo Sa'adatu gobe-goben nan kamar yanda ta buƙata, yanzu ɗin ma don ba ta kusa ne da sun yi waya.
Washe gari zuwa yamma sai ga Sa'adatu ta dira garin Kaduna
Hajja Fatu zuwa tayi har ɗakin Baffa ta tasa shi gaba akan “lallai-lallai sai ya je ya ɗauko Sa’adatu a airport”.
Ba da son ransa ba haka ya tashi ya saka riga a saman Singlet ɗin dake jikin sa, ya fito ya wuce ya shiga motar sa ya bar gidan, a cikin mota in banda tsaki da yake saki babu abinda yake yi, kaso mafi rinjaye na zuciyar sa yana ga Ɗahira, ya rasa meyasa zuciyar sa ta kasa nutsuwa da halin da ya saka ta, yana ji a jikin sa tabbas tana wani hali a sanadiyar Text ɗin da ya tura mata, amma ya zai yi? Bazai iya zuwa ya same ta ba, bazai iya jure ganin damuwa a kyakykyawar fuskar ta ba, ya gummaci ƙaurace mata har sanda komi zai dai-daita. Lumshe idanuwan sa yayi yana buɗe wa sai ga hawaye sun zubo masa a kunci, hannu ya saka ya share yana jan numfashi cike da takaicin Mahaifiyar sa, zuciyar sa sosai take mishi ƙunci fiye da tunanin mutum, yana ji a ransa bazai iya jure wa ba, bazai iya auren kowa ba face Ɗahira, dole ya sake yi wa mahaifiyar shi magana, ko zata iya tallafa wa rayuwar sa, Allah ya gani ba ya ƙaunar yarinyan nan da za’a liƙa masa, sannan kuma bazai iya zuwa ya tunkari wata ɗiya mace da sunan so ba, bare har ya iya auren ta, ita dai Ɗahiran da Hajja ba ta so ita zuciyar sa ke so..
Be fasa tunanin sa ba har sanda ya dangana ga airport ɗin, tunda ya faka motan ya hange ta, sabida kasancewar ta doguwar mace, idan har ta tsaya cikin mutane nan da nan ake iya gane ta, ga ta fara kuma tana ƙara wa dana kanti
Ya ɓata lokaci cikin motan kafin yaja numfashi ya buɗe ya fito, yana hangen ta sai faman waige-waige take yi tana duba agogon dake ɗaure a tsintsiyan hannun ta. Lumshe idanu yayi ya sake buɗe wa a kanta, kamar bazai taka ya isa wajen ta ba, sai kuma ya daure cike da baƙin ciki ya nufe ta, fuskar sa babu ko alamun walwala
Sai da ya dangana ga inda take tsaye, sannan ne ta hange sa, ai nan ta saki murmushin da ya bayyana haƙoran ta, wanda da gani kasan tana cikin tsantsan farin ciki, kiran sunan sa tayi tun kafin ya ƙariso
Sai ya kau da kai yana sake ciccin magani, ya tsaya cak a wajen
Ɗaukar jakar ta tayi ta nufo sa tana sake washe baki, tana iso wa wajen sa ta soma gaishe sa cike da fara’a, amma yanda ya amsa mata ne sai walwalan ta ya ragu
“But yaya lafiya dai ko?” Tayi masa tambayar tana kallon sa
Be ce mata komi ba ya juya ya nufi motar sa
Sai ta tsaya kawai tana kallon sa baki sake, duk da ta san ba ya son ta amma ai suna mutunci sosai ba kamar yanda ya nuna mata haka ba, “so what’s wrong with him?” Tayi wa kanta tambayar har yanzu tana tsaye a inda take. Sai da taji horn ɗin motan sa kafin ta ankara, taja akwatin ta ta nufi motan, buɗe bayan tayi ta saka akwatin kafin ta shiga gaban motan ya ja suka bar wajen.
A cikin motan ma babu abinda yace mata, duk da kuwa ta sake tambayar sa abinda ke damun sa, amma yayi mata banza, har suka kai gidan ya sauke ta yaja motar sa ya bar gidan
Tsaye tayi a wajen tana bin motar har ya ɓace wa ganin ta, sai kuma jiki a sanyaye taja Trolly ɗin ta tayi cikin gidan, duk wanda ta gani a hanya gaishe sa take yi har ta isa Part ɗin Hajja Fatu