FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

Horn tayi, me gadi ya leƙo, sai da ya zo wajen ta tayi masa bayanin kanta, kafin ya buɗe mata ta shiga ciki, tana yin parcking ta fito tayi cikin gidan

Tun daga haraban gidan komi ya burge Ɗahira, da ace ita baƙauyiya ce, ko ba su da shi a gidan su, da har zilalan yawu sai tayi lokacin da ta shiga parlour’n Yusra, sai dai kasancewar ta wayayyiya kuma masu shi, shiyasa sama-sama tayi ma komi kallo, a ranta kuma sosai komi ya bata sha’awa, tana ganin Yusra ta more da komi, domin tayi Sa’an muhalli.

        Fitowar wata babbar mace da kaya haɗin gambiza a jikin ta, ya tabbatar wa da Ɗahira ƴar aiki ce, a ranta tace, “su Yusra uwar son jiki! Har an soma ajiye ƴar aiki”.

Matar iso wa wajen ta tayi, ta zuƙuna har ƙasa ta soma gaishe ta

Saurin yalwata fuskar ta da fara’a Ɗahira tayi, tace da ita, “don Allah Mama ki tashi, Ni Yakamata in gaishe ki ai ba ke ba”.

Murmushi matar tayi tace, “ai babu damuwa ɗiyar albarka, idan na gaishe ki ma girman ki ne, don daga gani ke ƴar uwan matar gidan ce, kinga kuwa be kamata naƙi gaishe ki ba”.

Itama Ɗahiran murmushi tayi tace, “amma ai kin girme Ni Mama, don Allah kar ki sake zuƙuna min kinji? Ki ɗauke Ni tamkar ɗiyar ki”.

“To babu damuwa, insha Allahu. bari in Kira miki Hajiyan”. Matar tafaɗa da fara’a, a ranta sosai taji ƙaunar Ɗahira sabida mutunta ta da tayi, har tana jin da ita ce Uwar gidan nata.

     Har tayi nisa kuma ta juyo ta tambayi Ɗahiran “wa zata ce mata ta zo?”

Ɗahira ta sanar mata da sunan ta

Ita kuma ta juya ta shiga ciki.

     Kamar shuɗewar mintuna biyar sai ga ta ta dawo, tace mata “ga ta nan zuwa”

“To Mama na gode”. Ɗahira tafaɗa tana murmushi

Itama murmushin tayi tace, “babu damuwa ɗiyar albarka”.

Daga nan juya wa tayi taje ta kawo mata Drinks kamar yanda ta saba tarban baƙi idan sun zo, sai dai na Ɗahira har da abinci ta sawo mata, tunda tana ganin ita ɗin ƴar uwanta ce, be kamata ta tarbe ta da Drinks kaɗai ba, kuma abincin na Mijin ne tayi masa cus-cus, tunda shi ya fi so kuma yace ayi masa. To ta ga bata rigada ta sauke sauran abincin ba, shiyasa ta ɗibo mata nashi.

      Matan tana barin wajen, sai ga Sulaiman ɗin ya fito, da fara’an sa ya zauna suka gaisa da Ɗahira, har yana tsokanar ta da “sai yau za su ga idon ta, gaba ɗaya ita tayi wuyan gani, dole sai an cike Form me tsada ake iya ganin ta, da biki ma ko ganin ta be yi ba”

Ɗahira na murmushi tace dashi, “Allah Sarki Yaya Sulaiman, wlh ciwo nayi shiyasa kwata-kwata ban fita waje ba, kayi haƙuri”.

“Eyya Sorry! But ban ji labari ba ko kaɗan wlh, domin dai Yusra bata sanar min ba, ai da mun shiga mun gaishe ki, Allah ya ƙara lafiya, yasa kaffaran zunubai ne”.

“Amin Amin Yaya Sulaiman, na gode sosai”.

Murmushi yayi yace, “ki dena godiya Auntyn mu, mun rigada mun zama ɗaya Yanzu”.

Murmushi kaɗai tayi ita dai

Yace, “sai fa kin yi haƙuri da wannan ƙanwar taki, tana shirya wa ne amma yanzu zata fito”.

“A’a babu komi wlh”.

“To bari in ɗan fita waje, zan haɗu da Maƙoci na ne, idan ta fito ki ce mata yanzu zan dawo”.

Amsa mishi tayi cikin murmushin da ya zame mata jiki

Shi kuma ya tashi ya fice a Parlour’n

Ajiyan zuciya Ɗahira ta sauke, tana ɗauke kai daga hanyar da yabi, sai kuma ta kalli Centre table ɗin da me aiki ta shirya mata abinci da drinks, hannu ta sanya ta ɗauki Robbern fanta, ta buɗe ta tsiyaya a glass cup ta soma sha. Abu kamar wasa har tsawon mintuna 15 suka shuɗe babu Yusra babu dalilin ta, don haka ta zuba cus-cus ɗin ta soma ci, kasancewar sosai take jin yunwa

Tana cikin ci ne, sai Yusra ta fito cikin takun ta ɗai-ɗai tana faman taunan cwhingum

Da kallo Ɗahira tabi ta dashi tana mamakin ganin ta da Shimi da dogon wando, babu alamun dai shirya wa ne ya tsayar da ita, koda yake da ta tuna ba shiri suke yi ba, tasan komi zata iya mata, don haka ta tsayar da cin abincin da take yi tana kallon ta fuskar ta cike da fara’a, ganin yanda tayi mugun sauya mata, tamkar dai ba satin su biyu ne da aure ba, tabbas aure ni’ima ce, Allah yasa mu dace.

      Yusra dai tunda ta ƙariso wajen taga abincin da Ɗahira ke ci, sai ta sake ɗaure fuskar ta tamau fiye da yanda ta ɗaure, tana faman fiffizge kai tana taunan cwhengum ɗin ta har da su ƙas-ƙas-ƙas

Ɗahira ita ta soma mata magana, tare da gaishe ta cikin fara’a

Sai da ta zauna ta gama yamutsa fuskar ta kafin tace, “Lafiya. Dama ke ce?”

Murmushi Ɗahira tayi tace, “eh”.

“Yayi to”. Tafaɗa tana sake taɓe baki

Shiru ne ya biyo bayan maganar ta, don ita kanta Ɗahira bata san me zata ce ba, domin kawai yanda ta amshe ta ɗin, sai jikin ta duk yayi sanyi, tamkar ma ta ƙaro wulaƙanci ne, ga shi sai mata kallon banza take yi kamar dai ta ga kashi..

Numfashi taja sabida maganar Yusran da ya dawo da ita hayyacin ta

“Wai Husband ne yasa a kawo miki abincin nan?”

Shiru Ɗahira tayi tana kallon ta, don bata san me zata ce mata ba, tunda bata gane ma manufar ta ba

Guntun tsaki Yusran taja tana ɗaga murya ta soma kiran matar nan, “Marka.. Marka”.

“Na’am yallaɓiya, gani”. Cewar matar da ta fito da gudun ta

“Wa ya baki damar zuba mata abincin Husband?”

Shiru matar tayi tana zazzare ido, ta kalli Ɗahira ta kalli Yusran

Sai da ta daka mata tsawa da faɗin, “ba dake nake yi ba?”

“Kiyi haƙuri Ranki ya daɗe! Gani nayi ƴar uwan ki ce, shiyasa na zuba mata tunda yanzu na ɗaura sanwa, kuma zata…”

“Dalla rufe min baki”. Ta katse ta da faɗar haka

Jiki a sanyaye matar tayi shiru tana sad da kanta ƙasa, zuciyar ta cike fal da mamakin uwar ɗakin nata

“Wlh duk sanda kika sake ɗaukar abincin Miji na kika ba ma wata, a mean ba ita ba ko waye ma, wlh ranki sai ya ɓaci! baza ki sake zamar min a gida ba, ba na haɗa Miji na da ko wani tarkace kina ji ko?” Tayi maganar cikin isa da gadara

“Eh naji ranki ya daɗe! amma wai da naga ita ɗin…”

“Shut up I say”.

Gum Matar tayi jikin ta na rawa, sabida sosai tsawar ta ya shige ta

“Ki kwashe ki mayar min dashi kichen, idan kin girka wancan sai ki zubo mata”.

“To”. Matar ta amsa da sauri tana nufan Centre table ɗin, ta ɗauki Plate ɗin kacokan ta wuce kichen, zuciyar ta gaba ɗaya babu daɗi, sosai taji tausayin Ɗahira har tana sake waigo wa ta kalle ta da zata shiga kichen ɗin

Ɗahira na zaune dai tana kallon ikon Allah, har a ranta sosai da sosai abinda Yusra tayi mata ya bata mamaki da tsoro, “shin wani irin tsana ce take mata da har zata yi mummunan wulaƙanta ta haka? Tana a matsayin ƴar uwan ta?”. Sosai ta danne ɓacin ranta da komi, cikin juriya ta ƙirƙiro murmushi kafin tace, “Allah ya huci zuciyar ki! wlh nima bansan abincin Mijin ki bane, da ban ci ba”. Sai ta miƙe kafin taci gaba da faɗin, “Ni zan tafi, su Umma da Mama suna gaishe ki”. Ta ƙare maganar da yin gaba ta nufi ƙofar fita

Taɓe baki Yusra tayi tana faman kaɗa ƙafa, a fili ta furta, “dama ba gayyar ki nake yi ba”.

     Ɗahira na fita ta saka hannu ta share hawayen da suka zubo mata a fuska, ta saki wani irin numfashi tana jan majina, lumshe idanu tayi tana haɗiyar wani abu da ya tsaya mata a maƙoshi

“Lafiya Ɗahira? Why are you crying?” Cewar Sulaiman dake tsaye gaban ta ba tare da ta san da zuwan shi ba.
????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button