FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

“I don’t understand?” Ayush asked looking at her
“I mean. duk ta hanyar da za mu bi don hana yiwuwar hakan za mu yi, domin cin ma burin mu, ke dai kawai ki tabbatar kin samo yarinyan ko wace ce, a nan ne zan tabbatar miki da shirin mu a gaba, inyaso sai mu koma ga Malam ya saka mishi ƙaunar ki a zuciya”.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
AFTER TWO WEEKS
Gaba ɗaya ahalin gidan suna zaune a babban Parlourn gidan, yau har da Aunty Zulaiha da Aunty Zainab duk sun samu zuwa taron Familyn da suke gabatar wa a duk ƙarshen wata, haka ma Shakira da Yusra duk sun hallara, har Sa’adatu tana a cikin parlour’n, kasancewar itama yanzu ta zama ƴar gida
Abba ya soma buɗe taro da addu’a, inda Kaka ya bi su bayan ɗaya yana jin matsalolin su, tare da tambayar zaman nasu a gidajen mazajen su. sai da komi ya nitsa kafin ya kira sunan Usman
Usman dake zaune a gefen Baffa kan two seater, ya amsa mishi yana me ɗago kai ya kalle sa
“Ina muka kwana a zancen mu na auren ka?”
Dama ya san kwanan zancen, duk da an kwana biyu ba’a tayar da maganar ba, shiyasa ya sake ɗaure fuska, cike da isa yace, “har yanzu ban samu wacce tayi dai-dai da ra’ayi na ba Kaka, Ni a gani na gwara a dena zancen aure na yanzu, because I’m not ready to do it now.”
Big Dady ne yayi ninyan magana, sai Kaka ya katse masa hanzari da faɗin, “to shikenan, tunda baka shirya ba, ai mu mun shirya aurar da kai yanzu”. Sai ya juya ga Ɗahira yace, “What about the My wife? Are you still silent?”
Gyaɗa masa kai tayi kanta a ƙasa tana wasa da kwalliyan rigan ta
“To duk wani dama da Yakamata mu baku mun rigada mun baku, tunda har yanzu baku samo abokan zaman ku ba, mun yanke shawara Ni da iyayen ku, Kai Usman, da ke Ɗahira, za mu haɗa ku aure a tsakanin ku, ina fata dai…”
Zumbur Usman yayi ya miƙe yana dakatar da Kaka da faɗin, “haba Kaka! What are you saying? Dani da wa zaka haɗa aure?”
“Dan uban ka With you and your younger sister Ɗahira”. Cewar Big Dady yana tsare Usman ɗin da kallo
Huci Usman ɗin ya soma, kafin yace, “It is not possible at all. You must change your mind soon. I will never marry this girl.” Yana gama faɗa yayi hanya zai fice
Big Dady yace dashi, “Wlh if you go out, ranka zai ɓaci, come back and sit down, ka dawo nace ka zauna ko baka ji bane?”
Lumshe idanun sa yayi yana dakata wa daga inda yake, dunƙule hannun sa yayi yana faman huci, kafin kuma ya juya a zuciye ya dawo inda yake da zama ya koma ya zauna, gaba ɗaya fuskar sa ta haɗe tayi murtik, jira kawai yake yi ya amayar da abinda ke cikin sa.
Hannun ta da Kaka ya riƙo, shi ya dawo da ita hayyacin ta, ta ɗago kai tana kallon sa da idanun ta da suke zubar hawaye tun soma jin zancen Kaka
Hannun ta ya sake riƙe wa ƙam yana faɗin, “Nafeesa mene ne ya saka ki Kuka?”
Kasa magana tayi illa kallon sa da take yi, sai da taji saukar muryan Abbun ta ne kafin ta sake ƙifta ido tana mayar da idanun wajen sa, jin abinda yake cewa ya tabbatar mata ba mafarki take yi ba
“Sakarci ne irin nata, amma in ba sakarci ba meye na kuka a wannan maganar?” Ya ƙare maganar yana balla mata harara
Gaba ɗaya mutanen wajen, idan ka ɗauke Sa’adatu da tayi murnan jin zancen nan, sai kuma su Abba da su sun san da maganar, amma babu wanda haɗin nan yayi masa daɗi, musamman Hajja da take jin tamkar ta shaƙe Kaka da maganar ya fito daga bakin sa, baƙin cikin ta ma har ya fi na Hajiya da take uwar Usman ɗin
Ita kanta Aunty Amarya bata san meyasa ba, sam ta ji zuciyar ta ta karye da wannan haɗin, tana ji a ranta tabbas ɗiyar ta zata shiga wani hali a kan wannan auren, tamkar dai wani abu zai same ta, “shin sun manta da cewa Ɗahira da Usman ba sa shiri ne suke son haɗa su aure?” Tayi wa kanta tambayar a cikin ranta..
Muryan Big Dady ne duk ya dawo da kowa hayyacin sa, yace dasu, “mun tsayar da ranan auren nan da wata ɗaya me zuwa, don haka ban yarda ko inji ko in gani wani ya yi maganar akasin abinda muka faɗa ba, sai kowa ya soma shiri tun yanzu, za ku iya tafiya”.
Baffa ne ya riga kowa tashi ya bar parlour’n yana me riƙe da kansa
Da sauri Sa’adatu ta miƙe tabi bayan sa zuciyar ta fari karrr, ko ba komi tana gani an kawo mata ƙarshen matsalan ta
Ɗaya bayan ɗaya kowa ke tashi ya bar parlour’n, ban da Usman da Ɗahira da suke zaune tamkar an dasa su a wajen
Ganin haka yasa Aunty Amarya da zata wuce, ta nufi wajen ta ta ɗago ta, tare da riƙe mata hannu suka bar parlour’n
Shi kuwa Usman yana zaune ya haɗa kai da hannayen sa yana faman huci, gaba ɗaya idanun sa sun kaɗa sun yi jazur
Babu wanda ya kula shi a cikin su Abba, har sai da kowa ya watse, inda Abba ya gungura Kaka zuwa ɗakin sa, Big Dady na biye da su a baya yana amsa waya
While Abbu na zaune be tashi ba, sai da ya ga kowa ya bar parlour’n kafin ya miƙe ya iso gaban Usman, hannu ya saka ya dafa sa yana me kiran sunan sa
Ɗago jajayen idanun sa da har sun tara hawaye yayi, ya kai duban sa ga Abbu yana me taune haƙoran sa da ƙarfi, take jijiyoyin kansa suka fito raɗo-raɗo
Shi kansa Abbu jikin sa sai da yayi sanyi da yanayin da ya gansa, be iya ce masa komi ba illa kallon sa da yake yi
Hakan yasa Usman ya ɗauke idanun sa, yana miƙewa tsaye ya doshi ƙofa ya bar parlour’n
Da kallo Abbu ya bi shi da shi har ya fice, a ransa yana ayyana “shin wani irin tsana ne me ƙarfi da Usman yake yi wa ƴar sa? Anya baza su yi kuskure ba idan suka haɗa su Aure?” Babu me ba shi amsa, dole ya saki ajiyan zuciya ya juya ya nufi ɗakin Kaka ransa duk babu daɗi.
.
too chakwakiya … now the game will start … Just follow me to hear how it will go … Don’t forget your comments it will make me more typing.
????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????
????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????
MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL
بسم الله الرحمن الرحيم
⚖
FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓
JIKAR LAWALI CE✍️
Wattapad: UmmuDahirah????
\F.W.A????/
SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY
TUNATARWA
”’Manzon Allah ya ce mana, “tsabta kam ita ce rabin imani kuma ita ce mabuɗin Sallah. Abu na farko da ake buƙata kafin a shiga sallah shi ne tsarki, tsabta ta zuciya da jiki, ta tufafi da kuma wurin yin sallar.
Sallah ibada ce ta ruhu, kuma a cikin ta ne Bawa yake ganawa da Ubangijin sa, yake tsayawa a natse a gaban sa yana yabo yana godiya, yana roƙon Allah ya shiryar da shi bisa ga tafarki madaidaici. Saboda haka bai kamata Bawa ya shiga wannan ganawa ba sai bayan ya shirya kansa da kyau, ya tsarkake jikin sa da tufar sa da wurin sallar sa. Zai yi alwala in ƙaramin tsarki ya kama shi; in kuwa babban tsarki ne sai ya yi wanka don kuwa ta haka ne zai haɗa tsarkin jiki da na zuciya a lokacin ganawar sa da Ubangiji.
Allah yasa mu dace.”’
.
EPISODE Thirty Four
Direct Aunty Amarya ɗakin ta ta wuce da Ɗahira, suna shiga ta zaunar da ita kan kujera tana kiran sunan ta
Sai dai ga duk kan alamu Ɗahira tayi nisa a duniyar mu ba ta jin ta. Sai da ta saka hannu ta riƙo mata kai tana shafa mata fuska, kafin taja numfashi tana ware idanun ta da suka sauya launi a kan ta