FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

Ita kanta Aunty Amarya ta tsorata da yanayin kallon da take mata, shiyasa tayi saurin cewa, “Ɗahira Are you all right?” Ta ƙare maganar tana ɗan ƙara girgiza ta
Sai kawai gani tayi ta ƙame alamun ta sume idanun ta a buɗe, sosai hankalin Aunty Amarya ya tashi, babu shiri ta hau girgiza ta tana hawaye cike da ruɗu, sai kuma ta miƙe zata yi waje, har ta kai bakin ƙofa ta sake dawowa tayi cikin Toilet, domin tana ganin be kamata a san halin da ɗiyar ta take ciki ba, musamman yanda ta san ba ita kaɗai bace a sashin, yanzu sai aje ana yamaɗiɗi da maganar kuma ta daban
Ruwa ta ɗibo ta zo ta shafa mata a fuska, sai da tayi haka sau uku kafin Ɗahira ta farka, sai dai tana buɗe ido tayi arba da fuskar mahaifiyar ta sai ta fashe da kuka, nan da nan Aunty Amarya ta sake ruɗe wa, tayi saurin ajiye Cup ɗin hannun ta a ƙasa tana tambayar ta “what’s going on?”
Cikin kuka Ɗahira tace, “Mama don girman Allah kiyi min rai! idan har ba mafarki nake yi ba, ki taimake Ni ki je ki cewa su Abbu ba na son Ya Usman, wlh Mama Mutuwa zan yi idan na aure sa, Mama ba ya ƙauna ta ko kaɗan, Ni ba na son sa wlh bazan iya auren sa ba, ki taimaka min Mama, ki ce musu kar su haɗa mu, sam-sam ba mu dace ba Mama”. Sosai take kuka har da majinu
Riƙe ta Aunty Amarya tayi cike da tsantsan tausayin ta, cikin sanyin murya tace, “I don’t know what to say to you Ɗahira, amma abinda zai fito daga baki na be wuce haƙuri zan baki ba, kiyi haƙuri ki ɗauki ƙaddaran ki, tunda iyayen ki sun rigada sun yanke wannan hukuncin; ki daure kiyi musu biyayya kinji?”
Girgiza kanta ta soma yi tana ci gaba da zubar da hawaye, tace, “Mama ko kin manta da waye za’a haɗa aure na? Aure fa za’a haɗa Ni dashi, Yaya Usman da ya tsane Ni tun ina tsumman goyo na, yanzu shi ne zan aura a matsayin miji na? Please Mom help me I can’t marry him, I like Yaya Baffa .. “
Shigowar Abbu da sallaman sa, shi ya hana Aunty Amarya jin ƙarisan zancen nata, bare kuma dama tana kuka ne tana maganar, hakan yasa ba lallai ka fahimta ba. kallon sa kawai take yi bayan da ta amsa mishi sallaman nasa
Zuwa yayi ya zauna a kan hannun kujeran, inda suka saka Ɗahira a tsakiya dake faman kuka sosai, ta haɗa kanta da gwiwa tana ta rerewa, hannu yasa ya ɗago kanta yana kallon ta cike da tausayin ta yace, “Mama na, please stop crying. Stop kinji.. alfarma zan roƙa wajen ki, duk da na san ba kya son Usman, Amma Ina son ki amshi maganar nan hannu bibbiyu, kiyi mana biyayya kinji? Mu iyayen ki muka ga dacewan haɗa ku, abinda mun daɗe muna fatan haɗa zumunci, duk da bamu so mu yi wa ɗayan ku tilas ba, amma kuma ga shi mun aiwatar a kan ku, sakamakon rashin kawo naku zaɓin da baku yi ba, mu a ganin mu wannan haɗin da muka yi shi zai kawo daidaito a tsakanin ku, hakan ne ya ƙara bamu ƙwarin gwiwa, don Allah ɗiya ta ki daure ki amshi wannan haɗin da muka yi muku, ba na son ko kaɗan wani abu ya fito daga gare ki da sunan ɓata shirin iyayen ki kinji?”
Tsamm Aunty Amarya ta miƙe tayi hanyar waje tana me share hawayen tausayin ɗiyar ta, “kenan babu shakka dole sai an yi auren nan? Tana ji tana gani dole za’a ɗaura wa ɗiyar ta ƙwalli ɗaya wanda ba ta so” ba ma wannan ne matsalan ba, mutumin da ya fi tsanar ta da kowa shi zata aura, to taya zata ji daɗin rayuwa? gaskiya wannan abun da cutar wa ga ɗiyar ta
Da kallo Abbu ya bi ta dashi har ta fice, shi kansa ƙarfin hali yake yi domin babu yanda zai iya, wannan shawaran ba shi ne ya bayar ba, shi dai kawai ya bayar da yardan shi ne don biyayya ga mahaifin sa, amma yana ganin tabbas wannan haɗin akwai cuta wa ɗiyar sa, da yana da halin da zai samo mata wani, da tuni ya samo mata kafin hakan ta faru..
Numfashi yaja yana saka hannu ya ɗago kan Ɗahira da har yanzu take ta sharɓan kuka, kallon ta yake yi cike da tausayin ta yace, “yanzu shin Nafeesa ba mu isa kiyi mana biyayya bane?”
Ɗago jajayen idanun ta tayi tana kallon sa, cikin dauriya da cije kukan ta ta girgiza masa kai, sai dai tana son yin magana amma ta kasa
“But why don’t you accept the destiny God has chosen for you? Why not accept your parents’ choice?”
Shiru tayi tana shashsheƙan kuka, sai kuma daƙyar ta iya buɗe baki tace, “Abbu.. na.. na amin ce.. zan.. yi muku biya..yya”.
Yace, “Alhamdulillah, this is what I want to hear from you, insha Allahu baza kiyi dana-sani ba, kuma ko yaushe ke ce a sama in Allah ya yarda, albarkacin biyayyan nan da zaki yi mana, Allah zai daidaita tsakanin ku, zaku yi alfahari da junan ku, Allah ya miki albarka kinji? Share hawayen ki”. Ya ƙare maganar yana saka yatsun sa yana share mata
Itama hannun ta ta saka tana share wa
Yace da ita, “yanzu ga yi can ana kiran sallah, ki tashi ki je kiyi kinji? Kar kuma in dawo inga kina kukan nan kinji Mamana? ki sanya dangana a ranki”.
Ɗaga masa kai kawai tayi har ya fita bata ce komi ba, yana fita ta kwanta tana lumshe idanun ta tare da ci gaba da tsiyayar da hawaye
Yau wani irin baƙar rana ce a rayuwan ta da tazo mata? Ba ta jin zata iya kai wa zuwa anjima a yanda take ji, taya ma zata iya rayuwan aure da mutumin da tafi tsana a rayuwan ta? Sannan shima ya tsane ta fiye da kowa? Taya?
“Ya ilahi! Wannan wani irin mummunan ƙaddara ce ta zo min? God I beg you! If I am asleep, O God, wake me up quickly.” Ta ƙare maganar tana me fashewa da kuka, kukan da ke fitowa can cikin zuciyar ta, tare da saka mata raɗaɗi me zafi, babu wanda zai iya gane halin da take ciki, sai wanda ya tsinci kansa a irin wannan yanayin, tamkar dai ranta zai fita take ji sabida tsaban ƙunci da baƙin cikin dake tattare da ita.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
“I’m so happy Hajja wlh, Ni wannan haɗin da aka yi yayi min dai-dai, domin kuwa ta hakan ne Ɗahira zata ɗanɗani wulaƙanci a rayuwan ta, Ni na tabbata babu ta yanda za’a yi Ya Usman ya ƙaunace ta, I know Kare ma sai ya fi ta daraja a gidan shi”. Shakira ta ƙarisa maganar nata cike da farin ciki da ya nuna a fuskar ta
Cikin ɓacin rai Hajja ta kalle ta tace, “dalla rufe min baki, kin san kuwa abinda zai faru a wannan auren da kike murna? To bari kiji muddin ina numfashi sai na wargaza auren nan, Ni da nake neman hanyar da zan fitar da uwar ta gaba ɗaya a gidan, a’a sake neman gindin zama suke yi a gidan, tun farko a raina ke nayi Wa sha’awar auren Usman, amma hakan be faru ba..”
“Ni kuma Hajja?” Shakira ta faɗa tana me ƙwalalo ido waje tare da dafe ƙirji
Dogon tsaki Hajja taja tana cewa, “meye kuma haka?”
“Yo Hajja do you know what you are talking about? Ni fa kike wa fatan rayuwa da wancan miskilin mara mutunci? Ina sam.. Allah ya kyauta wlh, gwara ma da Allah yasa nayi aure na; ba Ni ce aka haɗa Ni dashi ba”.
Tashi Hajja tayi fuuu ta wuce ta bar Part ɗin, don sosai Shakiran ta ɓata mata rai
Ita kuwa Shakira taɓe baki tayi tana gyara zaman ta tace, “lallai kam Hajja ban san ba kya so na ba sai yanzu, ina Ni ina auren wannan mutumin? Kenan in ƙarike rayuwa ta a cikin uƙuba da rashin jin daɗin Rayuwa? Ina sam”. Sai kuma ta kwashe da dariya tana cewa, “ai wlh haɗin nan ya min daɗi, uhmmm ina tausaya miki Ɗahira, kin shiga bakin mayunwacin zaki, me fitar dake kuma ban ganshi ba, haka zaki dauwama kina me dana-sani a rayuwan ki”.