FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

Tana kwance ta ƙudundune cikin bargo sai rawan sanyi take yi, tun daga bakin ƙofa yana jin yanda haƙoran ta suke karkarwa
“Ya subhanallah..” Abbu ya faɗa yana zama bakin gadon, gaba ɗaya ya ruɗe da yanda ya ganta
Cikin sauri ya yaye bargon yana cewa, “Mamana kina jina?”
A lokacin ne ta buɗe idanun ta da suka kaɗa suka yi jazur ta sauke kan su daga Abbu har Aunty Amarya da ta shigo ɗakin a yanzu, sai hawaye take yi
Kallon sa Aunty Amarya tayi tace, “Abbun Zulaiha don Allah ka taimaki ɗiya ta, kana ganin yanda take yi ko? Shikenan ka ga zan rasa ta?” Tana maganar ne duk a rikice
Shi kansa Abbu tsaban tausayin Ɗahira ce ya kama shi, yace da Aunty Amarya “ta taimaka mata ta shirya ta su tafi asibiti, don be kamata su zauna a gida ba,” sannan ya tashi ya fice.
Kai tsaye asibiti suka wuce har da Aunty Amarya, inda tuni Umma ta je ta shafa wa mutanen gida halin da ake ciki, daga Hajja har Hajiya babu wanda ya damu, ita Hajiya ma ko a jikin ta, domin ta ɗanta take yi, tunda ya shige ɗaki a daren jiya ya ƙi fitowa, juyin duniya ta buga masa ƙofa ya buɗe amma ya ƙi, Usman da kwai kafaffiyan zuciya, idan yace ba ya son abu ba ya so ne kawai, idan kuma aka matsa mishi tabbas rayuka ne za su ɓaci.
⚫⚫⚫
Hajja kuwa shiri ma tayi ta wuce gidan ƙawar ta Hajiya Sa’ima.
“Ya na ganki duk a firgice ƙawata? Lafiya dai me ke faruwa?” Cewar Hajiya Sa’ima tana kallon Hajja da ta buga tagumi
“Hmm Ina fa lafiya? Wlh baƙin ciki ne yake son kashe ni a kan A’isha”.
Dariya Hajiya Sa’ima tayi tace, “wai ke kam har yanzu baza ki bar baiwar Allan nan ta huta ba? Ina ce yanzu Safiyya tayi auren ta har da yaran ta, kuma ke kanki kin fi kowa sanin tana jin daɗi a gidan mijin ta, to mene ne dole sai ta auri Mijin A’ishah?”
Hajja tace, “baza ki gane ba, wlh duk wanda yaci dani tuwo miya yasha, hankali na bazai taɓa kwanciya ba har sai na ƙuntata wa A’isha, sai na ɗaiɗaita ta sannan hankali na zai kwanta, buri na kawai yanzu in ga tabar gidan nan. Ba ma wannan ba, yanzu ta ɗiyar ta nake yi, kin san cewa yanzu za’a haɗa auren su da Usman?”
“Haba dai?” Cewar Hajiya Sa’ima tana kallon ta
“Wlh kuwa, ai tuni iyayen sun haɗa auren nan, kuma kin san halin Kaka, shi ya tsara wannan abun, sannan tunda yace za’a yi to tabbas sai anyi, tunda Ƴaƴan sa baza suyi masa musu ba, abinda yake so shi suke so”.
Cike da baƙin cikin jin zancen Hajiya Sa’aima tace, “to shi Usman ɗin yana son ta ne dama?”
Dayake itama tana wa ɗiyar ta kamun Usman, burin ta kenan ɗiyar ta ta shiga gidan, shiyasa maganar be mata daɗi ba
“Ki bari dai, Usman ba ya son ta, haka Hajiya ba ta son auren, tunda duk yanda zan yi nayi don ganin naga ta tsane ta, kuma buri na ya cika, yanzu abinda nake so shi ne tsayar da auren nan, ba zan taɓa bari ayi auren nan ba, gwara taje ta auri wani a waje hankali na zai fi kwanciya, da ace ta auri ɗan gida, hakan na nufin wata rana A’isha da ɗiyar ta…”. Sai tayi shiru saboda baƙin cikin abinda take son ƙarisawa
“Kin kawo kuka gidan da ya dace, ai tun farko abinda ya kamata kiyi kenan, ina da hanyar da zan taimaka miki wajen raba auren nan, akwai wani Malami a can hayin mu, wlh an bani labarin sa aikin sa kamar yankan wuƙa ne, ai kawai wajen sa zamu je ayi wa tufkar hanci”.
“Hajja tace, “ke Ni ban ƙi aje wajen duk wanda za’a je ba, koda Boka ne, in dai buri na zai cika, idan ba Allah ya tsare Ni ba, da tuni a kan ɗana baƙar ƙaddarar nan zata faɗa, da tuni Baffa zata aura”.
“Ke dan Allah?” Cewar Hajiya Sa’ima tana ƙwalalo ido waje
“Wlh kuwa, ke dai bari, A’isha gaba ɗaya ta gama siye ƴan gidan nan, asirin nata kuma so tayi ta mallake min ɗana, ɗiyar ta ta aure sa, amma sai da nayi da gaske sannan Baffa ya bar zancen, har yanzu kuma ba wai dena son ta yayi ba, sun rigada sun ba shi a ruwa ya sha”.
“Jar uba..! To wlh zama be kama ki ba Fatu, tashi mu je kawai, ai wani kissa duk da zaki yi yanzu bazai yi aiki ba, tunda itama a tsaye take, watarana ma yanda kike son ganin ta fice a gidan, ke zata fitar wlh, ai yanzu kai ya waye sai ana yi ana neman taimako wajen malamai”.
Hajiya Sa’ima tana yafa gyalen ta, suka fito suka hau motan Hajja Fatu suka bar gidan, suka nufi gidan Malam.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Yanda jikin Ɗahira yayi tsanani, dole aka bata gado
Su Big Dady duk hankalin su ya tashi da wannan ciwon na Ɗahira, sai dai babu wanda yayi yunƙurin sanar wa Kaka, kuma sai da suka kira gida suka yi musu gargaɗi
Duk kawaicin Aunty Amarya sai da tayi ta sharan hawaye a gaban su Big Dady, sosai hankalin ta ya tashi, musamman yanda wajen awanni biyu da kawo Ɗahira amma babu ci gaba, jikin ta sosai yayi zafi, suman da tayi kuwa babu iyaka, daƙyar aka samu numfashin ta ya dawo aka sanya mata oxygen, sannan aka saka mata ƙarin ruwa, zazzaɓin ne yayi mata mummunan kamu.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Su Hajja sun isa gidan Malam, inda suka samu ganin sa, sannan suka sanar masa abinda suke buƙata
Hajja ta so tace a hana auren ne, sai kuma taga idan tayi haka bata ci riba ba, sai tace a ƙara rura wutar ƙiyayyar da Usman yake yiwa Ɗahira, bayan an yi auren yayi mata sakin wulaƙanci tare da wulaƙanta rayuwan ta, sannan tana son itama Aunty Amarya tabar gidan, ayi mata saki kamar yanda za’a yi wa ɗiyar ta
Duk kuɗin da Malam ya buƙata, haka Hajja ta lale ta bashi, tunda tana da su, kuɗi ba matsala bace wurin ta, burin ta kawai haƙan ta ta cinma ruwa..
*
Su Big Dady ba su san takamaiman abinda ke damun Ɗahira ba, tunda daga Abbu har Aunty Amarya babu wanda ya faɗa musu, shi da kansa ma Abbun yayi mata gwaje-gwaje, inda ya gano damuwa ce ya haifar mata da wannan mugun zazzaɓin, kasancewar ta me raunin zuciya, wanda nan da nan damuwa yake kwantar da ita.
Sai da aka kwana biyu, lokacin har Ɗahira tana iya gane mutane, saboda zafin zazzaɓin ya sauka sosai, sannan ne aka sanar wa Kaka
Duk da haka sai da ya tashi hankalin sa matuƙa, sosai yake ƙaunar Ɗahira a cikin jikokin sa, shiyasa ko ya ya ne abu ya same ta, sai ya shiga tashin hankali matsananci
Yanda yaga jikin nata kuma da sauƙi, sai yaji ɗan dama-dama a zuciyar sa, ya tambaye su Abbu “ciwon me take yi?”
Abbu yace, “zazzaɓi ne kawai”.
Da haka aka ci gaba da kula da Ɗahira, kwanan ta biyar ta ƙara aka sallame ta. Koda suka dawo gida, daga Aunty Amarya har Abbu babu wanda yake barin ta ta zauna ita kaɗai, zaunar da ita Abbu yayi yayi mata nasiha sosai, wanda sosai ya ratsa jikin ta ainun, har tana jin zata iya yin musu biyayya, koda kuwa waye suka kawo gare ta, sai da Abbu ya sake yiwa Aunty Amarya kashedi, ta dena barin ta tana zama a ɗaki tana yin tunani, hakan zai saka damuwar nata yariƙa yawa har ya haifar mata da matsala, kuma ya hana ta zuwa aiki gaba ɗaya, yace “sai ta warke sosai”
Shiyasa koda yaushe tana ɗakin Aunty Amarya suna hira, ko tayi ta mata nasiha tana faɗa mata tayi ta roƙon Allah, idan Usman ba alkhairi bane a rayuwan ta, wlh Allah maji roƙon Bawa ne, kuma yana jin ta zai amsa mata