FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

Murmushi Dr. Sabo yayi yace, “tirƙashi akwai aiki kenan Dr.”.

Murmushi kawai Dr. Sa’id yayi, sai kuma yace, “baza ka gane bane. Let’s stop talking now, I will call her now nayi mata murna, yanzu sabon salon zai fara”.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

        Biki nata ƙarato wa, inda tuni an soma shirye-shirye ko ta wani ɓangare

Gefe ɗaya kuma Ɗahira har yanzu fama take yi da kanta, domin a tsaitsaye take rame wa sabida zullumi, ko yaushe ba ta jin daɗin jikin ta, yau ciwo gobe lafiya

Duk yanda Aunty Amarya tayi don ta kwantar mata da hankali, amma abun ya citura, ta kasa cire damuwa a ranta, gaba ɗaya ta rame sosai, sai haske da ta ƙara da girman idanu a waje, dama ba auki ne da ita ba, kamar ta karye take jin ta tsaban siranta, yanzu kuwa har tafi Da sirance wa

Har yanzu kuma bata koma bakin aikin ta ba, dole Abbu ya hana ta koma wa, tunda har yanzu ba ishashshen lafiya ne da ita ba, tarigada ta saka abun a ranta yana ta cutar da ita.

       Gefe ɗaya kuma Usman shima yana cikin tashin hankali, musamman da yaga auren yana ta ƙarato wa, tabbatan dole sai an yi, shiyasa gaba ɗaya ya shiga  damuwa tsantsa, ko abinci ba ya ci duk ya hana kansa sukuni, gaba ɗaya ma ya dena zama a gida, sai dare yake dawowa. duk yanda Hajiya tayi don ta samu ta kwantar masa da hankali, ya ƙi sauraron ta, shiyasa kullum ranan duniya sake jin tsanar Ɗahira take yi, ga shi ko gayya taƙi yi, ba ta shirin komi na bikin, duk yanda kuwa ta so da cin zaƙin bikin ɗan ta mafi soyuwa a ranta. A ganin ta baza ta iya taron biki tana murna ba, ɗan ta kuma yana cikin damuwa, ga shi Big Dady ko bi ta kansu ba ya yi, ya bar su ya zira musu ido daga ita har shi Usman ɗin, kuma ya hana su sake zuwar mishi da zancen.

                  ⚫⚫⚫

           ONE WEEK AGO

      Yau ma kamar kullum yana zaune a Office ɗin sa, ya haɗa kansa da table yana ta faman tunani, dama nan ne wajen zaman sa koda yaushe, tun safe idan ya zo ya rufe kansa a Office ɗin, sai dare yake koma wa gida.

    Nocking ɗin da aka yi masa, shi yasa ya buɗe jajayen idanun sa da suka kumbura ainun sabida rashin barci, da kuma ɓacin rai, be motsa ba har sai da yaga me Nocking ɗin ya dame sa, tsaki yaja yana ɗago kansa yabi ƙofan da kallo, gaba ɗaya fuskar sa ta gama haɗe wa tayi jazur sabida tsantsan damuwa, da gani kasan ba a cikin mood ɗin sa yake ba

Lumshe idanu yayi yana buɗe baki a hankali ya ba da iznin shigo wa, sai dai babu yanda za’a yi aji sa, dole ba don ya so ba ya sake ɗaga murya ya ba da iznin shigo wa

Wani staff ne ya shigo ciki, tare da gaishe sa cikin girmamawa

Sai dai yanda kasan kamar dutse haka Usman yayi banza da shi, illa rikitattun idanun sa da ya kafa masa

Duk ya ruɗe ɗan saurayin sabida Mayun idanun sa da ke kallon sa, ya matso yana miƙa masa envelope, sannan ya sanar masa, “wani ne yace a ba shi”

Be ce masa komi ba, yayi masa alamun ya ajiye masa

Ajiye masa yayi a saman table kamar yanda ya ba shi umarni, kafin ya fice da sauri

Da kallo Usman ya bi envelope ɗin da shi, yana mamakin mene ne a ciki? Da Kuma wanda ya aiko?

Tsaki yaja yana sake gyara zaman sa kan kujeran, ya saka white hand ɗin sa ya ɗauka ya soma buɗe wa, hotuna ne ya zaro guda biyar

Hoton farko dake saman sai da ya ɗauke numfashi na wucin gadi sabida munin hoton, Ɗahira ce kwance tsirara da wani ƙaton gardi suna manne da juna babu kaya suna aikata masha’a

Saurin lumshe idanun sa yayi yana jin wani tashin zuciya na son kama shi, take a nan ya saki sauran hotunan zuwa ƙasa ba tare da ya gani ba, sosai zuciyar sa take tafarfasa da abinda ya gani

“Yanzu wannan sheɗaniyar yarinyan karuwa, ita ce su Kaka za su aura min?” Yayi maganar a maƙoshi yana jin tamkar ya haɗiya zuciya ya mutu tsaban baƙin ciki

Hoton yabi da kallo daga ƙasa, sai yayi saurin kawar da kansa saboda ganin sauran da suka ninka wanda ya gani muni, kifa kansa kawai yayi a saman table ɗin yana riƙe da kansa dake faman sara masa, tuni idanun sa sun juye sun sake zama ja sabida tsaban ɓacin rai, a fili ya furta, “na tsane ki sosai fiye da komi dake duniyar nan! dama tun ba yau ba na rigada nayi tunanin hakan a Raina”. Sai yaja dogon tsaki yana tunanin yanda zai yi, “anya bazai ɗau hotunan ya nuna wa iyayen sa ba, wataƙil ma ya samu damar tsere wa auren?” Zuciyar sa ta raya masa hakan

Take kuwa ya saka hannu ya kwaso hotunan, ya mayar dasu cikin envelope ɗin, miƙe wa yayi tare da wayan sa a hannu da keey ɗin motan sa ya bar Office ɗin.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

         Tana kwance a saman gadon ta tayi samɓal da ƙafafuwan ta, sai ta kifa cikin ta ta tusa kanta ƙasan pilow, a hankali take fitar da numfashi ɗai-ɗai.

        Fadila ce ta turo ƙofan ta shigo da sallama a bakin ta, da kallo tabi Ɗahiran dashi har taƙariso bakin gadon tana zama tace, “Sister lafiya dai?”

Ɗahira da taji muryan Fadila tamkar daga sama, domin mugun tunani ta afka da gaba ɗaya ma ba ta cikin duniyar mu, da sauri ta zaro kanta dake ƙasan pilow tabi Fadila da kallo da manyan idanuwan ta da suka gama sauya kala suka yi jazur tamkar tayi kuka, ga shi sun faɗa sosai, hakan yasa idanuwan suka sake fito wa waje suka yi ƙwala-ƙwala

Nan da nan Fadila ta ruɗe da ganin ta a haka, tace,”lafiya Sis? what’s going on? What’s wrong with you looking at your eyes have changed color?”

Murmushin ƙarfin hali Ɗahira take yi, ta tashi zaune tana kallon ta da kyau, kafin tace, “nothing Sis, yaushe kika zo?”

“Ya zaki ce min babu komi? Kin kuwa ga yanda kika koma? Ciwo kika yi ne ko wani abun ke damun ki?” Fadila ta sake faɗa tana ƙare mata kallo, ganin yanda ta ƙara ƙarmashe wa sabida tsaban rama har ƙasusuwa ake gani ta wuyan ta

Stil dai murmushin tayi mata tace, “ciwo nayi Sister”.

“Amma shi ne baki sanar dani ba, babu wanda ya kira Ni ya faɗa min? tun yaushe kike ciwon ne da kika rame haka?”

Ɗahira dariya tayi me bayyana haƙora, wanda idan ka kalla kasan cewa na dole ne, tace, “kin sauya ƴar uwa, yau ke ce kike jero min waɗannan tambayoyin?”

Hararan ta Fadila tayi tace, “Seriously, it’s not a joke. I’m asking you ciwon meye kika yi ya mayar dake haka?”

“Hmmm ciwo ne kawai, zazzaɓi”.

Kallon ta Fadila tayi, sai tace, “ko dai kan maganar auren ki ne? Of course there is something going on. nayi mamakin jin cewa an haɗa ki da Ya Fodio, na kira wayan ki duk ba ta shiga, meyasa Sister kika yarda da auren nan tunda kin san ba kya son shi? In fact ma ba kwa shiri ke dashi?”

Shiru Ɗahira tayi bata ce komi ba

Fadila ta sake cewa, “I know wannan raman yana da nasaba da auren ki, ban ji daɗi ba gaskiya yanda na ganki haka..”

Shigowar Fadil ne yasa Fadila yin shiru, duk kan su suka bi shi da kallo har ya ƙariso ciki

Hannayen sa biyu cikin aljihun wandon sa yake kallon su yace, “Aunty Ɗahira Kaka na neman ki”. Sai kuma ya mayar da idanun sa kan Fadila yana dariyan tsokanan da zai mata yace, “ke kuma nan kika yo daga zuwa? ga shi can mijin ki na bilayin neman ki, ashe ke kin zo nan kin maƙale, halan kewar ɗakin kika..”

Bugun da ta kai masa ne, yasa shi guduwa ba tare da ya ƙarisa zancen nasa ba, sai da ya kai bakin ƙofan ɗakin yana dariya yace, “to ki dai fito ga shi can yana neman ki cwhengum ɗin naki, sai kace ba yanzu kuka rabu ba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button