FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Take faɗi kawai, while zuciyar ta tamkar ta fashe tsaban takaici
Da sauri ta ɗago kanta tana share hawayen fuskar ta, tuna wa da tayi a hanya take, kuma kowa zai iya ganin ta idan bata tashi ba. Miƙe wa tayi tana sake share hawayen ta, ta nufi Part ɗin su zuciyar ta cinkushe da baƙin ciki, har wani jiri-jiri take gani a hanya, Allah yasa babu kowa a parlour’n, sai tayi saurin shige wa ɗakin su, Toilet ta shige ta rufe kanta tasha kukan ta ma’ishi, sannan ta wanko fuskar ta tare da ɗauro alwala ta fito
Tana tayar da Sallah Fadila ta shigo ɗakin, dama kiran ta ta shigo yi don su ci abinci, tunda taga tana sallah sai ta koma.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Ɗakin sa ya wuce kai tsaye, ya faɗa kan gadon sa yana me lumshe ido, shi kaɗai yasan me yake ji a duniyar nan, da ba don kalaman Dadyn sa da yake tunawa ba, wlh da tuni sun neme sa sun rasa ya bar ƙasan, sai dai ya rigada yace masa, “muddin be bari an yi auren nan lafiya an gama lafiya ba, to wlh sai yayi dana-sani a rayuwan sa, domin wlh sai yayi mugun saɓa masa”.
Dogon tsaki yaja yana miƙe wa zaune, ya ɗauki envelope ɗin da ya ajiye sa saman drowern gadon sa tun dawowar sa, ciro wa yayi ya hau yaga hotunan ɗaya bayan ɗaya, zuciyar sa na ci gaba da tafarfasa tamkar zata ƙone, ko wani daƙiƙa sake jin tsanar Ɗahira yake yi, wanda ko ada be ji makamancin irin sa ba, a yanzu kuwa ji yake yi da za’a ba shi wuƙa ya yanka ta, sai yayi mata gutsi-gutsi yayi filla-filla da naman jikin ta
Yana gama wa ya kwashe ya zuba a basket ɗin dake bayan ƙofan sa, ya shige Toilet don yin alwala.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
A hankali gida ya soma cika da mutane, sabida ƙaratowar biki, ƴan uwan Aunty Amarya duk sun cika Part ɗin su tun ana saura kwana uku biki, dayake itama ƴar dangi ne babu laifi duk sun zo
Duk wani shiri da ake yi na Amare Ɗahira bata a ciki, su Fadila da su Firdausi, da sauran ƴan matan Familyn su suke yin komi, ita dai tana ɗaki sai dai ta ƙule taƙi fitowa, gaba ɗaya ma ba jin daɗin jikin ta take yi ba, saboda zazzaɓi da take fama da shi, shiyasa babu wanda ya takura mata, gyaran jiki ma tace “ba ta so” dole aka ƙyale ta, daƙyar ta bari ana gobe bikin aka yi mata saloon da lalle.
Washe gari 27 April 2021. Aka shaida ɗaurin auren DR. USMAN NOOR AL’AMEEN tare da Amaryan sa DR. NAFEESAT AL’AMEEN AL’AMEEN (ƊAHIRA). bikin da ya tara dubbannin jama’a, sai mu ce masha Allah
Daƙyar Usman ya halarci ɗaurin auren nan, ana gama wa aka neme sa aka rasa, dama be gayyaci kowa ba, bare abokan sa ma ba ƴan nan bane, sai dai wasu sun ji labari kuma sun halarta, sai dai shi be ma gansu ba ya arce.
Ana ta neman Ango an rasa, haka dai aka gama gaishe-gaishe ƴan uwa da abokan arziƙi aka soma watse wa.
Cikin gida ma ana ta shagulgulan biki, babu abinda za’a yi a bikin, tunda daga Amaryan har Angon babu me halarta, Ɗahira na fama da kanta, tunda tun sanda aka ɗaura auren jikin ta ya rikice, dole aka ɗaura mata drip aka yi mata alluran barci don zuciyar ta ya huta, dayake Abbu ne ya duba ta shiyasa ya gane damuwa ce kawai da yayi mata yawa
Lokacin da ta tashi har ɗakin ya shiga, ya zauna daga shi sai ita, yayi mata nasiha me ratsa zuciya, kuma ya roƙe ta “ta dena saka damuwa a ranta, ta riƙe auren ta da amana, tayi biyayyan aure”, nasiha sosai yayi mata wanda take ta faman kuka.
An rigada an shirya mata Part ɗin ta ya tsaru, dayake duk na gida ne, Big Dady da Abba suka ɗau nauyin yin mata komi, an shirya mata ɗakin ta irin na ƴan gata, komi sai dai ace Masha Allah.
Zuwa dare aka kai ta ɗakin auren ta, wanda tasha kuka ba Ni da kuka ba, aka watse aka bar ta ita kaɗai tunda baza a kwanan mata ba.
Sai da Big Dady ya kira wayan Usman ya shaida masa “muddin be kwana a gida ba tare da matan sa ba, sai ya saɓa masa”. Kuma ya basa umarnin yayi maza-maza ya dawo gare ta.
Be dawo gidan ba, sai ƙarfe 01:00am. Na dare. Lokacin tuni Ɗahira tayi barci abin ta, bayan ta gama kwankwaɗan kukan ta son ranta, wanda ya haddasa mata zazzafan zazzaɓi, daƙyar ma barcin ya kwashe ta tana ƙudundune a kan gadon ta.
.
to nan ake yin ta fa, ya zaman Ɗahira da Usman zai kaya? Wani irin zama za su yi a rayuwan auren su? Hmm ku dai gyara zama kawai Ni dai abinda zan ce muku kenan, yanzu ne za’a soma chakwakiyar.
????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????
????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????
MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL
بسم الله الرحمن الرحيم
⚖
FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓
JIKAR LAWALI CE✍️
Wattapad: UmmuDahirah????
\F.W.A????/
SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY
NATSUWA A SALLAH
Sallah babbar matsala ce. Ganawa ce tsakanin Bawa da mahaliccin sa, Ubangiji maɗaukakin sarki. Saboda haka ana buƙatar cikakkiyar natsuwa, a tattara hankali wuri ɗaya domin wannan ganawa ta musamman.
A cikin ayoyi biyun farko na suratul Mu’uminun ana faɗa mana cewa:
“Lalle ne, muminai sun sami babban rabo, wanɗanda suke a cikin sallar su masu tawali’u ne.”
Watau, Muminai wanɗanda idan sun tsaya yin Sallah sai gaɓoɓin su da zukatan su su natsu, babu wani abu mai shagaltar da su daga ambaton zatin Allah maɗaukakin sarki, to, irin su suke rabban ta. Natsuwa cikin sallah da ƙasƙan da kai ga Allah su ne alamun imani na gaskiya da Tauhidi tsantsa, don kuwa ko yaushe bawa yayi kusa da Ubangijin sa sai ya haɗa jin tsoron sa, musamman ma dai a sallah inda yake ganawa da shi, yake tunawa da girman sa. Allah yasa mu dace.
.
EPISODE Thirty Eight
WASHE GARI
Tunda aka yi sallan asuba Usman be dawo gidan ba, be kuma bari kowa ya gansa ba ya bar masallacin.
Ita kuwa Ɗahira tunda ta tashi tayi sallan asuba itama, ta sake komawa barcin, dayake akwai zazzaɓi a jikin ta shiyasa har gari yayi haske bata farka ba, sai da taji hayaniyan ƴan biki da wasu suka zo su sake ganin ɗakin nata, kasancewar a lokacin za su tafi, shi ne ta farka, lokacin 12:00pm.
Har ciki suka shiga suna ta mata tsiya, ganin ta da suka yi tana ta barci
Ita dai bata ce musu kanzil ba, illa murmushi da take tayi, sai kuma daga baya ta gaishe su.
Ba su wani jima ba suka yi mata sallama suka tafi.
Sake koma wa tayi ta kwanta, don sosai kanta yake sara mata sakamakon tashin ta da suka yi, ta rufe ido kenan taji an hankaɗo mata ƙofan ɗaki, da sauri ta buɗe idanun ta tana bin Yusra da ta shigo da kallo
Ita kuwa sai faman taɓe baki take yi tana girgiza jiki, sai kuma ta mayar da idanun ta kan Ɗahiran tace, “baƙar munafuka! burin ki ya cika kin auran min Yaya, to wlh ki saka a ranki, kamar auren nan ya rabu ne, ba ke ba zama a gidan Yaya Usman, domin ba ya ƙaunar ki, ba kuma zai taɓa ƙaunar ki ba, wlh dani dake yanzu ma muka soma ƴar tsama”.