FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL 1

Kai tsaye ɗaki ta wuce sanda Abba ya sanar mata a parlour ya fice, wayan ta ta ɗauka jiki na rawa ta kira Ƙawar ta Hajiya Sa’ima, nan take shaida mata abinda ke faruwa
Itama Hajiya Sa’ima baƙin ciki kamar ya karta, ta ma kasa yin magana
Hajja Fatu tace, “yanzu ji be abinda ke faruwa, mu da muka je neman taimako waje Malam ya hautsina musu zaman auren, daga ƙarshe ya yi mata sakin wulaƙanci, amma kin ga sakamakon tafiya ma suka yi, ta ya idan ya tsane ta daga yin aure zai ɗauke ta wai fita hutun amarci, anya kina ganin aikin Malamin nan yana ci? Ki duba fa ki gani, ita kanta Mahaifiyar ta da na saka ayi min aiki a kanta, shiru kake ji babu wani hayaniya a tsakanin su da zai nuna min suna faɗa”.
Ajiyan zuciya Hajiya Sa’ima ta sauke, kana tace, “Wlh nima abinda nake tunani kenan, amma kuma Wlh Ni na yarda da aikin Malamin nan tabbas yana ci, sai dai kuma idan akwai maƙarƙashiya ce, ke da kanki kin ce itama uwar ba zaune take ba, to kin ga baza muyi mamaki ba da abinda za mu gani, amma Ni nan nake ganin aikin Malam, duk da Ni ban taɓa zuwa wajen sa ba sai a wannan lokacin, ƙawata da nake raka wa ina ganin yanda take watayawa a gidan mijin ta, kuma kin san kishiya ce da ita, amma yanzu tuni ta bar gidan duk sabida aikin da Malam yayi mata, yanzu ita take juya gidan, duk abinda tace shi Mijin nata yake yi”.
“To yanzu ya kike ganin zamu yi?”
“Ai zama be gan mu ba, koma mishi zamu yi, idan ma akwai matsala a sake sabon aiki, domin muddin kika zauna ke ruwa sai sha”.
Hajja Fatu tace, “haka ne. Amma ki bari zuwa gobe idan na fito aiki sai mu je”.
“To shikenan Allah ya kai mu rai da lafiya”.
Da haka sukai sallama. Inda Hajja Fatu ta miƙe ta nufi sashin Hajiya don sake jin ƙwaƙwaf tare da zigin da ta saba.
Oh Allah ya raba mu da halin Hajja Fatu, HASSADA mugun ciwo.
*
Hajiya Sa’ima kallon ɗiyar ta Zeena tayi, tace, “kin gani ko? Dama nace zata kira Ni, amma kuma maganar tafiyan nan nasu ya girgiza Ni fa”.
“Hmm Mama ke ya girgiza ko Ni? Wlh baki ji yanda ƙirji na yake suya ba da jin zancen”. Cewar Zeena tana kumbura fuska kamar zata yi kuka
“To ki kwantar da hankalin ki, ai yanzu za’a sake sabon aiki, kin ga mun yi da Malam dama in sake karkato ta ta dawo, to ga shi ita da kanta ta neme Ni, duk kuɗin da zata bayar ayi wa uwar aiki, sai a mayar dashi kanki, zai miki aikin da shi da kanshi Usman ɗin sai ya zo ya duƙa yana kuka ki aure sa, ita kuma matsiyaciyar can (tana nufin Ɗahira) watan wahalan ta ne ya kama, da ƙafan ta zata gudo saboda azaba, daga nan kin ga shikenan tana dawowa iyayen suka san halin da ake ciki za su ce ya sake ta, kin ga burin mu ya cika, da zaran ya sake ta ke kuma zaki bayyana a wajen sa kamar yanda Malam yace, faƙaɗ”.
Dariya Zeena ta saki tace, “Wow har kin sa naji Daɗi Mama, Wlh ina mugun son Bawan Allan nan, muddin ban aure sa ba to mutuwa zan yi”.
“Ba ma za’a kai da haka ba ɗiya ta, aure babu fashi dake dashi, idan har Ni mahaifiyar ki ce, to, Wlh ko zan yi yawo tsirara ne sai na cika miki burin ki. Ke kaɗai ce fa dani, idan ban miki ba wa zan ma?”
Farin ciki ne sosai ya cika Zeena, tana ji a ranta da kalaman Maman ta tamkar ta cika burin ta ne, “waiii! Wa ya ganta gidan Dr. Usman Noor Al’ameen, a gaskiya sai ta zuba ruwa a ƙasa tasha ranan don murna. Hohoho!”.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Itama Ayush ta shiga tashin hankali jin labarin tafiyan su Usman wani ƙasa, su da suke burin raba auren don me zai tafi ya ɓata musu aiki? Ga shi ba su ji sakamako ba a kan Hotunan da suka tura masa, duk da suna kyautata zaton aikin su yana yi, amma kuma tafiyan nan ya rusa mata gaba ɗaya lissafin ta, dole ta nemo Safra ta sanar mata komi
Itama kanta Safran abun ya girgiza ta, domin tun sanda suka biya wani saurayi yayi musu aikin haɗa hoton nan suka aika, sai ta koma Zaria school ɗin ta, shiyasa bata san wainar da ake toya wa ba, duk da suna waya da Ayush ɗin, but bata taɓa tunanin shirin su zai ƙi tasiri a ƙanƙanin lokaci ba, ga shi kuma tsaban rashin samun nasara har tafiya suka yi tare, a ranta tana tunani “an ya ma Usman ɗin ya buɗe hotunan ya gani?” Domin ta tabbatar babu namijin da zai ga matar da zai aura a wannan mummunan yanayin be rabu da ita ba, ko da son ta shi ne ajalin sa ƙariƙon mamaye masa zuciya.
Ce ma Ayush ɗin tayi, “ta shirya idan ta samu lokaci ta zo Zarian su je wajen Malamin, tunda dama ce musu yayi “idan aka yi auren alokacin ne zai raba, ita kuma Ayush ta shiga”. To yanzu tunda aikin su be yi ba za su koma masa, da fari ma ya soma saka soyayyar Ayush ɗin a zuciya tun wuri Usman ɗin ya san da ita, kafin a raba auren.
Washe gari Ayush shiri tayi da wuri ta wuce Zaria, domin ko wajen aiki ba ta jin zata iya zuwa idan bata je ta san matsayan ta ba.
Koda ta sauka masaukin Safra, sai da ta huta taci abinci sannan suka ɗauki hanyar da zata fito da su Zaria, daga nan kuma suka karya kwana har zuwa gidan Malam
Suna isa bakin Bukkan yayi musu iso zuwa ciki. Bayan sun zauna sun kai gaisuwa wajen sa
Ya amsa yana bin su da kallo, sai yace, “kun dawo kenan?”
“Eh Malam.. yanzu aikin muke so sosai Malam, Dan Allah ko nawa ne zamu biya domin kayi mana aikin me kyau”. Cewar Ayush cikin damuwa
Dariya ya saki yace, “kee yarinya dama wa yace miki ba na aiki da kyau? Ki ajiye kalaman ki wataƙil zai miki amfani a can gaba amma ba anan ba”.
“Ran Malam ya huce”. Cewar Safra tana ɗaga masa hannu alamun jinjina
Be ce komi ba ya soma musu aiki, sai can kamar mintuna 20 ya dube su yace, “ina ga aikin nan fa yana da sauƙi a waje na, amma a wajen ki yana da wuya, idan kuma kika aiwatar da abinda nace miki; tamkar shan ruwa ne zaki same shi”. Sai ya ja numfashi yana miƙo mata wani baƙin kwalba, sannan yaci gaba da cewa, ” riƙe wannan zaki je ki zuba jinin farkon saduwa dake da za’a yi, idan kin zuba sai ki nemi gashin kansa da naki sili ɗaya kacal, ki ɗaure su waje ɗaya, sannan ki saka shi cikin jinin, idan kika yi haka to sai ki dawo min da kwalban, Ni kuma zan saka aljanu su kai min tsaunin da mutane ma ba sa shiga, za su birne shi a ƙasan teku. Daga ranan babu wata mace da zai taɓa so idan ba ke ba, ke har mahaifiyar shi sai da amincewar ki zai nuna mata so, ke kaɗai zai ƙaunata kamar hauka, kuma daga ƙarshe Son ki shi ne ajalin shi. batun kuma rabuwa da matar sa, da zaran kin aikata abinda nace auren su zai warware”. Hhhhh ya ƙare maganar yana ɓaɓɓaka wani mahaukacin dariya
Daga Ayush har Safra tsimi suka yi suna kallon sa, babu wacce tafi ruɗe wa sama da Ayush, domin kalaman Malamin ba kaɗan ba ya gama hautsina ta
Safra tace, “amma Malam kamar ya ka ce “Son ta zai zame mishi ajali?”
Dariyan ya kuma saki, kafin yace, “ki adana kalaman ki har sai kin ga irin mahaukacin ƙaunar da zai mata, a nan ne zaki gane tabbas son ta shi ne zai zamo ajalin sa”. Ya ƙare maganar yana ci gaba da dariyan sa
Sai alokacin Ayush ta ɗan ƙifta idanu, kamar ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, cikin rashin kuzari tace, “amma ban gane ba Malam, idan mun yi aure da shi ne zan samu jinin bayan ya kusance Ni Ko kuwa?”