KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Dan Allah ni ka matsa mutum sai shegiyar mayata Wai……..

Hankadeta yayi hakan yasa bata karasa fadar abinda tayi niyan fada ba sannan ta dubesa aiko hatta jijiyoyin kansa sun tashi saboda Bacin rai .

Kofa kawai ya nuna mata Da hannu danshi kanshi tsoran motsi yake dan gani yake babu abinda zai hanashi yiwa zakiyya dukan kawo wuka a darennan.

Zakiyya na ganin haka tasan ta kwabsa domin ko ta bata masa rai Wanda hakan ke nufin bazai hukunta minal Ba tunda dama ta bada Kaine saboda taci uban minal gobe never the less she enjoyed it.
Aiko dole ta gyara kafin reshe ya juyewa mujiya, matsowa tayi kuwa dashi yace out,tace bab….

Kofa ya nuna mata tare da maimaita mata Cewa tabar masa daki rungumosa tayi yace ke banson iskanci meye hakan? tace ban koshi bane .
Wani harara ya watsa mata irin me kika mayar dani kamin ya yakiceta ya fada bathroom yana mai jin zafin hali irin na zakiyya Sam Daga bukatarta ta biya to shikenan shikam ko oho
Son kai yayi mata yawa…….. Haka ya dinga sake sakensa yayi wanka tare da wankan tsarki sannan ya fito

Koda ya fito Bai sameta Ba Dan haka ya Shirya abinsa yayi kwanciyarsa zuciyarsa cunkushe ga kuma wutar déjà vu dake addabarsa yanajin Kamar zaiyi hauka.
Bashi yayi bacci Ba sai wajen 2:30 domin juye juye yaketayi dayaga babu sarki sai Allah kawai sai ya fara kuka hawaye nabin kuncinsa ga wani mugu Abu mai zafi daya tsaya masa a zuciya gameda abinda zakiyya keyi masa.

Abangaren minal kuwa kwashe ceramic din take tana kukan takaici da bakin ciki ita yanxu a haka zata karashe rayuwarta cikin bauta?Allah ka kawomin dauki shine abinda take fadi tana gama kwashewa ta zubar ta gyara wajen sannan ta tafi dakinta wanka ta Shiga ta Dade Kamar yadda ta saba(ko me takeyi oho muje zuwa daganan zamu gano)

Fitowa tayi sannan ta tsaya a gaban madubinta taci gaba da abinda take yi a bandaki kullum tun tana gida har ya zame mata jiki in batayiba batajin dadi.

Bayan ta gama Shirye shiryenta tayi alwala sannan ta kwanta tana mai nazarin rayuwarta

Zakiyya ko koda taje dakin ta Fadawa gadonta tayi tana mai tsaki kana tace kaika sani Idan jarabarka ta matso ka zama kazo ne sannan ta bingire da bacci Ba tare da tayi ko tsarki Ba balle wankan tsarki ko makamancinsa(uhm Allah kyauta)

MORNING

Yau kam minal sai 7 tukunna ta fito yin aikinta Wanda takeyinsa bisa kwarewa bayan ta kammala ta Koma daki tayi wanka ta Shirya cikin atampa blue mai mai circle yellow sannan ta zauna a kan kujera tunda batada right din zama a gado tana karanta wasikar jaki.

Banko kofar dakinta taji Anyi take jikinta ya dauki rawa domin tasan cikin biyu daya ne ko mijin ko matar sa

Aiko yazeed ne yana wani yatsine fiska Kamar yaga kashi sannan yace wato ke gaki hamshakiya ko in bada umarni ki take
Sai yayi murmushin gefen baki to ai shikenan kinga ko Ba Komai zaki ragewa washing machine dina aiki Wanda ke nufin bill din nepa da kuma kudin gas zai ragu domin Daga yanxu  ke zaki dinga wankemin singlets and boxers dina Mara mutunci gold digger kawai.(uhm yazeed kenan sai kace kuddin bill din wani Abu yaje rage masa)
Zaki tashi kije dakina ki dibo su yanzu ko sai na wanke miki wannan shegiyar fiskannaki da tafi
Jiki na rawa ta mike zata fita yace “hold on! dakata” ta jiyo wannan karan ranta adan bace
Yace ya zama dole kibi umarnin matata

Batasan lokacin da tayi kicin kicin da ido tace wallah nanne kuma kayi karya na rantse……

Aguje ta fice domin yunkurin da yazeed yayi zai kamota ya gwabe bakin da Kamar zai bita sai ya Fasa ya nufi dinning area yana mamaki Wai yarinyarnan ce ke masa irin wannan rainin wayon da fitsara?

Zuciyarsa ce tace masa what do you expect from a ghetto girl like her?inbatayi fitsara bama sai Allah ya tambayeta(fadi Gaskiya babana?

Dinning room ya Shiga abinshi ya hada tea yasha tare da cin plantain baifi 5 slice ba Sannan ya wuce gym room dinsa.

Minal ko data dauko kayan wankesu tayi tas  sannan ta shanya sannan ta koma ta nemi abinci taci

Zata koma dakinta taji ance ke!..ke!..ke! asararriyar baiwa zonan juyowa minal tayi a hasale kawai sai kalaman yazeed ya fado mata

Wani irin kallo takeyiwa zakiyya at any moment zata iya mata illa zakiyya ko dukda tana shakkun captain yayiwa minal din magana ko baiyiba amma bazata barta taci banza Ba

Zaki rama ne? Shiru minal tayi, zakiyya ta tabe baki kana tace zokiyi min tausa
Wani harara ta rafkawa zakiyyan aranta tace wallahi baki isa Ba saide mijinki ya kasheni
tasowa zakiyya tayi tana nufo minal domin dauketa da tafi minal ko rayawa take aranta irin rashin mutuncin da zata antayawa zakiyya Idan ta tabata Dan ita Ba jaka bace

Yazeed ne ya shigo cikin isa fiskannan Kamar bakin hadirin daya taso Daga yamma kamshin Cologne din da yakeyi ne ya Sanar da minal isowarsa

Atake kirjin minal din ya buga kana tsoro ya shigeta amma kunsanta da taurin kai bata nuna Ba saide tanaji jikinta har makarkata yakeyi

Wajen su ya iso ya watsawa zakiyya kallon me kikeyi Anan?tsaki taja ta wuce koda ya juyo ganin Inda minal ke tsaye  yaga empty,ta arce.

Zakiyya kam ficewa tayi Daga gidan tana Cewa malam sule idan ya dauko yaranta kar ya kaisu gida ya Kaisu su siyo cup cakes kamin ya kawosu boutique dinta Kamar yadda ya saba

Yace to hajiya Insha Allah ta wuce abinta ta shige cikin 4matic dinta ta wuce .

Don’t forget to vote,share and comment pleeease because that is the only way zan gane yadda kukeson novel din.

Taku for life;karamarsu babbarsu wato

Miss untichlobanty💕

13th October, 2019.

🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹@mzz_untichlobanty🌹

CHAPTER 32

Sama ya haura direct dakin minal ya Shiga ya sameta tana ajiyar zuciya yace follow me !

Ta dago idanunta ta kallesa domin neman karin bayani wani electric shock sukaji dukkansu biyu kamin ya waske ta hanyar Cewa ko bazaki iya zuwa bane kin kafeni da inu munafuka?

Shiru still tayi ya fice itama ta bisa subul subul tana mai gyara zaman yellow hijabinta
Koda ta shigo dakin akan coach ta samesa zaune ya daura daya akan daya yace bazaki iya karasowa bane?
Ahankali ta tako a tsure dukda bata bayyana hakan Ba ta tsaya a Dan gefensa
Yace closer tare da mata alamu da hannu ta Dan kara matsowa harara ya buga mata tare da Cewa cinyeki zanyi ta girgiza kai tana mai karasowa da Dan Sauri tsayuwa tayi a kansa
Ya kamo bakin hijabinta ya janyota kasa
Dan kara ta saki domin hijabin ya Dan kurji gefen wuyanta kana visa kuskure ta Dan taka kafarsa kamin ta zube,yace Dan kaniyarki haka zaki tsaya akan yayanki ta girgiza kai yace bakida baki ne tace a’a

Harara ya kwada mata yana mai hadawa da rakwashi kwas a tsakiyar kanta yace bakisan in antaka mutum hakuri ake basa Ba?girgiza kai tayi alamu tasani tana rarraba idanu Dan rankwashin ya shigeta

Janyota yayi ya matse cute pinky lips dinta  yana kalla yace wato gani sarkin mahaukata ko ina magana kin bawa banza ajiyata

A hankali hannunta na rawa ta daura akan nashi alamun ya sake bakin zatayi magana idanunta ko ya cicciko da hawaye saboda radadin da bakinta ke mata shikuwa wani yaaaam yaji Ba shiri ya saki bakin kana ya kauda kansa gefe domin jin bananarsa na kokarin kawo masa raini

Ahankali cike da in’ina tace kayi hakuri na taka ka,tsika jikinsa suka mike gabadaya yayinda hawayen da taketa boyewa ya samu nasarar saukowa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button