KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Baby dole fa mu Shirya aminanmu kinga dai yadda suke fada. Gyada kai tayi suka cigaba da lekensu dai dai lokacin su zalihan suka fadi murmushi yazeed ya sakarwa minal tare da pecking gefen wuyanta.
Kallon kallo su lukman suka tsayayi kamin zaliha yaja tsaki ta hankadeshi tare da fadin dalla malan Daga ni.
Tashi yayi cikin borin kunya yace sekace wani abar zanji a kashinnan. Murkuda baki tayi tace a hakan dai aka danneni aikin banza dadai lokacin lukman ya lura dasu yazeed Dan shi yake facing kofa hakan yasa ya janyota ya rungume ta kam yana shinshinanta Kamar romance suke Dan a tunaninshi lokacin su yazeed suka zo ganin zata kwace yasa ya kara kankameta abinda be saniba kuwa zaliha wani Yan ayi ta fara Shiga saboda margin sha’awarta Dan har tafi minal dukda minal dinma ba’a barta a bata ba.
A kunnenta ya rada mata su yazeed Suna kallon mu so act.
Jikinta ya sake Dan haka ta kasa reacting ma balle ta masa taurin kai ko ta bijire.
Sakan jikinta tayi tare da kamo fuskarsa ta fara kokarin sunbatarsa Dan tama manta Waye a wajen.
Minal ne ta kwalka ihu a take suka zabura hard a yazeed Wanda ya shagala da kamshin jikin minal din.
Yace minene? Tace cinnaka ne ta cijeni janyeta yayi suka bar wajen Inda aka bar zaliha da borin kunya tsaki taja tare da fadin Dan iska kawai biyota yayi ta fice a guje yace zan kamaki yar renin hankali kuma tare zamu tafi gida.
Juyowa tayi tace me ? Yace kwarai tace kana nufin yau zan tare yace tarewan ma taci ub*nsa daganan sai gidana kimaji da Wai.
Tattarowa sukayi suka Koma gida bayan sunyiwa su ummi sallama mom sai dadin ganin yanda yazeed dinta ya canja take. Ya Koma ainihin yazeed dinsa me faran faran kamin rasuwar dad dinsa.
Godiya dubu ga dunbin masoya na da kuma masu sharing littafinnan Allah ya saka muku
WANNAN PAGE NA SADAUKAR DASHI GA FANS DINA BAKI DAYA
INA KAUNARKU SOSAI! TAKUCE KARAMARSU BABBARSU.
Miss untichlobanty?
12 January, 2020
??KURUCIYAR MINAL??
?by miss untichlobanty?
?CHAPTER 64?
Koda suka shigo gidan zaliha na kokarin fita Daga motan luku ya riko hannunta kyam wani yar sukaji amma bai saka ba saima harara daya banka mata. Kiciniyar takeson masa ya mata rikon maza mom Suna fita ya zama saura su biyu ya lafta lock. Wancalar da hannunta yayi yace Menene ma wannan tsiyar hannun naki Kamar muruci? Tsaki taja tareda fadin dalla malam budemin mota na fita.
Banson wulakanci baza’a kwana a gidan naka ba ana dole ne?
Take motar yayi Wanda yayi sanadiyyar da yasa zaliha fasa baki tare da Kwandale kai a window kicin kicin tayi da ido kamin tace kane bala’i na rantse da Girman wallahi Bashi Idan ba saina rama ba me nake.
Daidai lokacin suka iso Dan haka ya fice yana fito kallon part dinsu zaliha ta tsaya yi ba karya ya hadu. Ko nasu minal saide ya Nuna musu girma da tsadan kayan furniture amma saboda hali irin nata tabe Baki tayi tare da fadin saboda wannan tsiyar gidan aka raboni Dana iyayena.
Shrugging yayi yace Aike rayuwarki tsiya tsiya ne iyayenki ne kawai na arziki.
Tsabar tsiya sadakarki aka bani kuma na kawoki matsiyacin gida zaki kare matsiyacin rayuwarki acikinsa tareda matsiyacin mijinki. Ya fadi hakan yana mai mata murmushi.
Iya shaka kam ta shaka kuka ta fara tare da fadin Allah ya isa na nikam an cuceni wallahi da aurenka gara Lauren kolo. Wannanta wuce bazar bazar ta mangajeshi ta fada wani Daki yace jeki dama nanne dakinki. Leka dakin yayi ya ganta kwance kan gado tana kuka yace my wife dagowa tayi tana aiko masa wani harara kiss yayi blowing? Mata tare da cewa kayanki na wardrobe ayi kuka lafiya sannan ya fashe da dariya. Tasowa tayi kamar zakanya. Yayi saurin rufe Mata kofa dadai zai fita daga side dinsu yaga minal tana shirin shigowa hannunta rike da sahir da safwan….
????????
Su minal suna Shiga gidan su suka labe suna kallon abinda su zaliha keyi dafe kai yazeed yayi yace gosh wai ace bazasu taba yin shiri ba ? Dole ne mu hada kansu. Miko Mata hannu yayi yace plan karba tayi sukayi musabaha tace yes plan.
Daughter! Daughter! Mom ke kwalawa minal Kira tana fadin zoo ki tayani kunce kayana in baki tsarabarki. Zata tafi yazeed yayi saurin rokita kamin tace mom zatazo anjima yanzu ina bukatar matata.
Lekowa tayi ta sama tace iyeeee mai mata manya. Umm Nide kada ka riketa dayawa yafi awa daya Dan yunwa mukeji kuma abincinta mukeso. Zaro ido yayi yace mom bafa haka nake nufi ba magana zamuyi fa sai in danji duminta. Dariya mom tayi tace zama kayi bayani Nide na fada maka.
Sannan ta Koma tana mai jinjina halin rashin kunyan yazeed don atunaninta wani abar za’ayi.
Yazeed ko minal yaja zuwa kitchen wadda duk kunya ya rufeta saboda ganin da mom ke mata.
Fuskar yara ya mata yace babe kiyimana pancake dinki muci please.
Gyada kai tayi ta fara hado abubuwa sai murmushin jin kunya take yazeed ko daya hau kan island ya zauna tareda dauko wayarsa yanata daukar? hotonta tana aiki saide duka fuskarta bai fito ba.
Ajiyan zuciya yake sauke wa yawunshi har tsinkewa yake yace kai nikam ataimaka min na fara cin nawa. Zuba mai tayi ta bashi zata Koma taci gaba da suya ya riko hannunta cikin shagwaba yace ni kibani a baki.
Hannu tasa ta taba goshinsa da wuyarsa ba zafi. Yace yadai tace na dauka bakada lafiya ne naga kana Abu Kamar baby. Yace aini Babyn ki ne kashe gas cooker din tayi ta dawo ta zauna a gefensa bayan ta dauko juice da honey da lemon. Tace da wanne kakeson honey ko lemon yace lemon dinde saboda tsami tsami.
Haka tayi ta bashi sunaci Suna hada plan din yadda zasu hada kan su zaliha da lukman da kuma yadda zasu gudanar da bikin su Abubakar Dan sun dano taragonsu.
Saide kash bansamu Dakar mina? abinda suke Cewa ba saboda ina can ina satar pancake dan? Nasan ko na tamabaya yazeed bazai bani ba tsabar santi Dan naji lokacin dayake Cewa in so samune minal ta bashi duka pancake din sai ta dafawa su mom wani abincin.
Bayan sun gama ci cikin raha da kaunar juna. Yazeed yace kai kullum sai kiyimin irinsa har iya tsawon rayuwar mu. Kuma duk ranan da banci Shiva Toh ko me naci saide inci Dan yunwa. Girkinki na daban ne masoyiya. Hugging dinshi tayi tace Insha Allah kullum zannayi maka girki kuma duk ranan da ban Daga ma abinci da hanuna ba Toh ko wa na dafawa aikin banza ne.
Karashe aikinta tayi yazeed ya tayata jera dining table.
Kowa sai Santi yake sahir Dan taurinkai tasowa yayi ya rike hannun yazeed yace daddy I am sorry I called you a bad daddy you are the best daddy because you married the best aunty who can cook the best pancake.(baba kayi hakuri nacema kai ba ubanl na gari bane. Kai din uba na gari ne daya a cikin miliyan saboda auro aunty wacca tafi kowa kuma ta iya soya pancake dayafi ko wanne dadi.) Shafa kanshi yazeed yayi yace is okay my boy. Wajen minal yaje yace aunty will you be my friend?(aunty shin zaki zama kawata?) Daga kai tayi tana murmushi tace yes peck ya mata a kumatu sannan ya hau cinyanta ya zauna bayan ya janyo abincinsa gabanta yace ita zata bashi yazeed yace my boy ka girma fa karka balla min aunty.
Safwan ne ya taso yazo wajen yazeed yana turo baki yace am I not your boy? (Ni ba yaronka bane?) Yazeed yace yes your are my dearest son(eh kai danane da nakeda kusanci dashi). Gwaliyo sahir ya masa. Kallon minal safwan din yayi tace masa karka damu kai amini nane ba abokina bama. Din buro fuska sahir dake cinyanta yayi tace sorry sahir karkayi kuka kaima amininane.