KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Hararta minal tayi tace shegiya sai Sanin sirrin kula da miki amma ba’a aiki dashi. Kinyi asara, ni ba wannan bama Wai a ina like Sanin abubuwan nan ne? Zaliha tace mutum da salularsa a WhatsApp mana a irin groups hakannan kinsan sai kaga dama zakayi misusing phone. Kinsman wasu su suke jawa Kansu duk abinda ya samesu. Minal tayi ajiyan zuciya tare da Cewa hakane Nide ki hada lambata a lintsima ni Dan baza’ayi babu ni ba. Zaliha tace angama matar oga. Dariya su kayi kamin suka shige wata hirar.
Yazeed ko wanka yayi ya fito ya rasa yadda zaiyi da ransa rana zafi inuwa kuna.
Bayan sallar isha’i zakiyya ta hada golden morn tana sha yazeed ya Shigo. Ajiyewa tayi agun ta haura sama abinta shikam kallo ma yake binta dashi. Dakinshi ya wuce abinsa koda yaje Abu yagani cikin bargonsa karasawa yayi yaga minal ce ke bacci tabe baki yayi yace uhm matsoraciya kawai.
Wanka yayi abinsa ya Shirya kamin ya kunna game yana bugawa abinsa. Tashi juyi tayi hakan yasa bargon yadan zame taga Ashe bra ne ajikinta take ya juya kai tare da Cewa kul yazeed barta tadan huta zuwa ka dawo Daga mission dinka wata zuciyar tace amma kai sai ka cutu ? Yana cikin wannan zazzafar muhawara da zuciyarsa minal ta bude ido gashi tayi ta zauna kawai ta ganta ba kaya ihu ta kwalla ai super daya yayi yasa Hannu ya toshe mata baki yace ke lafiyarki kuwa? Zazzare ido tayi ganin Daga shi sai boxers itama kusan yanayi daya suke amma Idan zata tuna ai da kaya ta Shiga dakinnan kamin bacci ya kwasheta kallon window tayi taga duhu hakan yasa ta fincike hannun yazeed tayi saurin dauka tare da fadin waiyo banyi sallah ba. Kunya ne ya kamata tayi saurin shigewa toilet tare da yin dahara sannan tayi alwala. Bath robe ta saka kamin ta fito domin ta gano na kowa ya sheka mata tsiyarnan ba illa zaliha kuma zata rama.
Kayanta ta dauka ta Shirya kamin tayi sallah. Koda ta idar kin hada ido tayi da yazeed. Murmushi yayi ya rufe laptop din Nasa kamin yazo ya tsuguna a gabanta. Sunkuyar dakai kasa tayi ya dago da fuskarta yace me na sunkuyar dakai Dan tureshi tayi a wasa tace ni kunya kake sani ki kasaka kaya.
Dariya ya kyalkale dashi yace Idan wani ya ganki zai dauka wata salihar baiwa ce nanko wani abin dakika sani koni ban sani ba.
Kwanciya tayi akirjinsa tana rufe ido da hannun ta Dan dariya yakeyi mata yana shafa kanta. Cikin shagwaba tace Dan Allah ka dena ni kunya kake sani ji. Cakulkuli ya fara mata tun tana nokewa har ta fara dariya. Cakulkulin itama ta masa kamin ta mike da gudu nanfa suka fara guje guje pillow ta dauko tana kwala mai tare da Cewa banaso aiko kaimi ya kara wajen yi mata cakulkuli tana fading waiyo zanyi fitsari cikina. Shikam dariya yaketa yi. Dukansa ta fara yi dakyau da pillown shima ya dauko wani Daga nan aka Koma pillow fight abin dai gwanin ban sha’awa sanda suka faffasa pillown gaba daya dama guda 4 ne yazeed daya kalli dakin yaga yadda ya wargaje saboda wayo yace uhm bari inje in yin kallon mikewa yayi zai gudu tayi saurin cafko wandonsa ta janyosa tare da saurin rude koda tace babu Inda zaka sai Mun gyara dakinnan. Fuskar abin tausayi yayi mata taja hancinsa tace oga babu wannan maganar fa. Nanfa suka dukufa ka’in dana’in suka gyara dakin. Sai haki suke yazeed ya baje a gado. Minal ta dauko takarda ita ma ta fada gado jagab. Miko masa takaddar tayi yace haba uwar karatu ai ma huta na yau ko bakiga yadda Muka gaji bane. Jinjina kai minal tayi alamar yadda Dan itama dama ta gaji tace ya batun tausar fa yace barshi kawai shima. Murmushi tamai ta rungumesa kamin ta kwanta a wurinta. Tace Saida safe yazzy baby. Matsowa yayi yace ke madam tashi.
Zama tayi yace akwai matsala tace name fa? Yace ni bana iya bacci Idan babu pillow tace Toh bari in dauko ma a daki na ta fadi hakan tana kokarin sauka Dan ta dauka da gaske yake. Riko hannunta yayi yana mata wani munafikin murmushi yace haba mutuniyata ace duk aikinnan da kikayi kuma sai na baki wahalan dauko mina pillow? Zo ki kwanta abinki tace Toh ya zakayi kayi Baccin? Yace kwanta kede ki gani tana kwanciya ya kwanta a kirjinta dariya tayi tace zama kayi bayani. Da ka fadi kanka tsaye kace kanaso ka kwanta a jikina ba ka tsaya noke noke ba. Murmushi kawai yayi Kamin yace Allah ya miki albarka tace Ameen da alamu bacci na Neman saceta. Hannunsa ya daura a cikinta yace my minal inama ace yanzu haka akwai Dan Babyn mu acikinki mu rayu dukanmu harda su auntynki cikin farin ciki Dan dariya yayi idonsa fal da kwalla domin yana matukar son ya samu haihuwa yace ace Ku haihu rana daya kuma Ku haifi Yan uku uku. Jin shiru bata kwafso masa wani kwaba ba yasa ya kalli fuskarta yaga ai tana wani duniyan sumbatar ta yayi kamin ya kwanta bayan ya musu addu’a yana Rokan Allah ubangiji ya azuetashi da yaransa na kansa.
Kuyi hakuri nace zan muku update jiya kuka mini shiru afwan banida lafiya ne Kamar yadda wasunku suka sani amma yanzu dai na samu sauki kuma da izinin Allah jibi zan muku update.
Longest chapter ever Dan haka nima inason sweetest comments
Love you all?
Miss untichlobanty?
22 January, 2020
??KURUCIYAR MINAL ??
?by miss Untichlobanty ?
?CHAPTER 69?
Zakiyya kam koda ta gama kukanta fitowa tayi domin ta dauki golden morn dinta amma sai taga abinda akasha har wuce rabin Wanda ta dama kuma Idan zata iya tunawa cokali 3 tasha, tabe baki tayi tace may be ban lura bane shiyasa.
Shanyewa tayi kamin takai kitchen. Dakin da ayush take ta shiga ta duba ta sannan tayiwa nurse saide safe saide ta lura kamar akwai abinda ke damun nurse din amma sai ta basar.
Koda ta koma daki taga 2 missed calls from summy wannan friend dinta yar lesbian.
Calling back tayi ringing 2 ta dauka gaggaisawa sukayi tayi Mata Jaje sannan ta sanar Mata cewa mom dinta batada lafiya jibi zatazo ta dauketa sai ta duba ta. Zakiyya tace toh amma sai ta fadawa yazeed.
Koda gari ya Waye registration nasu jamb da WAEC and NECO akayiwa minal bakinnan har kunne. Bayan sun dawo minal tana Yan tattare tattare a dakinta sai ga zakiyya. Gaisawa sukayi tace toh mu fara ko. Minal tace toh bari na gama Dan tattare tattare nan. Hannun zakiyya tasa sukayi tare bayan sun gama suka nufi toilet minal tace toh tayi Mata alwalar yadda ta iya ta gani sai ta Mata gyara.
Abinda ya bawa minal mamaki shine ta iya tace Mata to ai kin iya ma. Murmushi kawai tayi akayi Salah ma gyara kadan aka Mata. Bayan sun gama har su azkar minal tace toh aunty zakiyya duk kin sani ma ai gyaranki kadan ne. Murmushi tayi tace thanks to my father lokacin da muke yara…..
TUNA BAYA
_
Wani mutumi ne me kimanin shekaru 45 tsaye a tsakiyar parlourn gidanshi da alamu an bata masa rai duba da yadda yaketa huci kofar wani daki ya kalla tare da cewa ummi! Zakiyya! Idan na shigo dakinnan zaku gane kuranku. Wata budurwa me kimanin shekaru 15 ce ta fito tana zumbure zunbure. Wani kallo ya bita dashi yace kede ummi kinji kunya babbar banza kawai ke bakisan cewa Ilimi shine gatan mace ba da makarantar boko ne kinfi kowa rawar kai wato shine kika fara hurewa yar uwar taki kunne ko.
Kauda kai gefe tayi tare da zura hijabin islamiyarta. Yarinya me kimanin shekaru 11 ne ta fito tare da cewa abba kayi hakuri hijab Dina na rasa. Murmushi yayi yace ba komai AI nasan ki zakiyya ta badai himma ba wajen karatu dama ke na sawa me sunan mamana ba wannan babbar kwabon ba. Kallon ummi yayi yace Allah ya shirya ta tabe baki.
Mota suka shige ya nufi islamiyarsu. Koda suka isa yace toh ummi Allah yasa muga alkhairi wannan karan. Indai sakamakon nan da zaku karbo yayi kyau to zan sayo miki wannan takalmin Kema zakiyya Allah yasa kinyi maintaining position dinki. Ameen tace cikin ajin dadi kamin ta dauki Jakarta. Naira biyar biyar ya basu yace ga wannan ku rike ko? Godiya zakiyya tayi tana mai jin dadi yayinda ummi ta yatsine fuska ta karba sannan ta fice ba ko godiya.