KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Akwana a tashi yau sati daya amma a yan uwan zakiyya babu Wanda ya bugo tunda dama mommyn ta rabasu da Dangin mahaifinsu, danginta ko babu Wanda zakiyya ta sani idan ba ayush ba itama zata can jibge banbancinta da gawa kadan ne. Rayuwa kenan yau Kaine gobe waninka yanzu duk yadda take fantamawa jibi yadda cikin kankanin lokaci DUNIYA tayi Mata atishawan tsiya.
BAYAN WATA HUDU
Rayuwa ta warware ma jeedmar family,minal ta gama zama jarabawarta har admission ya fito tayi su registration in 2 weeks time zata fara zuwa makaranta. Tsakaninta da yazeed kuwa komai ya daidata kuma suni cewa daga ya dawo zata bashi hakkinsa a matsayin welcome gift. Yaune kuma rananda yazeed zai dawo daga mission din daya tafi Kamata yayi ace sun dawo tun last week amma lukman ya Kira yace wani Abu zai tsaida su sai this week. Gidan ya kacame sai aiki ake oga yazeed yayi wata daya baya gida. Ayush had yau shiru kakeji mashkur kuwa ya nemi transfer gaba daya zuwa Nigeria inda ya hada hannu da yazeed suka siye hospital din. Su ya Abubakar ma an saka ranan aurensu kuma yanzu haka saura wata daya Dan haka sunata shiri,Abin saide hamdala.
Su zaliha lamarinsu ba’a cewa komai domin lamarinsu kara gaba yakeyi a kullum sukanyi fada yakai sau 3……..
Minal ne ta fito da gudu hannunta rike da wani container cike da cakes yayinda su sahir ke binta a baya suna cewa mommy zamuci mommy zamuci
Dariya zakiyya? ke musu daidai lokacin zaliha ta shigo tana murmushi tace ku kuma lafiya haka kuketa gudu. Rugowa sukayi wajen zaliha sukace yauwa aunty black beauty dan Allah kicewa mommy minal ta bamu cake. Fuskan abin tausayi zaliha tayi Mata tace haba mommy minal bazaki bamu cake din ba? Dariya zakiyya ta fashe dashi tace kede zaliha anyi babbar banza.? Guda daya minal ta dauko zata raba musu zaliha tace me kike nufi uwar rowa don Allah mu ki bamu muci mu koshi minal tace ananne kuma kikayi karya daddaya San Baku. Jiniya suka juyo hakan yasa suka firfito waje dukansu mom harda saurinta itace a gaba. Koda motocin suka tsaya ido suka zura domin ganin yazeed dinsu farinciki kuma jagoran gidansu saide me lukman ne ya fito rike da sandar guragu(crotches), ambulance din hospital ne ta shigo aka bude bayanta tare da sauko da gawa take mom ta zube a kasa ba tare da tashirya ba yayinda jiri ya dauki minal itama ta zauna zakiyya kam an fara zama customer din masifa da tashin hankali dan haka sankarewa tayi……….
? kai jama’a ban gane ba yazeed,yazeed ya mutu a filin yaki? Waiye? huhuu !!!???
Domin samun cigaban wannan labari ku sabarbado comments tare da sharhi masu tarin yawa.
Wannan page sadaukarwa ce ga @?+249 90 592 7248? Allah yabar kauna sis.
Lovelies karku damu indai mutum yanayi comment yadda ya kamata toh zan saudakar masa da page
Takuce (shesshekan kuka) KARAMARSU BABBARSU
Miss Untichlobanty ?
??KURUCIYAR MINAL ??
?by miss_untichlobanty ?
?CHAPTER 71?
KAFIN MA KI KARANTA KI SANI YAZEED YA MUTU ?
Sauko da modern keken guragu wato wheel chair akayi, kofa aka bude aka aka ciro yazeed aka daura akai gaba daya jikinsa bandage ne. Haaaaaah ! Kowa ya kara firgicewa. Firgicinsu na yanzu yafi na sanda sukaga gawa suka dauka yazeed ne, Kai sukam Allah ya duba musu. Daga sun fita daga sannan matsalar sai su fada wancan. Innalillah wa inna ilaihi raji’un shine abinda suketa maimatawa da gudu minal ta rugo tanaso ta fada jikinshi ta rungumeshi amma ba hali saboda jikinshi baki daya ciwone. Dakyar mom ta Mike idanunta sai anbaliyar hawaye suke tace my son? Me zan gani haka? Kaine kuwa ? Ji yadda ka koma. Hawayene ya gangarowa yazeed minal tasa hannu ta goge zakiyya ko tama kasa yin komai kawai kallo take yayinda zaliha ta karasa kusa da mijinta jiki ba kwari riko hannunshi tayi tace ahhh! Ta hararesa kasa kasa tace kaide anyi rago ka duba yazeed jarumi. Turbune fuska yayi yace a haka kika aurenin dai kinga ko bakida bakin magana.
Da badan yanayin da ake ciki ba da babu abinda zai hanasu yin fada. Ciki suka dunguma baki daya batareda sunbi ta kan gawan ba Wanda ya kasance na Joshua.
Tarairaya da kula kam yazeed yashashi a wajen ahalinsa? cikin Kan kanin lokaci duk an since bandage din jikinsa na wuya da hannu ne sukayi saura. Kwance yake kan gado yana anfani da wayana da dayan hannunshi sai ga minal ta shigo niki niki da kayan abinci zakiyya na biye da ita zakiyya ce ta taimaka masa ya zauna minal tace ya yazeed(bata kiransa da yazzy baby a gaban zakiyya) kasan me? Murmushi yayi yace a ah. Tace nayi maka pancake. Murmushinsa ne ya kara fadada yace a lallai yau zanci abinci dayawa.
Zakiyya tace ni kuma zobo na maka yace masha Allah nikam Dan gata ne. Murmushi suka mai kamin suka zuba abincin da zobo zakiyya ce ta zauna a gefensa tana bashi yayinda minal ke masa tausa Kamar yadda dr ya uemura saboda har yanzu baya tafiya dan haka zama waje daya zai iya ja mai matsala.
Dadi yakeji sosai a ranshi sanda yaci ya koshi yayi nat kamin yace na koshi.
Zakiyya tace AI ni mamaki ne ma ya isheni wai yaushe ka fara cin abinci dayawa minal ya nuno yace aunty minal ne ta koyamin ya fadi hakan kamar yaro. Dariya suka mai kamin taja hancin minal kallon juna suka tsayayi. Zakiyya ta lura da hakan aranta tace ya Allah karka raba masoyannan ya Allah ni kuma ka bani Wanda zai nuna min soyayya fiye da wannan. Ganin abin ba karau ba yasa ta tattare kwanukan ta fice dasu tare da rufe musu kofarsu.
Can mutaneku suka farga dubawan da zasuyi sukaga har ta kwashe kwanikan ta fice. Hannun minal yazeed ya riko ya daurata a cinya yace my minal kenan kinsan nayi missing din lips dinki ko ? Murmushi tayi tana Dan sauke kai tace nima domin ta dan rage jin kunyarsa. Pecking lips dinta yayi yace minali na, tace na’am yazzy baby yace akwai wata magana da nake so muyi. Tace ina jinka yace inasonki kuma kema kin sani saide kaddara ta Riga fata domin bazan danne miki hakki ba. Ki saurareni da hankalin fahimta inaso ki sani wannan Abu daya sameni daga Allah ne, hankalinta ne ya fara tashi ganin yana shirin kuka. Shafa kanshi tayi alamun yaci gaba yace ba… zan iya biyawa mace bukatarta balle ta kai ga a Sami rabo. In hankalin minal yayi dubu toh ya tashi amma sai ta dake tace innalillah wa inna ilaihi raji’un!kayi hakuri insha Allah komai zai daidata. Riko hannunta yayi yace inaso ki amince na rabu dake ki samu wani miji kiyi aure domin ko a musulunci zamanmu akwai matsala. Rungumeshi tayi kam tana kuka tace wallahi idan ka kara tunanin rabuwa dani saina falls maka Mari ko da haihuwa ko babu ni zan zauna dakai har abada. Kuka take sosai domin ta tausayawa yazeed saboda yasan yadda yake burin samun haihuwa. Kuka tasha sosai kamin yazeed yace taje ta kiramai zakiyya.
Koda zakiyya taga idanun minal tun daganan tasan akwai matsala cikin tashin hankali tace minal me ya faru? Fada kukayi?girgiza kai kawai tayi kamin tace yana kiranki sannan ta wuce dakinta.
Sallama zakiyya tayi ta shigo amma me? Yazeed ma dai a wargaje take tunani ta fara to kodai sakan minal yayi?
Jiki babu kwari ta karasa ta zauna. Bayani ya Mata yadda yayiwa minal amma batace komai ba can ta sauke ajiyan zuciya tayi salati kamin tace faduwa ce tazo daidai da zama domin kuwa nima ba Dade inaso inzo muyi magana dakai. Bazan boyeta ba tunda nake dakai ban taba gane cewa banasonka ba saida na shiryu,shi yasa ko jini banson hadawa dakai,ashe duk zamannan da muke kudinka da family name nakeso. Da badan kuskurena ba da yanzu kaga jininka domin ni ke Shan magungunan hana haihuwa a baya koda aka Sami kuskure ciki ya shigeni zubarwa nayi. Ina rokonka sa ka yafemin kusa kurai ba bazan kara ba. Tana kaiwa gabannan ta fashe da kuka hawaye ne ya silalo wa yazeed. Indai hakane toh fa zakiyya ta cuceshi amma ya zaiyi ? Dole ya yafe Mata tunda tayi nadama. Paper da Niro ta miko masa tare da cewa na gode da irin soyayyar daka nunamin. Tabbas baka tauyemin hakki ba kuma kikayi tunanin zan rabu dakai Dan abinda ya sameka ne ah ah zan rabu dakai ne saboda na cutar dakai kuma Allah ya kawo me kula dakai kiyimin izini in rubuta takaddar tunda kai hannunka da matsala. Gyada Mata kai yayi yace sau daya ya sake gyada kai. Abin abin tausayi rungumeshi tayi sukayiwa juna dogon sumbata kamar karsu rabu amma dole ta rabu dashi saboda ta kuntata mai dayawa yanzu itama gara tayita dakon sonshi a boye tunda ta nuna batasonshi kuma karya take dukda ko tanason dukiyarshi a baya suna shima tana sonshi. Kawai de ta biyawa son zuciya ne tare da hudubar Sheridan.