KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Sansadowa yayi ya warce papers tare da cewa me ki keyine baby. Turo baki tayi tare da kokarin kwace paper dinta canja hannu ya fara yi sanda ya bata wahala kamin ya bata. Yace list din menene wannan? tace list din kayan abinci ne. Dafatan akwai space a group building yace eh tace masha Allah daga gobe zamu fara saida snacks and desserts sannan zamu dinga yin contract na?abinci. Murmushi kawai yayi sannan ya tashi ya fice da sauri domin idonsa ya ciko da kwalla kar minal ta gani. Ita ko jikinta yayi sanyi ta dauka idea dinta ne bayaso hakan yasa ta yaga papern sannan ta fada gado ta fara kuka. Ace mijinta yana matsanancin hali kuma bazata iya taimaka wa ba?

Yazeed kam kukan farin ciki ne ya kama sa da nadaman yadda ya dinga treating dinta, Allah yasha dashi da ace ya sake ta da yayi babban asara. Komawa yayi yaga tana kuka yasa yayi saurin karasawa bakin gadon tare da fadin baby na lafiya kuma juyawa yayi ya kalli kujeran da suka zauna yaga ta yaga papern. Da sauri ya kwaso su kamin ya dawo gefenta ya zauna tare da fadin ya haka ? Me yasa kika yaga mana plan din? Cikin shessheka ta tashi tare da cewa na dauka bai maka bane ace kana da kudi kana da group ince maka ka fara saida abinci dukda cewa quantity da quality me kyau ne kuma naga cewa ba’a daukan shawaran Mata.

Murmushi yayi ya goge Mata hawaye tare da cewa wa yace miki na Rena shawaranki ? AI sana’a bata kadan albarka kawai ake nema. Batun shawara kuwa kin fini karfin tunani ma amatsayinki na mace. Murmushi tayi tace Allah? Yace kwarai kuwa mata ta sannan ya rungume ta.

Pieces din paper din ya bata kamin ya fita ya karbo glue ya like musu takardan sannan ya janyota suka baza shopping din kayan abincin su Dan da zafi zafi ake dukan karfe.
Gidan radio da talabijin aka sanar AI kan kace me wannan sun Sami order yafi dari saboda ana matukar son yazeed. Minal sanda ta tsorata ta fara? darewa tana ganin bazata iya ba yazeed yace karka damu zasu dinga Tahowa da masu aikin gidan su sai su dinga tayata, kuma ai shima yananan.

Haka suka dawo gida sunyi likis ranan da wuri suka kwanta 9pm a gado ta musu.

Kirrrrrr!kirrrrr!kirrrrrr!

Tsaki minal taja tare da sake shigewa jikin yazeed. Bacci sukayi bayan sunyi sallan subh sai suka saita Alarm din 6:30am suka saita dan shirya tafiya aikin su akan lokaci, badan ranta yaso ba ta tashi suka shirya sai jeedmar group sai dadi takeji.

Direct area dinsu suka tafi bashida girma; office 3 ne a ciki ba manya sosai ba sai kitchen da reception. Aiki suka fara minal da yazeed na girki saura na packaging da branding. Sallah da cin abinci kawai suke tsayawa yi. Masu delivery nata yi. Ga orders 3 na biki yazeed in yayi aiki sai ya dawo ya goge wa minal gumi sai yaci gaba. Haka suka yi ta yi har yamma tukunna suka tafi gida gaba daya sunyi likis wanka da ruwan zafi sukayi, tare da sallah da cin abin ci. Sai gado a kwana a tashi cikin sati daya aiki ya fi karfin Dan mutum ga riba sun tara sosai kawai sai suka siya engine. Sosai sukayi dedicating time dinsu suna aikin su.

Mutane kuwa ganin abin da akayi wa yazeed ba’ayi masa adalci ba gashi an kasa proving komai, an duba account summary dinshi da kuma information na company transactions dinshi duk kudinshi daga company dinshi ne albashinsa ne kawai from government.

Dan haka mutane suka fara zanga zanga cewa dole a sake masa dukiya tunda yana taimakon talakawa.

Zaune take akan kujera tana juya wa tare da busa shisha. Wani number ta Kira tace maza kuyi aikin ku da fatan mutanen sunzo? Akace yes ma tace don’t make a mistake……

Order phone din su yazeed aka Kira ya dauka nan akayi placing order na birthday party abincin 25 people.
Aka hada aka kai bayan 2 hours sai ga police wai abin cin da aka kai is poisonous kawai suka rufe shagon take yazeed ya Kira yan NAFDAC yace ya sun duba abincinsu ba’a basu number ba police yanzu sunzo sun rufe musu aiki.

NAFDAC suka ce gasunan zuwa after 30min sai ga su. Yazeed yace ga yan sandan can suna jira they should talk to them, shugaban tawagar tafiyar NAFDAC din yace it’s true abincin is poisonous. Yazeed yace toh me yasa suka yi musu register a baya ? Sukace ai Sam basuyi musu register ba sannan sukace ma yan sandan a tafi dashi cell dukda cewa military officer ne ai yayi laifi sannan bulldozer zata zo ta rushe part din ko kuma ya bar wa government yace ai ba nasa bane mallakin matarsa ne Dan haka basuda right akai. Sojoji ya Kira har Wanda gwamnati ta kwace masa sanda suka zo sai ga jama’a ma sun iso, domin live komai ke faduwa ga yan jarida rututu.

Sojoji da mutane suka kewaye yazeed mutane sukace ba’a isa a rushe wajen ba yayinda sojoji sukace ko abar maganan ko su bude wa yan sandan da nafdac wuta. Atake aka fara yada jita jita wai yazeed shi ke supporting din terrorism wasu kuma nacewa ya hada kai da yan boko haram ne.

Back up na 20 cars aka aiko ma yan sanda yayinda sojoji ma suka karo back up, kaucewa mutane suka fara yi Dan sunga fadan yafi karfinsu. Shugaban yansanda na lokacin ne ya zo shima sai ga shugaban sojoji ma .
Cikin isa shugaban yan sanda yazo ya danko hannun yazeed wai zai wullashi a mota minal tayi kukan kura ta raba hannun su tare da cin kwalarsa ta yarfa masa Mari 3 masu kyau. Sama yan sanda suka harba tare da saita ta da bindigogi amma ko gezau batayi ba sojoji ma suka harbi sama suka saita shugaban yan sandan sukace ana taba minal sunanshi sorry.

Huci minal keyi tare da kara matse damkar da tayi masa har yana ?a?arin amai , kawai wani Dan sanda mai rawan kai ya saita ta tauuuuu! Kakeji.

MASHA ALLAH! DONT FORGET TO FOLLOW ME, VOTE AND COMMENT AND INA BUKATAR ADDU’AR KU MUN KUSA FARA EXAMS

THANK YOU! TAKUCE KARAMARSU BABBARSU

miss Untichlobanty ?

23rd February, 2020.

??KURUCIYAR MINAL??

?by miss_untichlobanty ?

?CHAPTER 76?

RECAP

Back up na 20 cars aka aiko ma yan sanda yayinda sojoji ma suka karo back up, kaucewa mutane suka fara yi Dan sunga fadan yafi karfinsu. Shugaban yansanda na lokacin ne ya zo shima sai ga shugaban sojoji ma .
Cikin isa shugaban yan sanda yazo ya danko hannun yazeed wai zai wullashi a mota minal tayi kukan kura ta raba hannun su tare da cin kwalarsa ta yarfa masa Mari 3 masu kyau. Sama yan sanda suka harba tare da saita ta da bindigogi amma ko gezau batayi ba sojoji ma suka harbi sama suka saita shugaban yan sandan sukace ana taba minal sunanshi sorry.

Huci minal keyi tare da kara matse damkar da tayi masa har yana ?a?arin amai , kawai wani Dan sanda mai rawan kai ya saita ta tauuuuu! Kakeji.

CONTINUATION

Shiru wajen yayi tsit kowa yana register din abinda ya faru.
Faduwa minal tayi akan guiwanta tare da rike hannunta da aka harba. AI nan kakejin dau!dau! An sakewa Dan sandan nan bullet biyu a hannu.

Nan fa shugaban nafdac ya fara hadiya yawu tare da kokarin zamewa ya gudu, wabi cacuma sojoji suka masa sukace ko ya fadi gaskiya ko yaji ba kyau. Tsilli tsilli yayi da ido Dan yaga mutuwa a gabansa. Nan fa ya fara in ina,wani soja me zafin rai me suna musa ya gwabje sa da bindiga atake ya soma bayani cewa kudi aka biyasa ya fadi hakan.
Akace wa ya biyasa yace Alhaji tukur gadon kaya ne. Nan take ya basu registration number tare da bada hakuri yazeed yace ai dole a tsigeshi nan fa ido ya Rena fata m, haka ya dinga bada hakuri yana nuna nadamar da yayi sanda yazeed ya tabbata ya wahala yace yaji ya tafi zaiyi tunani amma fa hakan batayi wa Musa dadi ba Dan haka yasa shi lungu ya dan jijjibgesa ya sauya masa halitta kamin ya barsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button