KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Alokacin su scorpion Suna arean motan minal ta bace musu ganin yazeed ya fito daga motan gashi wandon sojojinshi yasa da farin T-shirt Ba shiri suka bar wajen shikuma da baiga kowa Ba kawai sai ya koma
Su ezikel ne suka fito da guntun kayan suka saka a booth din kamin suka rufe
minal tana hangosu suka daura mata kaya gashi ta gansu da kaki atake wani mugun fitsari ya matseta Â
Yazeed ya Duba agogo yaga 11:45 sai yace kawai su kaiwa zakiyya kayan sai su wuce airport
Dan ko su Jamal din sun iso kamin su sauko, kayansu ya taho, ya fito zai bata lokaci shi kuma bayason jira
Sai yace muje gida mu sauke kayan
Driver ya kunna mota suka nufi gida
Minal tanajin an kunna motan tace shikenan za’a kaini barikin sojoji na Shiga uku na lalace.
AT JEEDMAR
Suna shigowa yazeed ko fita daga motan baiyiba yace su sauke kayan daga motan su shigar gida
Sukace yes sir
Booth suka bude fara Ciro kayan lukman na daga Leda taga Kamar kafan mutum
Ahankali ya radawa ezikel “be ready something no dey right here
Ezikel ya Ciro AK47 dinshi ya saita daidai minal
Lukman ya ajiye ledan hannunshi ya daga daidai na kanta
Wata yar kyakkyawa ya gani mai cute pinky lips tana bacci babu Komai a fiskanta sai uban man baki Kamar zai digo
Suka furta wow a tare
Kallon juna sukayi Suna magana da ido akan yanda zasu fadawa boss
Lukman ya gyada kai alamun zaije ya fada
Kewayowa yayi murya kasa-kasa
yace boss an sami matsala
Yazeed: meaning?
Lukman: dama…em da Muka..mukaje Ciro kayan….shin……..
Yazeed: hope Ba Barin kaya kukayiba ?
ya fadi haka adan tsawace
Lukman: a a dama acikin booth…..
Ezikel ne ya tsindumo baki
Ezikel: boss lukman dey shy for u ooo,wani Yaro ne beauuuuutiful
Muka ganshi asikin booth yana bassi
Yazeed: ezikel what nonsense are you talking about ?
Ezikel: boss if adey lie,thunder fire me
Yazeed: let me go and see
Futowa yayi yazo wurin booth din minal ya gani tana bacci hankali kwance
Tabbas bazai manta wannan fiskarba
Wannan yarinyarce Wanda tamai fitsara jiya dole ya shaidata kodan man bakinnan lebensa na kasa ya gatsa
Sannan ya dakarkare ya daka mata duka a gadon baya yaga ko motsawa batayi Ba
Aranshi yace lallai wannan yarinyar ni zata nunawa jarumta
Kwata kwata bekawowa kansa Cewa zai iya yuwuwa suma tayi saboda babu ninfashi ba Wanda haka abin yake suma tayi Saboda rashin ninfashi inba hakaba minal ko cinnaka ya cije ta an Shiga uku balle soja ya watsa mata tafi.
Ciki ya Shiga babu kowa sai mai shara yace ta kawo masa chilled ruwa gora biyu
Jiki na bari ta dauko ta basa ya karba ya fita
Zuwa yayi ya kalli minal tana kwance yanda ya barta su lukuman a tsaye
Gora daya ya mikawa ezikel
Sannan ya bude dayan
Ezikel yace boss ruwan akwai sanyi sosai fa
Yazeed yace na fika sanin haka
Kamin ezikel ya kara magana
Yazeed ya juyewa minal ruwan sanyi…………..
Ina sonku irin sosai dinnan
9 June,2019
Mzz untichlobanty💕
2 – CHAPTER 11-20
ðŸ†ðŸ†KURUCIYAR MINALðŸ†ðŸ†
By miss untichlobanty
ðŸ€ðŸŒ¹CHAPTER 11🌹ðŸ€
A zabure ta wantsalo daga cikin booth din tana salati ta fado a gaban lukman ta kurje hannunta
Bude idon da zatayi taga takalmin soja
sai alokacin ta tuna mai ya faru kawai sai idonta ya ciko da hawaye
Fitsarin da takeji dazu ya dawo ya cika mata Mara taf
Yau tasan ta Shiga uku kashinta ya bushe ta Shiga hannun soja
Tsawa yazeed ya daga mata ke mike tsaye ?
Allurar ta motsa
Ba ita kadai Ba har su lukman Saida suka tsorata
fitsarin da takeji atake yabi jikin skirt dinta tana zazzare ido
tace kuyi hakuri walla…..
Bata karashe Ba yazeed yace shut up my friend, kalleni!
Sai alokacin ta kalleshi babu shakka wannan basamuden datayiwa rashin kunya ne jiya itakam ta shi uku Ashe soja ta tsokalo
Duka kam yau zata shashi harda na sadaka
Tace Dan Allah kayi hakuri ka yafe mini wallahi bazan kar….
Yace shhhhh yimin shiru
Yazeed yace Samuel inasu doggy suke ne?
Samuel:Suna cage ne fah
Yazeed: bring them out
Samuel: yes sir
Minal taji ance su doggy kuma ance cage sai ta dauka
Cage din da yake kai masu laifi nan zai kaita
Tafara Cewa oga sir kayi hakuri karka hadani da arna a caji office dinka wallahi na dena
Gashi idonta ya ciko da hawaye amma sunki su zubo tayi tayi sunki su zubo
Shi kuma yazeed abinda ke kara bashi haushi kenan takiyin kuka ita a dole jaruma
Haushin karnuka ta faraji a take ta kara tsula wani fitsarin
Wasu kosassun police dog ne guda biyu
Tsalle tafara tana ihu innalillahi wayyo inna na Shiga uku na lalace amma still babu hawaye
Alokacin duka masu aikin gidan sun taru
tsabagen muryarta shiyasa inna batason minal tana kuka ta kwammaci dije tayi sau goma akan minal tayi sau daya
kowa na tsoran bada hakuri kar a hada dashi
wasu kuma na mamakin mai ya hada oga da wannan yar kyakkyawar innocent yarinya Dan basu taba ganinsa a wannan yanayi Ba
dukda sunsan Cewa bayada sakin fiska ayanzu
Gashi mom batanan taje gidan friend dinta balle tasa baki
Madam zakiyya ma batanan ta tafi wani get together da sukeyi ita da business partners dinta Wanda yazeed bai Masan dashi Ba
Da minal tayi hawaye yazeed zaisa amayarda karnukan ganin takiyin hawaye tana ihu kawai yasa yake ganin pretending takeyi
besan tsananin tashin hankali yasa ta kasa hawaye ba
Kallonta yayi yace ke al’amarinnaki bayan tsiwa harda taurin kai ko ?
Tace wallahi oga sir Ba taurin kai bane
Yazeed yace release them!
Atake Samuel ya sakesu sukayo kanta babu shiri ta antaya a guje
fitsari nabin skirt dinta domin ahalin yanxu ta tsula yakai sau biyarÂ
Gudu take Suna binta har suka iso wurin swimming pools.
Toh anzo wurin minal nason wasan ruwa amma bata taba Shiga mai yawa Ba gashi Ba tashin kauye tayi ba balle ta iya nitso da linkaya
amma kuma ga karnika nan Suna tunkarota kuma wa dannan bazasuyi mata da kyau ba
Dan ga bakinsu har yawu yake zubarwa
Kawai sai ta yanke shawara gwara ta fada ruwan koba Komai gawanta zatayi mutunci
Finndumm!!
ta fada swimming pool din Samuel kuma da gudu ya riko karnikan Dan karsu bita cikin ruwan
Yazeed Wanda ke tafiyan kasaita har ya iso wajen
Alokacin lukman na shirin fadawa ruwan Dan ya cetota Yazeed ya dakatar dashi
Rigarsa ya cire sannan ya fada ruwan alokacin har tasha ruwa nimfashinta ya kusa daukewa
ya daukota
Akunnenta ya rada mata bashi sannan ya fito da ita
yacewa masu aiki su hada mata shayi mai zafi tasha sai su nuna mata side dinshi Tasameshi acan
sannan su lukman suje su dauko jamal kuma
karkowa ya sake ya fadawa mamy ko Jamal abinda ya faru
Ya wuce side dinshi
Wet trouser dinshi ya cire sannan
Ya saka wani tare da farin T-shirt kamar Wanda ya cire sannan ya fada gadonsa yana tunanin abinda zaiyiwa minal Idan ta farfado batayi kuka ba
Domin yaga sanda ta suma a hannunshi……..
Am feeling so sleepy yet typed coz of the love I have for u guys
Show me some love as well
11 June 2019
Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:44 AM] Mzz_Untichlobanty💞: ðŸ†ðŸ†KURUCIYAR MINALðŸ†ðŸ†
By miss untichlobanty
CHAPTER 12
minal kuwa shayin dazai taimaka mata da condition din da take aka hada mata
Kamin suka samo bowl da ruwan dumi da tsumma
Sannan suka dauko first aid box domin ciwon dake hannunta har yanxu yana zubda jini
duk ya bata mata hijab dinta
Tabawa dukkan maids da securities din gidan tausayi hatta sojojin domin duk rashin imanin wasu daga cikinsu sunsan Cewa minal ta horu