KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Tana gama karantawa tayi kicin kicin da ido duka ta kawo masa ya kauce yana dariya ta ?wale hannunta. Kafa tasa ta turesa daga kan gadon ya fadi fatt a kasa tace idan na ganja a gadon nan sai na cire ma idanu kuma bazan hado shayin ba. Kwanciya yayi a tsakiyar gadon ta juya masa baya. Murmushi me sauti yayi yace idan nan da minti biyar ya cika banga shayi na ba kinsan student ID card dinki yana gurina? Kaiwa zanyi lost and found na makarantar ku ince a club din hotel na samu kamin ya karashe maganar har ta isa bakin kofa. Yatsar tsakiyar hannu ta nuna masa wato alamar f*ck you sannan ta fita tana shiga kicin ta samu sahla da safwan a bakin fridge suna lobewa tsaki taja tace dalla malamai ku tafi dakinku.? Saa ne tace sis Allah ya isa kin kalle min kirji zayya tace dadin abun shekara daya da ya wuce ma tare muke wanka dukda an hanamu sannan taci gaba da harkar gabanta.
Washe gari Monday wato litinin aka sallamota. Koda ta dawo su zayya sun tafi makaranta. Direct dakinta ta wuce amma me tana shiga ta fara jin kukan jarirai hakan yasa babu shiri kafa a faffale kamar baba ari Dan wasan hausa ta fito da gudu ta koma mota tace summy tuka muje wajen mugu, maza kaini wajen boka mugu Dan wallahi akwai matsala ya taimaka min.
Bayan tafiyar awa biyu suka iso lokacin ayush tayi lubus Dan ba zama sai kwanciya a karkace shima. Taimaka Mata summy tayi suka shiga ta baya baya suna gafaran ku dai subhanallah sukaji ana fadi ayush toh kuji wata sabuwa ko batan kai mukayi bokan yana ganinta ya ganeta yace aishatu dakata daganan idan har kinsan da mummunar Niya kikazo Dan ni Allah ya shirye ni. Ayush tace taimaka boka taimaka…… datseta yayi yace ke ni ba boka bane ni yanzu gardi ne na makarantar allo. Shekarar da ta gabata ma nine jagoran yan maulidi toh ke maulidin ma na gane karyace bidi’a ce sahabbai basuyi ba manzon Allah baiyi ba baice a masa kuma de AI banfi sahabbai son manzo ba ko? Kuma dai manzon nan yace duk Wanda ya kirkiri wani aikin addini Wanda ba daga wurinsu yake ba toh an mayar masa.
Kinga ni ba Dan wahala bane da…….
Datseshi tayi ta hanyar cewa ni mugu duk wannan zance da kake yaushe ma nakeda imani balle na kama sunnar na bar bidi’a? Yace ke ba sunana mugu ba Salmanu nake atakaice ni me sunan salmanul farisiy ne. Tace toh koma wa kake ba salmanu ba nide taimaka wallahi kukan jarirai nakeji a daki na yace AI saima kin fara ganinsu AI duk Wanda muka yanka ne nima nan da kike ganina ina fara jin su na tuba Dan na gano an Sami matsala kiyi gaggawar tuba wata kila Allah yasa kiji kamshin rahama koda baki ganta ba. Kuka ta fara tace kash ba wani taimakawa da kake sai rura wutar ke sumaiya muje. Mikewa sukayi suka fita tana nazarin inda zata Sami sabon boka.
Koda suka dawo sumaiya tace toh ko wani aiki nayi miki za’a kara da kudin sa fa ayush tace ba matsala. Tana shiga ya leka dakin amma har yanzu kukan jarirai take ji haka ta kankame hannun summy har tayi bacci. Summy ne ta Sami mummy ta fada Mata abin da ya faru.
Cikin mamaki mummy taje dakin tana kalle kalle amma bataji komai ba tace ka bibiya kalle kallen film ya janyo Dan gobe sai tace taga kurwa.
Yazeed kam cewa yayi bazashi aiki ba yana makale a gurin minal yayi ma Jamal waya cewa a nemi gurbi a bawa sabir me gadi aiki sannan ya kashe wayarsa cikin hakane sukaji hayaniya ta bayan Window dinsu ta kasa lekawa sukayi suka ga ayush ne da wata amma da alamu ayush a firgice take. Minal har tana Tuntube ta kunna CCTV footage din suka kalli komai.
Minal tace na Sami idea! Yazeed yace na me fa? Tace tunda dai bisa alamu aljanune suke bibiyarta dole zasu hanata bacci da daddare da rana kuma sai mudinga yi Mata kurwa tunda kaji dai abinda mahaifiyar ta tace kaga sun yarda akwai kurwa kenan. Kaga kawai kowa kallon tabbabiya zai dinga Mata daga nan zamu San abinyi.
DON’T FORGET TO VOTE,COMMENT AND SHARE.
LOVE YOU ALL!
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU
Miss untichlobanty ?
3rd MAY, 2020
??KURUCIYAR MINAL??
?by miss untichlobanty?
?CHAPTER 93
RECAP
Minal tace na Sami idea! Yazeed yace na me fa? Tace tunda dai bisa alamu aljanune suke bibiyarta dole zasu hanata bacci da daddare da rana kuma sai mudinga yi Mata kurwa tunda kaji dai abinda mahaifiyar ta tace kaga sun yarda akwai kurwa kenan. Kaga kawai kowa kallon tabbabiya zai dinga Mata daga nan zamu San abinyi.
CONTINUATION
A makaranta kuwa zayya suna shigowa aka fara kallon sabon motan Dan ba’a sanshi ba saboda ba da wannan motan yazo ba a karan shi na farko. Ansiya musu sabin mota saboda sunyi aure. Kan kace me labari ya karade ai an kawo sabuwar daliba. Motan na tsayawa kowa yayi kur da ido amma me ? Zayya ce da sahir suka fito hannu sakale da na juna dukda ko mintsininta yakeyi.
Ta aika masa harara alamun zata Rama har hostel ya rakata sukayi sallama ashe yeonsil da halsey suna hangosu ta window Dan a second floor suke tana shigowa sanda gabanta ya fadi ganin mutane? biyu sun kafeta da ido da sauri suka zauna da ita a bakin gado sukace dama a wajen mr handsome kikayi spending weekend dinki bayan kin sanr da mu cewa auren mamanki zakije?? Tace da farko dai addinin mu ya hanamu kwana a gidan saurayi na biyu kuma labarin dogone zama suka gyara sukace mun shirya ko zai kaimu Isha’I. Dungure kansu tayi tace ajin fa sukace ki mana alkwari zaku bamu tace an gama sannan suka shirya suka wuce.
Bayan sun dawo daga aji ta labarta musu yadda akayi tass har inda aka daura auren shewa sukayi sukace mude ki bamu tsarabar my dauko ma kowa nata tayi daidai lokacin cingam ya fado yeonsil ta dauka dama ita uwar bari ce babu ruwanta ko me yazo fada kawai take tace la me nake gani anan ? Zayya tayi saurin warcewa tare da? cewa bani chewing gum Dina.
Tafawa sukayi halsey tace kai amma kin Rena mana AI baki cika alkwari ba tunda baki bamu labarin bangaren nan ba. Shine dan renin hankali muna gani condom baro baro kice mana cingam? Dan yamutsa fuska tayi tace con..dom? Halsey tace kwarai. Zaunarta sukayi tare da bata bayani filla filla. Kamar zakanya haka ta Mike ta danna masa Kira ringing 2 ya dauka cikin tsokana yace wifey kinyi missing Dina ne naga… kamin ya karasa tace idan na kara jin kalma daya daga gareka lahira zatayi bako. Wato da gangan kace na taho da wannan abar makaranta ko? Yanzu idan da principal ta gani me zance? Bari ma ka gani yanzu zanzo in sameka saina…..
Yeonsil ne tayi saurin karban wayan ta kashe suka sata a tsakiya. Dungure kanta yeonsil tayi tace kinada hankali kuwa ? Halsey ma ta dungure ta tace mijinki kike ma ihu? Yeonsil ta dungurota tace kuma Dan iskanci harda? cewa zaki kasheshi? A tare suka dungure keyarta sukace daga yau abinda mukace kiyi shi zakiyi.
A gida kuwa ayush ta samu ta fito harda kunna kallo amma me abinda ya fara baiyana shine horror movie. Cikin tashin hankali ta saki remote tare da kashe socket din. Ta koma daki da gudu bata fito ba sai bayan magariba da yunwa ya sakota a gaba. Da sanda take takawa babu kowa a parlourn kuma akwai duhu a hankali ta kunna wuta.
Wani Abu taga ya gifta acikin kitchen din gabanta na dukan tara tara sansada ta shiga amma bataga kowa ba. Shayi ta fara hadawa kawai wuta yadauke kofar kitchen din ya rufu da karfi ihu ta tsala ta taho da sauri taja kofar amma a rufe kuka ta farayi sai taji ana dariyar mugunta a bayanta juyawa tayi kafarta na karkarwa batasan tana fitari ba cikin bari tace waye?