KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Muryarce tace Mata gani nan a sama tana kalla kuwa ta zube kasa sumammiya. Abinda bata sani ba kuwa shine basirar sahla ce tayi aiki domin ta iya Zane hakan yasa tayi zanen kurwa ta abinda ake cewa 3D.

Koda ta bude idonta a daki ta sameta babu kowa saide ba’a canja Mata kayan jikinta ba har ta fara zarni. Mikewa tayi jiri na Dan dibarta taji ance sannu a kujerar dake dakinta. Tana juyowa sanda kirjinta ya buga wata ce zaune da farin kaya irin na nurse a jikinta kwayan idonta kore manya manya da gani kasan da matsala murmushi ta sakewa ayush tace sannu da tashi madam nice me kula dake har zuwa lokacin da zaki warke.? Yake ayush tayi matar tace kina bukatar wani Abu ne ayush tace eh fitsari zanyi. Kamata tayi ta taimaka Mata itadai ganin ikon Allah take domin bata taba ganin me irin halittar ba. Gabanta na faduwa ta shiga bandakin ta fara tsulawa kawai taga wuta ya mutu zabura tayi ta Mike tace nurse ke kika kashe wutan ne? Shiru sake magana tayi amma ba’a amsa ba hakan yasa da gudu ta fito ba tare da ta mayar da suturar ta ba tana haki tace mummy! Mummy!

A birkice mummy ta shigo tana fadin lafiya? Cikin tsinkewan numfashi tace ina…. ina take ? Mummy? tace wa? Ayush tace nurse din. Mummy tace nurse kuma? AI babu wata nurse a gidannan. Cikin Dibir bir cewa tace mummy kice Allah. Tace zan miki karya ne aishatu? Tace mummy na banu wallahi aljanu da kurwa nake gani.

Dariya mummy tayi tace kiji min ke da wani zance wai aljanu da kurwa. Kode minyard ce ta fara tabaki kinga ni barni naje nayi bacci kema ki kwanta ta fadi haka tana juyawa rikota ayush tayi shikin kuka tace mummy na karki barni Dan Allah na shigesu mummy tace ke ayush banson sakrci ya kike Abu kamar yarinya ne ? Ni ki wuce ki kwanta gobe ma tattauna ayush tace inada sheda akwai kurwar a kicin muje ki ganta nasan wannan ma buya tayi idan babu zan barki ki kwanta.

Kitchen sukaje babu komai su yazeed har sun goge. Mummy tace kingani babu komai haba yar kirki. Kawai ke kike ganin cewa akwai wani Abu amma babu komai je ki kwanta kinji cikin sanyin jiki tace toh amma a dakinki zan kwana mummy.

Dakin mummy suka shiga hankalinta ya Dan fara kwanciya hakan yasa ta yanke shawarar shiga bandaki tayi wanka bayan mummy ta tabbatar Mata babu komai a ciki. Da dar dar tayi wankan amma bataga komai ba har ta fara tunanin toh ko da gaske babu komai kawai rudewa tayi? Gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta cikin kwana biyu kamar ana tsotse Mata jini. Duk tayi wani kwarshal da ita fuskar nurse dinne ya fado Mata a zuciya take fitsari ya tsargo Mata. Har ta gabatar tayi flushing amma maimakon ruwa sai taga jini. Juyawa tayi bayan ta rufe ido ta daura hannunta a kirji tace ayush karki damu ba gaskiya bane. A hankali ta bude idonta sai taga jariri anyi masa yankan wulakanci jini yana bulbulowa kamar daga famfo da gudu ta fice Dan yanzu ba ta ciwon jikinta take ba yanzu ta ranta take. Mummy tace ke lafiya kika fito kamar kinga mutuwa? Ayush tace idan kika fadin hakan ma yayi daidai domin naga mutuwar. Mummy wallahi ba tunani na bane yanzu nan naga……..

Labarta Mata tayi mummy taja tsaki tace ke ni kin fara fice mini akai inba iskanci ba yaushe katuwa irinki zata dinga wani gudun kurwa da aljanu? Na fara? bacci na zaki wani fito da gudu ki tsinka mini gaba muje naga ni. Ayush ta shige bargo tana rawar sanyi tace bani kara shiga wallahi. Gobe dakin yaya yazeed zani Dan shi yana addu’a.? Mummy tace ni kuma kafura ko? Toh nima na iya addu’ar ai babu abinda zai bani tsoro ayush de batace komai ba illa kara kankame bargo da tayi.

Mummy cikin dure duren ashar ta shiga ban dakin tana fadin wani shegen ne? yake tsoratar min da yata? Aikin banza da wifi ashe ma matsorata ne kunsan dai ni ba gaba da gaba ba ko ta baya sai an shirya. Har zata fita taga brush din ayush dake jefe cikin sink. Girgiza kai tayi tana kaji shashashar yarinya. Bude famfon? sink? tayi ta wanke tace gashinan ruwa me kyau zata wani ce na jini ne. Kamin ta rufe bakinta ruwan ya koma jini. Murmushi tayi tace ka duba nima har tasa na fara gane gane. Rufe fanfon tayi dukda ko taga jini ne amma gani take kamar tunaninta be dago kanta da zatayi ta cikin madubi ta kalli wannan nurse din saide halittarta ta munana sosai anan murmushi tayi ma mummy tare da daga Mata hannu alamun hello sannan tace SANNUNKI!

Bude baki mummy tayi zatayi magana amma shiru kakeji ji kake jigib tayi ruf da ciki a gaban aljana tana. Waiyo! Waiyo ! Aisha! Aisha ki kawo Agaji ki taimaka.
Ayush ne ta leko kanta ta cikin bargo tace mummy ba komai fa karki damu shirme na ne. Mummy tace kiyi wa Allah kizo wallahi wannan shine fitsari na na 5 kenan kiramini yazeed yayi min addu’ar nan. Ayush tace AI kema kin iya? kiyi kawai kamin ta rufe bakinta wani saurayin aljanu kyakkyawa har yafi yazeed nesa ba kusa ba amma kwayar idonsa Jajawur ne ya zauna a gefenta tare da daura hannunsa a bakinta yana Mata murmushi yace matata kiyi shiru kinji? Kirjinta na bugu ta gyada kai.

A bandaki kuwa mummy fadi lakad ja’akum innaka innaka humaiya wai ita ta dage addua take harda daga murya………

TO BE CONTINUED IN CHAPTER 94…….

SISTERS? YA KUKE YA RAMADAN ? YA IBADA ALLAH YA BAMU LADANSA.

ME KUKE TUNANI GAME DA CHAPTER DINNAN ? SHIN HUKUNCIN DA NAYI WA SU AYUSH YA DACE DASU ?

KARKU MANTA KUYI VOTING DA COMMENTING TARE DA SHARING.

LOVE YOU ALL ?

miss untichlobanty ?

8th may, 2020.

?? KURUCIYAR MINAL??

? By miss Untichlobanty ?

? CHAPTER 94 – 95?

RECAP

Ayush tace AI kema kin iya? kiyi kawai kamin ta rufe bakinta wani saurayin aljanu kyakkyawa har yafi yazeed nesa ba kusa ba amma kwayar idonsa Jajawur ne ya zauna a gefenta tare da daura hannunsa a bakinta yana Mata murmushi yace matata kiyi shiru kinji? Kirjinta na bugu ta gyada kai.

A bandaki kuwa mummy fadi “lakad ja’akum innaka innaka humaiya” wai ita ta dage addua take harda daga murya………

CONTINUATION

Haka kawai ayush taji ta kasa yin komai jikinta duk ya mutu ta kurawa wannan aljanin ido. Bayan wasu dakiku yayi murmushi yace mahaifiyar ki ta fita raki daga ganin yaya ta duk tabi ta rikice murya na rawa tace waye kai? Murmushi ya Mata yace ni mijin ki ne. Zaro ido tayi tace AI inada miji kuma kai aljani ne tayaya zaka aure ni? Riko hannunta yayi yace zo mu tafi gidan mu masoyiya ta.

Kamar shashasha (dama shashashar ce) ta sauko daga gadon yace rufe idonki rufewa tayi. Taji kamar suna cikin iska bayan sakanni yace bude. Tana budewa ta ganta a wani kungurmin daji ta Dan tsorata amma ganin ya rike hannunta yasa ta Dan saki ranta tafiya suka fara babu jimawa ta hango wani dankareren gida kai kace ba duniya bace.

Murmushi tayi a ranta tace Allah me riko nikam abubuwa sunmin daidai ga miji kyakkyawa ga kuma dankareren gida. Murmushi me sauti aljanin yayi Dan yanajin duk tunanin nan nata.

Suna shiga cikin gidan kofar ta rufe gam sanda gabanta ya fadi juyawa tayi tare da kokarin bude kofar taji kyam Kyam ta juyo zata ma aljanin magana amma sai gata a kasa sumammiya saboda halittar sa ta asali da ta gani jibgege ne. Harshensa kamar na micijiya idonsa kore shar ga kaho, ga jela kai bazai kwatantu ba.

………

Zayya kuwa tsakar dare ta gudo ta nufi gidan sahir dama tana da mukullinta dan haka babu wani danna kararrawa ta danna kai ta shigewar ta.
Sahir yana bacci yaji ruwan sanyi sai jinsa kake a kasa fat! Ya fado. Mikewa yayi ganin zayya ce yace baby har kinyi missing Dina ne? Tace Allah ya kiyaye dama hukuncin abinda kayi min nazo ma kaga tafiya ta. Tayi ficewar ta kwafa yayi yace yarinyar nan sai na yi Mata seti tukunna.?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button