SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Mutane kowa mamakin auren babban Mutum kuma ɗan manya kamar Najeeb Jibo su ke. Aure ba IV ba sanarwa a kafafen yaɗa labarai ba komai.
Abunka da masu arziƙi a hakan sai da aka haɗa reception bayan an tashi a masallaci aka wuce venue wajen da aka ci aka sha.

Ƙarfe ɗaya saura motar da ta ɗauko su daga asibiti ta tsaya a ƙofar gidan. Ita da Ummi da Maijiddah ne a motan sai ƙanin AbdulWahab mijin Jiddah da ya ɗaukosu kasancewa motar Baffa Musa ta shiga garari.

A hankali su ka shigo gidan nan aka fara guɗa.

“Ayyiriri amarya a gidan manya, tsatson fulani tsatson larabawa. Kyakykyawa mai kyawun hali. Taka lafiya amarya agidan Alhaji Jibo.”

Chak ta tsaya lokacin da ta ji kalmar ƙarshe ” Alhaji Jibo”

“Mu shiga ciki Farida” Ummi ta faɗa tana hanata damar tambayar ma’anar abinda ta ji…

Zuwa bayan azahar Farida ta shiga ruɗani. Zancen da ake ma ta mai kama da shirin film ta ka sa processing na shi a ƙwaƙwalwarta.
Ba abinda Ummi da Nanna ke ce ma ta sai ta yi haƙuri haka ƙaddarar ta ya zo. Kodan ganin ba ta kuka ne ya sa su ke ma ta wannan zancen banzan wai ta karɓi auren Najeeb Jibo a matsayin ƙaddararta.
Ita da tun jiya da dare da ta fara jin sauƙi ta yankewa kan ta hukuncin komawa karatu ta yi pdg ta yi masters na ta. Sannan ace yanzu an aurar da ita wa Najeeb. Mutumin da ya rusa ma ta auren ta da Rayyan.

Zuwa yamma Baffa Musa ya sa aka kirata. Nasihar dai da su Ummin su ke ma ta shi ma ita ya maimaita. Wai ta yi haƙuri.

“Farida ke ‘ya ta ce, kuma ba zan ga abinda zai cutar da ke na tura ki ciki ba. Wannan al’amari rubutacce ne daga Ubangiji. Ki yi haƙuri ki yiwa mijinki biyayya ki kuma zauna agidan ki lafiya. Ki rage yawar magana dan Allah”

Jin Baffa kawai ta ke yi amma aure da Najeeb kam ba ta ga ta zama ba.

Ummi ce ta sa dole ta yi wanka duk da ta ƙi kwalliya amma ta sa wani leshi mai kyau wanda Ummin ne ta siya ma ta saboda wannan rana duk da kuwa a maimakon gidan Rayyan da za a kaita yanzu gidan Najeeb Jibo ne…

Ummi hawaye ta ke tana roƙon Farida ta zauna lafiya da mijinta. ” Aisha idan ba ki zauna ba haka za ayi ta irga mi ki aure. Kinga nima tawa ƙaddarar yadda ta kasance, aure na huɗu. Ba na fatan ki zama haka, idan ki ka bi a hankali da sannu za ki gano kan mijinki har ku daidaita kan ku” wannan nasiha na Ummi baƙaramin shigar Farida yai ba….

Ƙarfe takwas da rabi motocin ɗaukan amarya su ka zo. Ummi na kuka Farida na yi haka uwa da ‘ya su ka rabu.
Kai tsaye gidan su Najeeb aka wuce da ita. Nanna da Baaba Sabuwa ne su ke tare da ita a mota ɗaya. Su suka ma ta jagora zuwa cikin gidan su mijinta. Su Mom da tawagarta sun ƙarɓi amarya lafiya kuma an karrama baƙin amarya daga ƙarshe aka kaita ɗakin Najeeb wanda anan za su zauna kafin Najeeb ya ƙarasa gyara gidan sa.
Anyi nasiha kuma anyi addu’a kafin wanda su ka kawo amarya su ka tafi.

Tun tana zaune tana jiran ko Najeeb zai zo har ta haƙura ta kwanta dan ba ƙaramin bacci ne a idon ta ba.
Washegari ba ta farka ba sai ƙarfe takwas na safe. Ta shiga banɗakin da ke ɗakin dan ta yi alwala nan ta ga ƙaton bathroom wanda sai ka kwanta ka yi minshari a ciki. Tsaf-tsaf ya ke sai ƙanshi, akwai bathtube na wanka sannan gefe akwai Inda aka kewaye da glass wajen shower kenan. Ta gama kallon banɗakin kafin ta yi alwala ta fito.
Karfe tara sai ga Adama tana ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin.

“Amarya wai ki fito ki karya in ji Hajia” ta ce da ita.

“To barin shirya”
Ta yi wanka ta nemi atampa ta sa cikin kayan da aka kawo ma ta daga gida.

Lokacin da ta sauko sun gama karyawa tana saukowa tanajin Najdah na yiwa Mom ƙorafi ” Mom wallahi i cant believe wai Big B ya yi aure, wai hakan ma da lousy secretary ɗin sa”

“Be happy for your brother, finally ya yi aure @35yrs”

“Mom ba ta dace da gidan nan ba…”

“E’e’em” Farida ta yi gyaran murya

Najdah ta ɗago ido ta kalleta. Farida ta ɗan risina ta gaida Mom. Mom ta ma ta ya kwanan baƙunta.

“Najdah take her to the dining plz”

Maimakon Najdan ta yi abinda Mom ta ce sai ta fara kiran Adama.

Farida dai ta taune ta haɗiye duk wani maganan da ke bakin ta, kar ace amarya daga kwana ɗaya ta fara faɗa da ƙanwar miji.

Da Adama ta kaita dining ɗin ɗiban abinda za ta ci ta yi ta koma ɗakin Najeeb ko na ce ɗakin su.

Baƙi sun zo ganin amarya kuma ta fita an gaggaisa. Yawanci ‘yan uwa ne da abokan arziƙi…

Tana sallar Isha ya shigo ɗakin zama yai a bakin gado yana kallon yadda ta ke sallah. He cant believe he got married to this girl, a mere secretary.

Lokacin da ta idar da sallan ya kalleta da kyau sannan ya ce ” Daddy na son ganin mu ƙarfe tara”

Zuwa yai ya zauna kan kujeran da ya ke aiki idan yana ɗaki, ya kunna laptop na shi yana duba wa su saƙonni.

“Sir Najeeb dama ka min sharri ne dan ka aureni?”

Yi yai kamar bai ji ta ba sai da ta sake maimaita tambayar sannan ya juyo ya ce ” i wanted to punish you, i wanted you to cry, but it backfires on me. Na aure ki ne saboda Dad, only because of him”

Shiru ta yi tana nazarin kalamanshi tareda tunanin mafita a rayuwar ta ko na ce a rayuwar auren ta.

“Dad ba ya zama a gida, Baby na zuwa makaranta, Justice Nabilah ma ba ta zama. You’ll feel bored at home”

“Ina ruwanka” ta faɗa da ƙarfi.

Juyowa yai yana kallonta sosai, har lokacin tana zaune akan sallaya.

“I’m offering you a job. Har yanzu ban samu secretary da zai maye gurbin ki ba, so you can have your job back”

“Kan uba. Lallai ma Sir Najeeb ka raina ni”

“Well its just an offer, idan ki na so za ki iya fara aiki next week monday”

“Allah ya isa na Sir Najeeb, Allah ya isa bulluƙutu”……

(Mrs Najeeb Jibo, Najeeb constructions needs your service, Oya de go de go????)

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi

0️⃣2️⃣4️⃣

Tare su ka shigo falon Daddy, ya na zaune yana karatun littafi su ka same shi.

Farida ta zauna ƙasa tana gaida Daddyn.

” ‘yata tashi ki zauna mana”

“Daddy na fi jin daɗin ƙasan”

Daddy ya ajiye littafin ya ce

“Aisha, ina so na baki haƙuri kan yadda al’amura su ka kasance. Kin ga wannan da ki ke gani” ya nuna Najeeb.
“Babban banza ne, ba abinda ya sani sai kan sa. Ina roƙon ki dan Allah, ki yafe ma sa duk abinda ya mi ki”

“Daddy komai ya wuce, na yafe ma sa”

“Allah ya mi ki albarka Aisha. Sai ki riƙa haƙuri da shi domin shi ɗin wani bahagon mutum ne”

“Dad” Najeeb ya faɗa yana tsume fiska

“Ai gaskiya na faɗa, ko ba haka ba ‘yata?”

“Haka ne Daddy, wallahi wani lokacin kaman majnuni” sai da ta yi maganar kuma sai ta ji kunyar abin da ta faɗa, ta fara rufe baki da hijabinta.

“To kinga duk waɗannan halayen na sa marasa kyau, ke ce za ki shafe su, ke ce za ki inganta rayuwar sa. Ina muku fatan samun zuri’a ɗayyaba”

Farida ta ɗago ido ta kalli Najeeb wanda ya watsa ma ta harara.

“Za ki yi haƙuri ku managing wannan gida zuwa wani ɗan ƙanƙanin lokaci kafin ya ƙarasa gyara gidan shi sai ku koma chan. Ina so ki sake jiki damu domin nan gidan ki ne. Allah ya sa albarka a wannan aure na ku amin”

“Na gode Daddy, Allah ya ƙara ma ka lafiya ya ƙara arziƙi da buɗi amin”

“Duk abinda Najeeb ya mi ki ba dai-dai ba, kinga duk girman shin nan a gaban ki zan sa bulala na zane shi”

Farida ba ta san lokacin da ta kwashe da dariya ba ta ce ” wayaga ana zane Sir Najeeb, har na hango shi yana tsala ihu”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button